Abba Ibrahim Wada" />

Ya Kamata Bale Ya Bar Real Madrid –Berbatov

Tsohon dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Dimitar Berbatob, ya shawarci dan wasan gaba na Real Madrid, Gareth Bale daya bar kungiyar saboda magoya bayan kungiyar basa goyon bayansa.
Bale, wanda tauraruwarsa ta haska a Real Madrid a shekarun baya yana shan suka daga bangarori da daman a kungiyar wanda hakan yasa ake rade radin cewa yana dab da barin kungiyar ta kasar Sipaniya.
Kungiyoyin firimiya da dama da suka hada da Manchester United da Chelsea da tsohuwar kungiyarsa ta Tottenham ne dai suke zawarcin dan wasan wanda ya taimakawa Real Madrid ta lashe kofin zakarun turai guda hudu.
“Jita-jita tana fitowa cewa Bale yanason komawa kasar Ingila domin ya ci gaba da buga wasa kuma ya kamata ya fara tunanin haka domin tauraruwarsa za ta sake haskawa idan har yakoma gasar firimiya’ in ji Berbatob wanda tsohon dan wasan Manchester United ne.
Ya ci gaba da cewa “Yanzu duk abinda Bale yayi a Real Madrid baya burge magoya bayan kungiyar kuma suma shugabanni da ragowar ‘yan wasa basa ganin abinda yakeyi hakan yana nufin yana bukatar yakoma inda ake sonsa”
Bale dai ya zura kwallo da bugun fanareti a wasan da Real Madrid tasha da kyar a hannun kungiyar Lebente a gasar laliga da suka fafata a ranar Lahadi kuma a ranar Laraba Real Madrid za ta kece raini da Barcelona a gasar cin kofin Copa Del Rey wasa na biyu.

Exit mobile version