Abdulfatah Hassan" />

Ya Kamata Jama’a Su rika Yi Wa ’Yan Majalisa Uzuri –Hon. Ahmad Yunusa

Wannan wata tattaunawa ce da ABDULFATAH HASSAN yayi da USTAZ AHMAD YUNUSA ABUBAKAR, dan majalisa mai wakiltar Yamaltu Deba daga Jihar Gombe, a majalisar tarayya. Ac ikin hirar ta su, dan majalisar ya bayyana yadda hakikanin aikin dan majalisa yake a hukumance. Ga yadda hirar ta kasance:

Mai karatu zai so sanin takaitaccen tarihinka

Suna na Yunusa Ahmad Abubakar, amma an fi kira na da Ustaz Yunus, wasu kuma su kan kira ni da injiniya Yunus, saboda ni injiniya ne.

Na yi makarantar Firamare tun lokacin da ake aji daya zuwa bakwai a wani gari da ake kira Difa a karkashin masarautar Yamaltu dake karamar hukuma Yanaltu Deba ta jihar Gombe. na fara makaranta daga 1970 zuwa 1977, daga nan wuce zuwa makarantar da ake kira makarantar Sikandiren gwamnati ta Kaltuji, a nan jihar Gombe, ko da yake a lokacin ana jihar Bauchi. Na yi aji daya zuwa biyar a wannar makarantar, wato daga 1977 zuwa 1982. Bayan na kammala ban yi jira ba na wuce zuwa makaranta ta gaba da sakandire in da na yi abin da ake kira Basic Studies a Jami’ar Ahmadu Bello dake zaria, a lokacin ba ‘Remedial’ bane. Domin a lokacinmu ba abin da ake kira JAMB. Bayan wannan na shiga Jami’ar Ahmadu Bello na fara karatun Digiri, amma daga baya na bari sakamakon wasu dalilai. Toh duk da haka na kara na dawo makarantar kimiya da fasaha wanda aka fi sani da ‘polytechnic’ ta Kaduna lokaci ita ce babban Kwaleji, inda Allah ya taimake ni na yi Diploma a nan, na kuma yi babbar Difloma (HND) inda na fita da sakamako mai kyau. Daga nan na tafi na tafi, jami’ar Legas na yi abin da ake kira post graduate Diploma (PGD).

Daga nan kuma na yi karatu na Jami’ar Manchester, dag nan kuma na sake komawa na yi karata bangaren sana’ata ta Engineering, na yi abin da ake kira, ‘kasuwanci da shugabanci. daga nan ma kuma, na yi karatu a London Graduate School, Shi ma ina da Master Class a wannan Certificate, a nan kuma ina da Honorary Degree, wanda ake kira Phd, da Jami’ar Jamus da California suka ba ni. Sannan akwai Jami’ar common wealth ta London, inda ita ma ta girmama ni da mukamin ‘Doctorate degree.’

Toh idan na dan koma baya kuwa, lokacin da na dan-taba karatuna a Polytechnic, na yi aiki a Jihar Bauchi inda na fara a ma’aikatar ilimi, na yi koyarwa a makarantar da yanzu ake kira Tatari Ali polytechnic, amman a lokacin tana, makarantar koyon fasaha ta Bauchi da aka kirkiro ta koma polytechnic. Toh akwai kuma wani abin da ya faru, na ga ba zan iya ci gaba da aiki a polytechnic ba, aka sauya min wurin aiki aka kaini makarantar koyon fasahar Gwamnati ta Gumau, na zauna can har na zama mataimakin Shugaban makarantar. Sai kuma na koma ma’ai katar ayyuka, na bar ma’aikatar ilimi. A lokacin har aka yi zaton ko fushi na yi, nan kuma sai aka ba ni makarantar Gumau din, to Shugaban da ban yi ba ma kenan.

A takardar su ta principal na nemi canji na zama Principal Engineer har zuwa 1993. Sai na bari na shiga siyasa, Lokacin ina da zummar na nemi shugabancin karamar hukumar na Yamaltu Deba. Toh muna cikin wanna lamarin, wata yana saura kwana uku ne mu yi abin da ake kira zaben fidda gwani, sai Shonekan ya ajiye aiki a matsayinsa na Shugaban  kasa na Interim National gobernment da aka yi. Toh a hawan Abacha sai ya rusa tubalin siyasa na NRC da SDP. Daga nan na tafi na shiga sana’ar koli da hajata ta bangaren ‘Engineering’ wanda aka fi sani da ‘Consultancy. Toh muna yi kuma dai wani lokacin ana da kwafolo da kuma abin da ya shafi kere-kere, gyaran na’urorin wuta da makaman tansu. Toh ana ciki haka, da Abacha ya zo aka yi jam’iyu irinsu DPN, su UNP, da sauransu nan ma muka taru muka shiga DPN, har na zo aka fara zabubbuka, aka zabe ni a matsayin wakili, a wannan ma zabar ta Yamaltu ta yamma a majalisar jiha. Muka ci zabe, aka cigaba da sauran zabubbuka saura a yi zaben Shugaban kasa.

