Daga Khalid Idris Doya
Sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Shehu Sani ya shawarci shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari da ya cire kansa daga babban ministan albarkatun mai gami da sauya shi da wani mutum mai gaskiya da riƙon amana wanda zai iya ci gabantar harkar albarkatun mai wanda zai zama magajinsa a kan sha’anin mai sannan kuma ya kasance mutum mai nagartar da zai iya bin diddigin kuɗin mai a dukkanin ma’aikatun mai dake faɗin ƙasar nan.
A cikin wata sanarwar da Sanata Shehu Sanin ya fitar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ya ce, Buhari yana da ƙayyadadden lokacin da yake warewa domin sanya ido da kula da ma’aikatun man fetur, ya kuma dage kan cewar tabbas samar da babban ministan ne kawai zai rage yawan tashin hankali da ake fama dashi a ma’aikatar man fetur ɗin.
Duk dai a cikin makon da ya gabatan ne wata takardar sirri wacce ƙaramin ministan harkokin albarkatun mai, Dakta Ibe Kachikwu ya rubuta ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari inda ya ke zargin shugaban kamfanin NNPC Dakta Maikanti Baru da rashin bin dokoki da ƙa’idojin da aiki ya shimfiɗa, tare da kuma zarginsa kan yi masa wulaƙanci a yayin aiki.
A ƙarshen makon ne Majalisar Dattawa ta kafa wani kwamiti mai ƙarfi domin binciken shugaban na NNPC kan zargin da aka yi masa.
Shehu Sani ya ce: “Ya kamata Shugaba Buhari ya ajiye kujeran ministan albarkatun man fetur ya nemi wani ya sanya a kujerar wanda ya dace da zai iya tafiyar da sha’anin man fetur wanda ƙasa za ta gamsu da yadda ake tafiyar da ma’aikatun.
“Riƙe shugabacin ƙasa da kuma haɗawa da babban ministan mai zai iya kawo cikas a sha’anin ɗanyen man fetur, domin kuwa ba zai riƙa samun isasshen lokaci wajen kula da sha’anin na mai yadda ya dace ba.” Inji Shehu Sani
Daga ƙarshe Sanatan ya ce, samar da babban ministan da zai sanya ido sosai gami da kula da harkokin albarkatun man fetur na ƙasar nan ne kawai zai shawo kan dukkanin wasu matsaloli da suke jibge a sha’anin man fetur ɗin.