Ya Kamata APC Ta Tsayar Da Dan Takarar Shugaban Kasa Gaga Kudancin Nijeriya- Malam Shekarau

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Kano

A cikin tsarin mulkin APC ba a rubuta zancen karba-karba ba, amma ni na yarda akwai tsarin mulki na hankali,in ji Shekarau

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, kuma dan majalisar dattawan Nijeriya, Malam Ibrahim Shekarau ya ce ya kamata jam’iyyarsa ta APC mai mulkin Nijeriya ta damka wa kudancin kasar takarar shugaban Kasa.

A wata hira ta musamman da ya yi da Ibrahim Isa na BBC Hausa, Sanata Shekarau ya ce ana bukatar yin hakan ne don tabbatar da adalci.

Da aka tambayeshi shin kana ganin jam’iyyarku ta ki tabo batun tsarin karba-karba, kuma ana ganin a nan ne za a iya kai ruwa rana. Ta yaya kake ganin APC za ta iya kauce wa wannan? Sai ya msa da cewa, a cikin Kundin tsarin mulkin APC ba a rubuta zancen karba-karba ba, amma ni na yarda akwai tsarin mulki na hankali.

Yanzu kamar tsarin shiyya-shiyya da ake yi ai ba ya cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya, amma tsari ne mai kyau, yanzu babu abin da za ka yi ba ka shigo da wannan ciki ba.

To haka ma zancen shugabanci tsakanin kudu da arewa, idan aka yi watsi da wannan to gaskiya ba a yi wa juna adalci ba, kuma ba mu yi wa tarihin kafuwar Nijeriya adalci ba.Ni ina da ra’ayin cewar wajibi ne don kowa ya ji cewar ana yi da shi.

Da aka tambayeshi cewa, yanzu Shugaba Buhari zai kammala wa’adinsa na biyu kana tunanin mulki ya koma kudu kenan? “Sosai kuwa, ni ina ganin ya kamata mu yi hakuri mu jawo ‘yan uwanmu na kudu mu da muke daga arewa. Ka ga ai da aka yi zabe, arewa ita kadai ba za ta iya Samar da yawan ƙuri’ar samar da shugaban kasa ba, kudu ita kadai ma ba za ta yi ba, sai mun hadu kuma zaman tare muke.

Ni abin da na yarda da shi shi ne ba ma wai shiyya-shiyya ba, babu wata jiha a Nijeriya yau da ba ta da wadanda za su iya yin shugabanci a kasar nan.”

Rashin yin wannan shi zai dada kawo rarrabuwar kawuna, wasu su dinga jin ba a yi da su ko ba a so a ba su dama ko wasu sun fi iyawa, wannan duk bai kamata ya taso ba.

Ita harkar siyasa al’amari ne na yawa, kuma arewa ana tunkahon tana da yawan masu kada kuri’a, injin shekarau

Da aka tambayeshi shin  Ba kwa ganin za ku iya rashin dabara idan abokan hamayyarku kuma suka fitar da dan takara daga arewa? Sai yace, to ai kullum kana yi ne kana kallon me ye adalci. Dukkanin jam’iyyun da PDP da APC a yanzu suna cikin wannan hasashe na kowa na kallon me wane zai yi da watakila zai sha gabansa.

Amma ni abin da nake son kowaccensu ta kalla, kar mu tsaya kallon me wane zai yi ya sha gaban wani, a’a mu kalli me zan yi ya zama adalci, idan ka yi adalci, adalcinka da nagartar wanda ka fitar su za su yi jagora.

 

 

Exit mobile version