Ya Kamata Marubuta Su Daina Batsa A rubutunsu – Khadija Dahir 

KHADIJA DAHIR da ake wa lakabi da ‘Little Khadija’, matashiyar marubuciya kuma ‘yar kasuwa, ta yi jan hankali ga marubuta da su yi wa Allah su daina sanya kalmomin batsa domin yin hakan yana illa ga al’umma. Khadija ta yi wannan furuci ne a hirarta da wakiliyarmu RABI’AT SIDI. A sha karatu lafiya.

Da farko za ki fadawa masu karatu cikakken sunanki tare da dan takaitaccen
tarihinki.

To da farko dai sunana khadijat dahir wacce aka fi sani da ‘Little Khadija’ an haife ni 2001 a karamar Hukumar Daura, na yi makarantar firamare da sakandare duk a cikin garin Daura, sannan kuma na yi karamar ‘diploma’ a fanin aikin asibiti duk a cikin garin Daurar.


A yanzu kina ci gaba da karatu ne ko aiki ko ko dai wata sana’ar ake tabawa?
A’a bana aiki kuma na gama karatu, ina dai taba ‘yar sana’a ita ma ba sossai ba.

Kamar wacce irin sana’a kenan?

Garin danwake, yaji, Kori, ina yin ‘Packaging’ na zuba a ‘Containers’ mutane suna saya Alhamdullilah.

Me ya ja hankalinki har kika tsunduma cikin harkar rubutu, kuma za ki yi kamar shekara nawa da fara rubutun?

Tun farko ba ni da burin yin rubutu a ‘Online’ na yi niyyar buga littattafaina da kuma littattafan wasan kwaikwayo, sai na ga kafin na fara ya kamata na rika na ‘online’ saboda fadakarwa, wa’azantarwa tare da nishadantarwa, na fara rubutun ‘littafi na turanci online Nobel’ a Fabarairun 2019.

Wanne littafi kika fara rubutawa kuma me littafin yake kunshe da shi?

Na fara rubuta littafina mai suna  ‘Khadijatul Islam’ na wasu yara marayu guda biyu da mahafiyarsu ke rasuwa ta barsu hannun kishiya ta ringa azabatar da su a karshe daya ta rasu sakamakon abincin bera da ta ci ya rage sauran Khadijatul Islam.

To ya karbuwar littafin ya kasance lokacin da kika fara sakinsa, kasancewar
lokacin kina sabuwar marubuciya?
Kai gaskiya na ga zallar soyayya, masu kirana a waya idan ban yi rubuta ba, masu turo min sako, kai abin ba a cewa komai na ga kauna sossai har daga baya muna tare da su sakamakon ‘hackers’ da suka yi min kutse cikin ‘Whatapps’ na hakura da layin shi ya sa yanzu ba ma tare da wasu.

Lokacin da za ki fara rubutu shin kin nemi taimakon wani ko wata?

Gaskiya da kaina na shiga ba wanda ya taimake ni ko da da shawara sai mahaifiyata, da ta ce kar na yarda na zagi kabilar addini ko yaren wani.

Nawane adadin littattafan da kika rubuta, ko za ki iya fadowa masu karatu sunayensu?

Guda biyar, Khadijatul Islam, Yarima Salem, Yarima Asad, Nadiya, Rayuwar Munibat.

Wanne littafi kika fi so cikin littattafanki kuma me ya sa?

Na fi son littatafai biyu. Khadijatul Islam, yarima Salim, Saboda su suka haskaka ni duniya ta san da zamana khadeejatul Islam kuwa littafin ni kaina idan zan yi rubutu na kan yi hawaye.

Kin taba samun wata kyauta ta dalilin rubutu ko shiga wata gasa ta marubuta?

Gaskiya a ta fanin hakan ban samu ba, amman ba saboda ban taba shiga gasa ba sai bana da na shiga ta ‘Plateau writer’ shi ma muna jiran sakamakon.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a harkar rubutu?

Na sami kalubale da dama daga wajen marubta da wasu daga cikin makaranta amma dama sai da hakuri da kuma fadar gaskiya, ko da hakan zai bata wa wasu rai zan fada. Farkon fara rubutuna bayan na samu nasarori na fuskanci hargitsi daga wajen marubuta wasu har sukan yi min dariya dan na tura rubutu sau biyu a rana, haka dai suna yi min kallon ban kai ba.

To ya batun nasarori, wanne irin nasarori kika samu?

Kai alhamdullilah, tun da gashi sunana a duniya inda kafafuna ba su kai ni ba, sunana ya je inda ban je ba, Alhamdullilahi godiya ta tabbata ga Allah Nasarori Alhamdullilah.

Ya alakarki take da sauran marubuta a yanzu?
To zan iya cewa muna da kyakkyawan alaka sossai daga cikin wadansu muna gaisawa sossai kam.

