Connect with us

LABARAI

Ya Kamata Dakta Ahmed Gumi Ya Koma Makaranta – Sheikh Baban Tune

Published

on

An bayyana maganganun da Dakta Ahmed Gumi yake yi a Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Kaduna, a inda yake sukar lamirin yaki da cin hanci da rashawa da Hukumar EFCC ke yi a kasar nan, da cewar alama ce ta lallai Daktan na da karancin ilimi, kuma ya dace ya koma makaranta da kusantar Malamai domin neman karin karatu.

A kalaman nasa dai in ji Malamin da ke kalubalantarsa, Dakta Gumin yana bayyana cewa bai dace a tuhumi barayin gwamnati a kan dukiyar kasa da suka sace ba,

Shugaban Majalisar Limamai da Malamai ta Jihar Kaduna,  Sheikh Usman Abubakar Baban Tune, ya bayyana haka a yayin  da yake jawabi wajen rufe karatun Tafsirin Alkur’ani mai girma na watan azumi wanda ya saba gabatarwa duk shekara a Babban Masallacin Juma’a na Matatar man fetur ta NNPC da ke Kaduna.

Sheikh Baban Tune, ya ci gaba da bayyana cewa, akwai abin bakin ciki da takaici a irin maganganun da Dakta Gumi yake bayyanawa a kan kudin gwamnati, a matsayin kudin banza,  kuma duk wanda ya ci kudin ya ci banza,  a inda ya kara da cewa,  wannan kalamai ba karamin jahilci da ganganci ba ne, Dakta Gumin ya nu na. Sannan  Majalisar Limamai da Malamai tana Allah wadai da irin wadancan kalaman na shi, domin ba da yawun su yake yi ba, da yawun kashin kansa ya ke yi.

Daga karshe, Shugaban Majalisar Malamai da Limamai ta Jihar Kaduna, Sheikh Usman Abubakar Baban Tune, ya bayyana goyon bayan majalisar su a kan yaki da cin hanci da rashawa da Hukumar ta EFCC ke yi,  a inda ya shawarci  hukumar ta EFCC, da ta kara matsa kaimi wajen zakulo barayin gwamnati domin ganin ta hukunta su, saboda yin hakan zai iya zama darasi ga ‘yan baya.  A cewarsa.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: