Ya Kamata Kungiyar Amnesty Ta Bar Nijeriya Ta Zauna Lafiya -Kungiyar Patriotic Elders

Wannan wata tattaunawa ce da MUHAMMAD ABUBAKAR ya yi da shugaban hadaddiyar kungiyar ‘yan kasuwa ta Nijeriya, Dr. BATURE ABDUL’AZEEZ, inda ya yi fashin baki kan dalilin da ya sa qungiyarsu ta ‘Patriotic Elders of Nigeria’ ta kalubalanci kungiyar Amnesty International kan goyon bayan masu zanga-zangar ENDSARS. Ga yadda hirar ta kasance:

Me za ka ce dangane cika shekara daya da zanga-zangar EndSARS?

Eh toh, wannan duk aikin Kungiyoyi irinsu Amnesty International ne. Sau da yawa dama sukan damu kasashe masu tasowa su ringa caccakarsu suna rura wutar rashin kishin kasa, ko rura wutar gaba da koyon bayan wasu tsirari masu taka doka.

Alal misali, yanzu abin da ya faru bara a Lekki da ke Legas, inda suka yi ta zuzuta cewa an kashe mutane 15, alhali karya ne. akan mutum 15 din nan har yanzu bayan shekara daya suna nan suna nema kafar haifar da rikici. Suna ta fada kan cewar an yi musu kisan gilla. Babban abin mamaki sun kasa nuna iyali ko ‘yan uwan ko da mutum daya da suka ce an kashe.

Za ka ga koda wanne lokaci wadannan mutane masu biyewa NGOs kodayaushe abin da turawa suke so suke yi, don suna amsan kudi a hannunsu. Su turawan nan ba su bari a aikata irin haka a kasashensu. Sai ka ga mutanen nan suna ba turawa da sauran al’ummar kasashen waje rahotonnin karya. Wannan lamarin na EndSARS ya tona asirinsu.

A boye suka shirya shirinsu suka so a tada hankalin kasar nan hade da irinsu Sowore. A takaice dai zanga-zangar ta janyo an kashe mutane da yawa. Saboda haka jihohin da suka kulla wannan magana ta EndSARS sun so su fake cikin zanga-zangar ‘yan kwadago, amma sai ya zama kaikayi ya koma kan mashekiya.

Yanzu irin wadannan jihohin da dama can barnace-barnace sun fi yawa, a wadancan jihohi SARS ke aiki, amma su suka kunna wuta aka dakatar da su. Toh yanzu da aka cire su, sai ya zama barna ta sake yawa a waadannan yankuna na Kudu. Duk duniya fa an san da irin wadannan kwararrun ‘yan sanda masu binciken barna ta musamman. Yanzu jihohin kudu guda 17 suna fuskantar matsaloli saboda rashin wadannan kwararrun ‘yan sanda.

A takaice, wadannan jihohin kudancin yamma da gabas suna fuskantar matsaloli. Yanzu suna girbar abin da suka shuka. Sune suka yi ta kone ofisoshin ‘yan sanda. Su jihohin Kudu maso gabas manufarsu ta tawaye ce. Ba su son motsi irin ta gwamnati, ta yadda ‘yan IPOB za su karbi iko. Da suka takurawa ‘yan sanda yanzu an wayi gari suna nan suna firgita junansu. Saboda a koyaushe ana iya kashe mutum ko iyalinsa. Abin da suka ga dama shi suke yi.

Wanne kira za ka yi wa ‘yan Nijeriya?

Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su guji wadannan NGOs din da ke yada jita-jita, su kansu NGOs kasashen da ke ba su kudi ba su kafu ba sai da doka da oda. Ita doka da oda dole ne a kiyaye ta, a ba mai hakki hakkinsa a kama mai laifi. Duk lokacin da aka ba mai laifi dama sai ya cutar da kasa.

Ina kira ga ‘yan Nijeriya da mu yi karatun ta natsu duk zantuttukan da miyagun ‘yan siyasa wadanda sub a kasar ba ce a gabansu, muna kira ga ‘yan nijeriya da su kasance cikin wannan kungiya tamu ta ‘Patriotic Elders of Nigeria’, kar mu yarda a yi amfani da mu a cutar da kasarmu.

Na kwashe shekaru ina mu’amala da Amurka, amma duk wadannan abubuwan da ake yi a Nijeriya su ba su bari a yi a kasarsu. Su kullum neman kasar da ba ta da hargitsi na siyasa don su haifar da damuwa. Misali, hatta korona ma ba yadda suka so ba kenan, sun so ta yi barna a Nijeriya da Afirka.

Mu kungiyarmu ta dattawa ‘yan kishin kasa mun danno kai, duk lokacin da wani marar kishin kasa ya ce, kule za mu ce masa as.

 

Exit mobile version