Ya Kamata A Kafa Kwamitin Binciko Wadanda Suka Kashe Shugaba ‘Yar Aduwa -Sanata Shehu Sani

Daga Ibrahim Ibrahim, Kaduna

Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattawa Sanata Shehu Sani,   ya bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari,   da cewa cikin gaggawa ya samar da wani kwamitin  wanda zai gudanar da bincike domin zakulo wadanda suke da hannu a mutuwar tsohon Shugaban kasa Marigayi Umaru Musa  ‘Yar’ aduwa.

Sanata Shehu Sani ya bayyana hakan ne, a shafinsa na ‘Facebook’, ya  biyo bayan wasu maganganu da suka fara fitowa daga bakunan wasu jama’a.

Santan a  inda ya kara da cewa, mutuwar Shugaban Kasa Umaru Musa ‘Yar’ aduwa,   da yadda aka bayar da sanarwar rasuwar shi,  tabbas da walaki goro cikin miya. Saboda haka ina kira da babbar murya ga Shugaban Kasa Buhari akan a gaggauta aiwatar da wannan bincike domin a zakulo musabbabin rasuwar margayi  ‘Yar Aduwa.

Bayanin Sanata Shehu Sani ya zo ne biyo bayan wani furuci da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El Rufai ya yi a ranar taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC ta Jihar Kaduna, Inda gwamnan yace shi ba kanwar lasa ba ne,  domin sun fafata da tsohon Shugaban kasa ‘Yar Aduwa,   kuma hakan nan ya tafi ya kyaleshi. A  cewar Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed  El-Rufa’i.

Exit mobile version