Kamar da wanne lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?

Da dare da kuma safe.

Wanne abu ne ya taba faruwa da ke na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ki taba iya mantawa da shi ba ta dalilin rubutu?

Akwai wata rana da wata mata ta karanta littafin Khadeetul Islam kusan wata 9 na ma manta da wani abin da ke ciki, ta dauki lambata ta kira ni muka gaisa ta ce na tura mata ‘Account’ an ba da sako ta bani ba ta nuna min komai ba na tura mata sai ga 5,000 na kira na ce wa ya ba da ta ce “na karanta littafinki, kyauta ce na ji dadi sossai”. Babu na bakin ciki, Ba na ajjiye komai a raina wanda ma ya yi min kansa.

Wasu sukan dauki yin rubutu kamar hanya ce ta lallacewar tarbiyya ga su masu rubutun har ma da makarantan, me za ki ce akan hakan?

Zan iya cewa ko wane bangare da kashi hamsin-hamsin, saboda marubuta na sanya tsauraran kalmar da kwakwalwar makaranta ba ta dauka, saboda a ka’ida akan so a boye wasu kalmomin, amma wasu na kara buda ta. Duk yarinyar da kika ga ta lalace sanadiyar rubutu ita ma da laifinta da ta ji yadda yake me ya sa za ta karanta.

Shin kin taba buga littafi idan kin taba wanne da wanne kika buga?

A’a amma ina sa ran zuwa nan gaba kadan

Wasu sukan sai da littattafansu ta hanyoyi daban-daban shin ke ma kikan yi hakan ne, idan kina yi ta wacce hanya kike sayarwa?

Ban taba sayar da litattafaina ba.

Idan wani yana neman littafinki ta wacce hanya zai bi ya samu?

Akwai daban-daban amman an fi nema a Guruf-guruf “Groups”

Me kike son cimma game da rubutu?
Ina so na zama cikakkiyar mai rubuta Dirama,wasan kwaikwayo kuma ina da burin daukar nauyin fim “Producing’ fina-finan Hausa

Ko kina da ubangida ko uwar daki a harkar rubutu?

Eh! akwai yaya Jamil Nafsin.

A baya na ji kin yi maganar wasan kwaikwayo shin a yanzu kina hadawa da rubutunsa ne ko kuwa baki fara ba tukunna dai?

Na fara har na tura maidu global amman ba a gama tantancewa ba.

Wacece babbar kawarki a marubuta?

Muna gaisawa girma da arziki da kowa amma babu na daban.

A can baya kin yi bayanin tarihinki sai dai ba ki fada wa masu karatu ba shin kina da aure ko babu?

A’a ba ni da aure, ina fatan kafin shekarar nan sabuwar shekara na shiga daga ciki.

To ya batun karatu shin za ki ci gaba daga inda kika tsaya ko kuwa?

A’a ina da burin ci gaba har illa masha Allah.

Wacce shawara za ki ba wa sauran ‘yan uwa marubuta da su kan su makarantan?

Marubuta su daure su daina saka batsa a littattafansu, sannan a rage rubutun kudi barkatai ko da rubutun kudi da wanne makaranta za su ji, Makaranta ya kamata su dage da yin ‘comment’ saboda shi ma yana kara wa marubuta karfin gwiwa kuma saboda haka wasu marubutan ke mai da littafinsu na kudi.

Wacce shawara za ki bawa sauran ‘yan uwa mata na gida musamman marasa aikin yi?

Gaskiya idan har mutun bai sami karatun zamani ba ya kamata ya kama sana’a duk kankantar ta, Saboda rufa wa kai asiri duk gatanka duk kudin gidanku bai kamata ku zauna ba aikin yi ba.

Ko akwai wani kira da za ki yi ga gawamnati musamman game da marubuta?

Ina kira ga gwamnati da su waiwayo su kalli marubuta muna da bukatar tallafi sossai daga wajen gwamnati rubutu saboda muna taka rawa wajen fadakarwa fiye da ko wa a iya karkato da hankalin jama’a.

Wanne irin abinci kika fi so da abin sha?

Na fi son wake da shinkafa da kuma Kunun Aya.

Wanne irin kaya kika fi son sakawa?

Atamfa ‘cotton’ Ina jin dadin amfani da ita.

Me za ki ce da LEADERSHIP Hausa?

Gaskiya ina alfahari da wannan gidan jarida ko ba komai shi ne gidan jarida na farko da ya taba hira da ni ina mashi fatan alkhairi Allah kara dauka ta da ma’aikatan ta.

Ko kina da wadanda za ki gaisar?

Ina gai da mamata Hajiya Usaina, ina gai da yayyena da kannena ‘yan gidanmu, ina kuma gai da yaya Jamil Nafsin tare da duk kawayena da abokan arziki tare da makaranta littafina ma’ana masoyana.

 

Exit mobile version