Sai Allah ya karbi ran, Janar sai Abacha, shi kuma Abdulsalami da ya zo ya rusa wadannan jam’iyyu. Jam’lyu biyar ne a lokacin aka fara yin Rijistar akwai su APP inda Allah ya dorani a APP na zo na zama Dan Majalisar Jiha a lokacin Gwamna Hashidu.

A yanzu kuma ina Dan-majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Yamaltu Deba. Kuma ni ne Shugaban kwamitin kula da aiyukan hukumar kula da hadura ta kasa wato (Road safety) kuma ina cikin kwamitoci Majalisa daban-daban da suka kai  goma. Na kuma gabatar da kuduri (bills) a gaban majalisa sama da Goma, kuma wasu sun wuce karatu na biyu dana uku, wasu kuma jira kawai suke a amince da su. Akwai wasu kudirorin gaggawa da na gabatar. To irin wadannan suna nan na yi su kusan30.

 

Ya kake kallon siyasar jihar Gombe a yanzu musamman ganin cewa jam’iyar PDP ce ke mulki a Jihar?

To Alhamdulillah, Idan muka kalli ita siyasa musammaman ma ta wannnan kasa tamu baki daya sai muce Tubarkallah, Dimokradiyyar Nijeriya ta samu tagomashi, tana cigaba, domin yadda take haka jiya ba haka ta ke yau ba. Jihar Gombe ma ba a bar ta a baya ba.

 

Wani irin karin bayani za ka yi wa mutane dangane da aikinku na majalisa.

Alhamdulillah wannan na daya daga cikin abin da nake ce maka alama ce ta ci gaban siyasa. Irin wannan abin yana furuwa ne a da, amma yanzu an ci gaba, saboda yawancin wadanda suka samu kansu zababbu irinmu muna kokarin wayar musu da kansu.

Hakan kuma ya kan faru saboda  rashin tsari. Kamar ni daga kauye aka zabe ni, ba an zabe ni ne in zo in yi aiki a Abuja. Kasan a ka’ida sau biyu ne ya kamata Dan majalisa yake ziyartar mazabarsa. Duk dan majalisa da yake zuwa mazabarsa ko wanne mako, to ba shi da abin yi ne, saboda haka tsari ne ya kamata wakilan su yi.

Ka san su mutane sun dauka ana ba wa dan majalisa wani kudin da zai je ne ya raba musu, wanda kuma ba haka ba ne. Shi ya sa dole dan majalisa ya duba ya ga inda zai samu kudi saboda yawan ba ni – ba ni da mutane ke yi, jama’a don Allah a rika yi wa dan majalisa uzuri, saboda tasowa daga gida zuwa Abuja ka dauko mota ka batawa kanka lokaci ba shi da amfani, kuma in ka zo ba ka same shi ba shikenan ya haddasa gaba.

Saboda haka, Dan-majalisa gwara yayi abin da zai cece dubu akan mutum daya. Ba wajibi bane ba ne akan ka kazo inda Dan majalisarka yake. Amma Alhadulillah, yanzu lamarin na raguwa, musamman ma da zuwan wannan gwamnatin, kuma duk da haka kila nan gaba, in an ce mutum ya zo ba zai zo ba, saboda wakilinsa yana aiki ‘yan siyasar KJK dinnan ko sun zo ka yi musu wani abu, idan sun koma gida sai su ce ai mun je bai mana komai ba, ya samu mun yi asara kawai. Shi ya sa ni in dai ka zo wurina zan fito mu gaisa, amma zance ka, koma gidanka ina da wakilaina a mazabata ka same su ka ce kana da matsala, su kuma za su yi min bayani, ni kuma sai na taimaka.

 

Ya ya ka karbi wannan kiran nasu?

Ka san sa kai ya fi bauta ciwo. Tun wancan na farko ina ta nema na iso wannan wuri, sai 2015. Kudirina dama shi ne na nuna cewa za ka iya amfai da wannan ofishin don ci gaban  yankunanka, don wasu sun gaza amfani da wannan damar. To don ba da tawa gudummawar ne ya sa na bar sana’ata na zo. Kuma daman karo na farkon ma na nema ne don na nuna muhimmancin ofishin. Kuma, alal hakika, ko yau kasuwa ta watse, dan koli ya ci riba. Jama’a ganin wannan ya sa suka ce hakika akwai wasu abubuwan da baka kammala su ba, irinsu kudirori da suran wasu ababuwa, domin idan aka je zaben fidda gwani dan majalisa ya fadi, toh daga nan kuma sauran ya majalisan ba za su sake masa gannin bashi da amfani.

