Tsohon mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen da kasar Jamus, Oliver Khan, ya bayyana cewa tsohon mai koyar da ‘yan wasan Real Madrid, Zinedine Zidane ne ya fi dacewa daya koyar da ‘yan wasan Bayern Munchen a kakar wasa mai zuwa.
Bayern Munchen dai za ta tsunduma neman mai koyarwa a karshen kaka sakamakon mai koyar da ‘yan wasan kungiyar na yanzu Nico Kobac zai iya barin kungiyar wanda hakan yasa Oliver Khan yake ganin Zidane yafi dacewa da aikin.
Khan ya ce Zidane zai dace da aikin saboda yanzu yaci kusan kowacce gasa kuma gashi yanzu baya tare da kowacce kungiya sakamakon barin Real Madrid da yayi a shekarar data gabata bayan ya ja ragarmar Real Madrid ta lashe kofin zakarun turai na uku a jere.
Ya kara da cewa Zidane mai koyarwa ne wanda yadace da kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen da kuma tsarinta sosai kuma dayawa daga cikin ‘yan wasan kungiyar zasuji dadin aiki da Zidane saboda gogewarsa ta rike babbar kungiya.
A kwanakin baya dai Zidane ya nuna sha’awarsa ta komawa kungiyar Chelsea sai dai kawo yanzu har yanzu kungiyar ta Chelsea bata sallami kociyan nata ba, Mauricio Sarri wanda yake shan suka daga bangarori da dama daga kungiyar.