Ya Kamata Gwamnatin Buhari Ta Tallafa Wa Manoman Timatir – Musa Dan Muhammad

Shugaban kungiyar yan gwari ta jihar Kaduna, Malam Musa Dan Muhammad Dutsen wai ya koka a bisa irin matsalolin da ke ci wa harkar noma da sayar da timatir tuwo a kwarya a kasar nan.Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a ofishinsa da ke garin Dutsen wai a yankin karamar hukumar Kubau.
Malam Dan Muhammad ya nunar bukatar da ke akwai ga gwamnatin tarayya karkashin jagoranci shugaba Muhammad Buhari ta hana shigo wa da timatir cikin kasar nan daga kasashen wajen, domin kuwa hakan na shafar sana’arsu a cikin gida Najeriya.Ya yi bayanin cewa yana da kyau ga gwamnatin tarayya ta hana shigo wa da dukkan abubuwan da ake iya noma su a cikin gida domin karfafa wa manoman rani da na damina noma daukar noma a matsayin sana’a.
Shugaban kungiyar ya kuma koka a bisa yadda ya ce gwamnatin tarayya ba ta sa kungiyarsu cikin irin kungiyoyin da ke tallafama wa a kasar nan.Don haka ya bukaci gwamnatin ta sa su tsare-tsarenta na tallafa wa manoma ta hanyar ba su rancen kudi mai saukin biya da kuma kayayyakin amfanin gona da ake bukata domin habaka noman rani a kasar nan.Ya yi bayanin cewa yayan kungiyar tasu na bukatar takin zamani da sauran kayayyakin aikin gona daga gwamnati a farahi mai rahusa domin yin hakan ne zai sa ta cika alkwarinta na bunkasa noma a dukkan fadin Najeriya.

Exit mobile version