Kuma duk abin da ya faro daga farko bai dammala ba shokenan ba za’aci gaba dashi ba tunda sabone wani sai gama shekara hudun baisan me yakeji ba. Daloli na biyu she, mutanene sun zauna sun ce’ ya kamata in koma, domin hausawa sunce da tsohon zuma ake magani.

Kuma a majalisa idan kayi zuwan farko ne toh a baya ka ke, kuma ba kowane irin matsayi zaka nama a majalisa ba. Amman idan kai tazarce ka yi toh kowane irin mukami zaka nema.

Toh shi ya sa al’umman mazabata suka zo suka same ni suka ce min sun gamsu da irin wakilcina  don haka na cancanci in zarce.

Toh da ya ke sune masu zabe kuma su sukemun kiranye, toh shi ya sa kawai na badakai bori ya hau, tunda daman sune masu zaben. amma wannan Damban da aka daura kuma in an dawo aiki zai iya fin na baya.

 

Wane kira za ka yi wa matasa don ganin sun kauracewa harkar bangar siyasa?

Matasa Babban kiran da zan muku shi ne, lallai ku yi amfani da abin da ake cewa jiki magayi, domin jiya, shekaran Jiya, an yi ta wannan bangar siyasar an yi ta sare-sare, me ya haifar mana ko me muka ribata. Shin riba aka yi ko asara aka yi? To shi fa duk abin da zaman lafiya ko salama bai ba da shi ba, to fada bai ba da shi ko yaki da ake ji gari da gari ko kasa da kasa, ba’a taba cimmawa ko a cikinsu da yaki, to fa sai an yi zaman an yi sulhu, saboda haka zaman lafiya ya fi zama dansarki, kuma ya kamata lallai su yi la’akari da wannan kuma su lura da ‘yan siyasar jamhuru, kar a zo a baka kudi a kauda gwaninka. Duk wanda ya baka kudi ka karba, dama can Allah ya riga ya tsara rabonka ne, amman ka yi abin da ya ke ingantacce.

In an zo kar a yi ya mutsi, duk wanda ya ga ba shi da nasara sai ta da yamutsi, ku kuma matasa ku dinga bai wa ‘yan Majalisunku shawara, ku ce masa mu fa yanzu akwai masu bukatar zuwa makaranta. Sannan akwai wadanda suke ‘yan kasuwa, muna so a taimake su ko da da jari ne.

 

Wani albishir za ka yi wa mutanen da kake wakilta:

To ni dai ina ga a ire-irenmu, wadanda aka zaba mu sani a karamar hukumata ko kuma a mazabar mu ta Gombe ta tsakiya, mu ‘yan majalisa guda biyu ne. Su kwatanta abin da na yi da kuma abin da ya ke yi a PDP ni kuma APC.

Sannan su kwatanta abubuwa mai girma Sanata Danjuma Goje ya yi a Gombe wanda yanzu muna tare da shi duk da dama can din  PDP ta ba shi, wannan karon ya ga PDP ba Za ta yi ba.

Ya dawo APC ya yi Sanatan farko yana PDP, yanzu da ya zo yana sunanta APC, kowa ya san ayyukan da ya kawo wa jihar Gombe ta tsakiya, ta ci uban na lokacin da yake PDP. To kuma duk yanzu a Nijeriya an daina yayin PDP. A jihohin Arewa nan fa, ina ba kwanakin baya  da Benuwe, da Sokoto suka yi batan-bakatantan ba? To kiran da zan yi wa jam’iyata, don Allah mu jajirce mu canza PDP a Gombe, ya kasance duka madafun mun sa APC in muna so Gombe ta ci gaba, don inda APC ne a ce ga Inuwa Yahya, ga Danjuma Goje, ga Gwamna APC ga ire-irenmu, da ci gaba ya wuce haka da Gombe ta ninka haka sau goma. Kuma da  shekara takwas dinnan da ba’ayi a banza ba inba haka,, ka dauki aikin ka kashe Naira biliyan uku, biliyan hudu, don kawai wai nan ka gama Firamare duk inda ka dauki makarantar Sakandire ka kasha mata miliyan dari ba karamin inganta su za ka yi ba

Gombe yanzu mutane ba wurin taro suke so ba, ina ruwanka da kashe kudi wai kai nan ka gina ‘International conference centre.?

Exit mobile version