Ya Kamata INEC Ki Duba Wannan Matsalar…

Bayan Njeriya ta yi sallama da mulkin soja a shekarar 1999, ‘yan kasar da dama sun riga sun amince da mulkin dimokuradiyya a matsayin tsarin gwamnatin da ya fi karbuwa a gare su. Kamar yadda aka sani, idan aka ce dimokuradiyya ana nufin tsarin shugabancin da zai baiwa jama’a dama su zabi shugabanninsu da kansu.

Domin tabbatar da inganci da hanya mafi sauki na zabin shugabannin; sai aka fito da tsarin yiwa wadanda za su rika zabe rajista tare da ba su katin shaida a matsayin katin da za su yi amfani da shi su jefa kuri’a idan lokacin zaben shugabannin ya zo.

Rajistar masu zaben tana da matukar muhimmanci a sha’anin zabe kasancewar ita ce take baiwa daukacin wadanda suka cancanci kada kuri’a damar zaben shugabannin siyasa.

Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta (INEC) ita ce aka damka wa alhakin yin rajistar ga masu zabe domin su yi amfani da ‘yancinsu na zabe kamar yadda ya kamata. Hukumar takan gudanar da aikin rajistar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Bisa hakan, wadanda ba su samu sun yi rajistar a wani lokaci ba za su iya yi a wani, sannan yaran da shekarunsu ba su cika na kada kuri’a a yayin gudanar da aikin rajistar a baya ba, idan aka zo yin nagaba suna samun dama su yi. Wannan ya sa hukumar ta zabe tun daga shekarar 2017 ta fara aikin rajistar zabe ga wadanda ba su yi ba tare da gyara rajistar wadanda suka sauya wuraren da suke son kada kuri’a a sakamakon sauya mazauninsu.

A zaben karshe da aka yi na kasa baki daya, masu kada kuri’a ba su fito kwansu da kwarkwata kamar yadda ya kamata ba. Domin daga cikin adadin ‘Yan Nijeriya milyan 120 da suka isa kada kuri’a, milyan 70 ne kawai suka yi rajistar katin zabensu. Daga cikin milyan 70 din kuma, milyan 30 kacal suka kada kuri’a a zaben shugaban kasa kuma su ne kadai suka yanke shawarar mutumin da ya cancanta ya shugabanci adadin ‘yan kasar mutum milyan 180. Ko ba a tambaya, tabbas wannan adadin ya yi kadan, a ce mutum milyan 30 ne za su yanke hukunci kan wanda zai shugabanci mutum milyan 180. Wannan ba abu ne da za a yaba da shi a cikin duk kasar da ta rungumi dimokuradiyya da hannu biyu-biyu ba.

Bayanai sun nunar da cewa Hukumar INEC tana da rajistar masu kada kuri’a milyan 80 a cikin kundinta kuma tana da burin kara yawansu zuwa milyan 85 domin babban zaben 2019 nan da watan Disamba. Har ila yau, bayanai sun nunar da cewa akwai adadin katin jefa kuri’a na dindindin kimanin milyan takwas da masu su ba su je sun karba ba.

A baya, watakila za a iya cewa yawo da hankulan masu kada kuri’a, mugun magudin zabe da aringizon kuri’a na rashin imani sun hasala ‘Yan Nijeriya da dama har suka yanke shawarar ba za a sake ganin fuskarsu a rumfunan kada kuri’a lokacin zabe ba. Amma a halin yanzu abin ya sauya, kwarya-kwaryar gyarar fuskar da aka yi wa dokokin zabe sun dawo da kima da martabar  sha’anin zaben kasar zuwa wani mataki abin yabawa.

Yadda sha’anin kasar ya fara daidaituwa a kan turba, an samu karin ‘Yan Nijeriya masu yawa da suke da muradin shiga a dama da su wajen zaben shugabannin kasar na gaba. Tuni har ma wadanda aka san su da rungume hannu a lokacin zabukan baya sun nuna alamar dokin zaben. Duk wannan saboda kwazon da gwamnati mai ci a yanzu take yi ne.

Kamar yadda aka zata, an samu karuwar wayar da kan jama’a daga sassa daban-daban na kasar a kan muhimmancin mallakar katin zabe ga duk wanda ya kai munzalin kada kuri’a. Ba a taba samun kaimi da kuzarin wayar da kan jama’a a kan muhimmancin katin zaben kamar yadda ake yi a yanzu ba, kasancewar abin ya cika gari lungu-lungu da sako-sako. A duk inda mutum ya juya zai ji ana batun katin zaben da muhimmancin yin sa. Hatta wadanda suka mayar da kafofin sadarwa na walwalar jama’a wurin tafka muhawara da cin diddigen juna ana wayar musu da kai cewa wannan ba za su fishe su ba, mafita gare su kawai su mallaki katin rajistar zabe.

Abin birgewa kan hakan shi ne yadda mutane suka amsa kira. Duk wanda bai yi ba yana kokarin zuwa ya yi rajistar a cibiyoyin da aka tanada na musamman domin aikin. Sai dai wani abu da za a iya cewa ya zama ga-koshi-ga-kwanan yunwa shi ne yadda mutane ke shan wuya kafin su samu a yi musu rajistar.  Aikin yana tafiyar hawainiya kuma ga wahalar yi. Mutane da yawa sun ba da labarin yadda suka shafe sa’o’i da dama kafin a kammala yi musu rajistar. Wannan ma ga wadanda suka taki sa’a ke nan, amma wasu da abin ya yi musu tutsu da yawa sai sun shafe kwanaki suna zuwa wurin rajistar ba su samu yi ba. Masu neman a yi musu rajistar zaben galibi sukan bar gida tun kafin Karin-kumallo kuma su shafe yini cur su dawo gida haka nan ba tare da an yi musu ba. Wadannan matsalolin ba su rasa nasaba da karancin cibiyoyin rajistar, na’urorin aikin da kuma rashin isassun ma’aikata.

A wasu wuraren kuma cibiyoyin da aka kebe na aikin sun yi wa jama’a nisa. An ba da rahoton cewa an bude cibiyoyin rajistar ne a shalkwatocin kananan hukumomi. A wasu kananan hukumomin kuma; babu ma cibiyar rajistar kwata-kwata, don haka sai mutane sun tafi kananan hukumomin da ke makotaka da su kafin su yi rajistar. Hakan ta kara jidali ga masu neman a yi musu rajistar tare da kashe musu kwarin gwiwa. A sanadiyyar hakan, wasu sun hakura da lamarin, inda wannan zai sa su rasa damar amfani da ‘yancinsu na zaben shugabannin da suka kwanta musu a rai. Bayan duk wannan, wusa kananan hukumomin jami’ansu sukan hana a yi wa wasu rajistar saboda banbancin shiyyar da mutum ya fito saboda wai fargabar kar mutum ya zo ya zabi dantakarar da ba shi suke so ya ci zabe a yankinsu ba. Tabbas, hakan ta saba wa ka’idar dimokuradiyya.

Saboda haka, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) kina da jan-aiki a gabanki kuma duk da cewa mun lura ayyuka sun yi miki yawa, ya kamata ki mike haikan wurin ganin kin magance wadannan matsaloli da suke dabaibaye aikin rajistar masu kada kuri’a. Ki duba yiwuwar kara yawan cibiyoyin aikin rajistar a manya da kananan garuruwa tare da na’urorin aiki da kuma isassun ma’aikata domin saukaka aikin kamar yadda ya kamata.

 

Exit mobile version