Ya Kamata Marubuta Su Tsaftace Alkalumansu – Ummyn Yusrah

Marubuta

Fitacciyar marubuciyar nan ta shafin intanet (yanar gizo) Malama Sakina Salisu wacce aka fi sani da Ummyn Yusrah, ta yi kira ga takwarorinta marubuta da su tsaftace alkalumansu yadda zai zama abubuwan da zai amfani al’umma kawai za su rika rubutawa ba wai akasin haka ba, kamar yadda wasu jama’a ke koke a kan irin batsar da ake sakawa a cikin rubuce-rubucen zube a halin yanzu. Marubuciyar dai ta yi wannan kira ne a lokacin da take tattaunawa da wakilin LEADERSHIP HAUSA, Adamu Yusuf Indabo. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:

 

A farko masu karatu za su so jin cikakken sunanki da kuma takaitaccen tarihinki?

Assalamu alaikum. Godiya mai tarin yawa, da wannan dama da aka ba ni.

Da farko dai sunana Sakina Salis Al-Imam, wacce aka fi sani da Ummyn Yusrah. An haife a ranar 2/3/1989 a cikin garin Bauchi, na yi makarantar Addini da na zamani daidai gwargwado. Yanzu haka kuma ina da aure da yara hudu Biyu maza, biyu mata. Sadeek, Fatima (Yusrah), Isah (Labeeb) sai kuma Hauwa’u (Afrah).

 

To Allah ya raya ya albarkaci rayuwarsu. Hajiya Sakina, an san ki gwana ce a fagen rubutun kirkira musamman ma a yanar gizo. Shin ko me ya ba ki sha’awar fara yin rubutu?

Allah Ameen. Na gode.

(Dariya) Ai ban zama gwanar ba tukunna. Har yanzun koyo muke. Kuma ba ni na zabi rubutu ba, zan iya cewa rubutun shi ya zabe ni, domin a da ban taba tunanin zama marubuciya ba, rana daya na tsinci kaina da alƙalamina a fagen Marubuta. Kuma Alhamdulillah! Ina alfahari da hakan.

 

Kin san marubuta wasu na fara rubutu ne saboda faruwar wani abu da ya shafi rayuwarsu, wasu kuma tsintar kai cikin marubuta ne ko kuma yawan karance-karance. Shin ke mene ne ya zama tsaninki na fantsama duniyar rubutu?

Hadakar wasu matasa da suka yi, na aurar da daya daga cikin su shi ne ya burge ni, har na yi rubutu a kai, don haka zan iya cewa wannan shi ne tsanina.

 

To tun yaushe kika fara rubutu, kuma wanne littafi kika fara rubutawa?

Na fara rubutu a watan sha daya, shekara ta Dubu Biyu da Goma sha Bakwai (11/2017) Amma ba zan iya tuna ranar ba. Na fara da rubuta labarina mai suna ‘Auren Awa Ashirin Da Hudu.’

 

Littafin ki da kika fara rubutawa ‘Auren Awa Ashirin Da Hudu’ a takaice me littafin ya Kunsa?

Littafi ne da yake nuni ga muhimmancin hadin kai, taimakekeniya tsakanin matasa, da kuma kishin juna. Labarin ya ginu ne a kan; Wata yarinya da za a yi aurenta, ana gobe daurin aure mijin ya ce ya fasa, kafin ka ce kwabo! Zance ya zaga unguwa. A wajen hira irin na matasa, sai aka tayar da zancen, daya daga ciki ya nuna tausayawarsa gare ta, har ma ya furta da yana da hali da ya aure ta a goben. Bayan abokan sun tabbatar da gaske ya ke yi, shi ne suka harhada duk wani abin da ya dace na neman aure, a Wannan daren. Zuwa washegari aure ya koma kansa. Hakan ya burge ni matuka. Wanda hakan ce ta faru a gaske kuma ya yi tasiri a zuciyata shi ya sa na mayar shi littafi.

 

To daga fara rubutunki tun watan 11 na shekarar 2017 zuwa yau, kin rubuta littafai nawa?

