Ya Kamata Kasashen Yammacin Duniya Su Lalubo Matsalolinsu Don Shawo Kansu

Daga CRI Hausa,

Babban mai sharhi kan tattalin arziki na jaridar Financial Times ta kasar Birtaniya, Martin Wolf ya rubuta wani sharhi a kwanakin baya cewa, ana kara nuna shakku ga ra’ayoyi da karfin kasashen yammacin duniya, don haka, tilas ne kasashen su lalubo matsalolin su tare da mayar da tsarin demokuradiyya bisa tafarkin da ya dace, don ceto kansu da kansu, amma bai wai nuna kiyayya ga kasar Sin ba.

A ganin Martin Wolf, cikin goman shekaru da suka gabata, an samu manyan lamura da dama a duniya kamar su yakin Afghanistan, da yakin Iraki, da rikicin hada-hadar kudi na duniya, da janyewar Birtaniya daga kungiyar EU da hawa kujerar shuganbancin Amurka da Donald Trump ya yi da sauransu, wadanda suka rage imanin jama’ar da suka amince da tsari da ra’ayin kasashen yammacin duniya.

Wolf ya bayyana cewa, idan kungiyar G7 ta bayyana goyon bayanta ga hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da ra’ayin kasancewar bangarori daban daban a duniya, da odar duniya bisa ka’idoji, dukkan jama’ar duniya za su zargeta, saboda ayyukanta sun saba da hakan.

A cewarsa, ba kasar Sin ce ta kawo barazana ga kasashe mafi samun kudin shiga masu bin tsarin demokuradiyya ba, matsalolin sun samo asali ne daga cikin kasashen.

Kana ya kalubalanci kasashen yammacin duniya da su yi watsi da tada rikici da kasar Sin, yana mai cewa, tilas ne a kiyaye bude kofa tsakanin kasa da kasa dangane da batutuwan da suka shafi cinikayya. (Zainab)

Exit mobile version