Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna
Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani, ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da cewa cikin gaggawa ya samar da wani kwamitin wanda zai gudanar da bincike domin zakulo wadanda suke da hannu a mutuwar tsohon Shugaban kasa Marigayi Umaru Musa ‘Yar’ aduwa.
Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne, a shafinsa na ‘Facebook’, ya biyo bayan wasu maganganu da suka fara fitowa daga bakunan wasu jama’a.
Santan a inda ya kara da cewa, mutuwar Shugaban Kasa Umaru Musa ‘Yar’ aduwa, da yadda aka bayar da sanarwar rasuwar shi, tabbas da walaki goro cikin miya. Saboda haka ina kira da babbar murya ga Shugaban Kasa Buhari akan a gaggauta aiwatar da wannan bincike domin a zakulo musabbabin rasuwar margayi ‘Yar Aduwa.