Yanzu haka na rubuta littattafai Sha Hudu (14) su ne: 1) Auren Awa Ashirin Da Hudu. 2) A dalilin Link. 3) Yesmin. 4) Rayuwar Asiya. 5) Sai Na Auri Mijin Nobel. 6) Rayuwar nobel. 7) Mawaƙi ne. 8) Ka Ki naka… 9) Mijin Bahaushiya Ko Matar Bahaushe. 10) Abulle Ta Mai Unguwa. 11) Rayuwar Lubna. 12) Ta Fi Bagaruwa Iya Jima. 13) Kowa nobel. 14) Marubuciya ce.

 

Lallai kin rubutu. To a cikin wanne ne bakandamiyarki?

Gaskiya ba zan iya cewa ga bakandamita ba, domin ko wanne da rawar da ya taka.

 

To wanne makaranta suka fi yabawa a cikin littattafan naki?

Gaskiya makaranta sun fi son ‘Abulle Ta Mai Unguwa’ don sun fi yaba shi fiye da sauran.

 

Kuma cikin littattafanki 14 wanne ne ya fi ba ki wahala wajen rubutun sa?

‘Ka Ki Naka…’ Domin har yanzu ban kammala shi ba. Amma ba wahala ya ba ni ba, rubutunsa ne ya fita a raina shi ya sa na ajiye shi gefe. Zan karasa In Sha Allah nan ba da jimawa ba.

 

Dama ana fara rubuta nobel ya fita daga kan marubucin?

Hakan za ta iya yuwu. Sai ka dauko labari daga baya kuma ka ji komai ya tsaya, abu mafi a’ala sai ka bar shi, domin idan ka matsa sai ka ci gaba, za ka rubuta abinda ba shi ne ba. A nawa fahimtar fa. Amma zan tambayi manyan malamaina. (Dariya)

 

Au, kina da wani ubangida ko malamin da yake bibiyar rubutunki kafin ki wallafa don ba ki shawarwari ko gyara a inda kika kuskure ke nan ko?

Sosai ma, kasantuwar muna da kungiya Hazaka Writers Association a can muke komai, muna da manyan malamai da ke zame mana ido a harkar rubutunmu.  A bayan fage kuma muna da babban Malaminmu Kabir Anka, bayan shi muna da irin su: Almu Dakata, Badiyya Adam, Muttaka A Hassan, Bamai A Dabuwa, Musaddam Idris, Abu Hisham. Sannan ba sai lallai su ba, ko a cikin makaranta aka min gyara ina jin dadi da farin ciki.

 

Kasancewarki marubuciyar online, ko kina da burin buga littafi a nan gaba?

Sosai nake da burin ganin littafina a tafin hannuna.

 

A cikin ‘yan uwanki marubuta, wace aminiyarki da koyaushe za a iya jin labarinki ko halin da kike ciki daga gare ta?

Duk ‘yan kungiyarmu ta ‘Hazaka Writers Association’ muna da kusanci sosai da su, za a iya samun labarina daga gare su In Sha Allah.

 

To a rayuwarki me kika fi so, kuma me kika fi tsana?

Ina son na ga na sanya duk wanda ke tare da ni farin ciki, kuma na tsani bata wa wanda ke tare da ni.

 

Mene ne babban burinki a rayuwa?

Babban burina in yi rubutu al’umma su amfana da shi.

 

‘Yan uwanki marubuta wanne kira za ki gare su?

Su tsabtace alƙalaminsu, su rubuta abinda al’umma za su amfana da shi, abinda ko bayan ransu zai amfani al’umma. Su kauce wa rubuta akasin haka.

 

Wane kira za ki ga makarantanki da koyaushe suke bibiyar rubutunki?

Kirana a gare su su yi amfani da darussan da ke cikin abinda suke karantawa daga rubutuna, su yi watsi da akasin hakan. Gyara ko shawara kuwa duk ina maraba da su.

 

To Malama Sakina muna godiya da lokacin ki da kika ba mu…

Ni ce da godiya, Allah ya saka da alkairi ya kara daukaka wannan jarida da ma’aikatanta baki daya. Ya kawo dumbin nasarori. Ameen.

 

Exit mobile version