Ya Kamata Matsalar Ƙuncin Rayuwa Ta Ragu A Nijeriya –Sheikh Muhammad

SHEIKH MUHAMMAD MUHAMMAD SARKI Mataimakin shugaban Majalisar Malamai na Ƙungiyar Izala ta Jihar Nasarawa, Malami ne wanda ya shahara wajen amsa fatawa a kafafen watsa labarai. Wakilinmu MU’AZU HARƊAWA ya tattauna da shi kan matsalolin da musulmi har ma da waɗanda ba musulmi ba ke ciki a Nijeriya da yadda za a gyara su a samu sauƙin rayuwa, ga yadda hirar ta kasance:

TAMBAYA: Akaramakallah wace nasiha ka ke da ita ga dukkan musulmi game da halin da ake ciki na rashin zaman lafiya a wasu sassan Nijeriya?

USTAZ MUHAMMAD SARKI: Bismillahir-rahmanir-rahim wassalatu wassalamu ala Rasulullah, Assalamu Alaikum. Matsalolin da ake ciki a halin yanzu akwai buƙatar kowa ya riƙa tunanin hanyar magancewa. Kuma duk mutumin da baya la’akari da hakan gaskiya ba shi da tunani mai kyau, amma mai cikakken tunani idan yana hango damuwa a nesa to yana tunanin za ta iya matso inda yake. Don haka akwai buƙatar duk ɗan Nijeriya ya fara tunani game da halin da ake ciki. Don haka nake kira ga al’ummar musulmi musamman na yankunan da wani bala’i ke aukuwa kamar na rikicin book haram da garkuwa da mutane da rikicin Fulani da makiyaya ko rigima tsakanin ƙabilu ko kan bambancin addini ko aƙida ko tsanannin cututtuka da talauci da ake fama da su. Neman yardar Allah (T) shi ne ya kamata dukkan mutane su sa a gaba kowane lokaci walau suna cikin jin daɗi ko cikin wahala. Allah yana kawo jarrabawa a lokacin da mutane suka yawaita laifuka domin ya zamo darasi ga masu kyakkyawar fahimta su koma ga Allah saboda shi ne hanyar kuɓuta daga kowane bala’i. Allah maɗaukakin Sarki yana cewa; “Bayyanar ɓarna a tudu da koguna sai Allah ya kawo jarrabawa da masifa ko hakan zai sa su tuba su dawo kan hanyar ƙwarai”.

A Nijeriya Allah kaɗai ya san laifukan da ake aikatawa, saboda akwai wuraren da suke miya da naman mutum akwai masu tsafin yin kuɗi da naman mutum akwai waɗanda suka mayar da ’ya’yan mutane kamar sune abubuwan biyan buƙatu na rayuwa. Bala’o’i ga su nan basu ƙirguwa, kuma sune ke sa Allah ya kawo jarraba ta bala’i domin hakan ya zame mana darasi don mu koma ga Allah.

Sahabban Manzon Allah (SAW) tsarkaka ne, amma a lokacin da aka je yaƙin Uhudu Manzo ya sanya wasu mutane a wani waje ya ce su tsaya su lura da wajen ko sun ci nasara kar so sauƙo don taya su murna kuma ko da za su ga ana yayyaka su kar su sauƙo, idan an gama yaƙi dukkan ganimar da aka samu tare za a raba,  kar su sauka sai ya musu izini.

Amma a lokacin da mutanen suka ga an ci nasara ana kwasar ganima sai suka bijire wa umarnin Manzo suka sauƙo, a wannan dalili Allah ya jarrabi musulmi aka karkashe sama da mutum saba’in, duk sakamakon ƙauracewa umarnin Manzo (SAW) ƙwaya ɗaya. To idan mun yi la’akari da Nijeriya a yanzu umarninsa nawa ake lalatawa a kowane ɓangare ba adadi. Balle wancan lokaci na sahabbai tsarkaka guda ɗaya aka lalata amma ga abin da ya biyo baya.

TAMBAYA: Ina mafita game da halin da ake ciki?

USTAZ MUHAMMAD SARKI: Ya zamo wajibi kowa ya yi wa kansa faɗa, saboda kowa ya san laifin da ya ke aikatawa a ɓoye da bayyane, idan kowa ya ji tsoron Allah, zai kawo sauƙi al’umma su samu rayuwar salama, kowa ya maida buƙatarsa ga Allah ya tuba don Allah ya sa sanadiyyar wannan bala’i ya zamo hanyar yafewa kowa laifukansa. Waɗanda kuma ba wannan bala’i a wajen su kowa ya matsa da addu’o’i da roƙon Allah da shigar da Malamai na kirki cikin lamarin don su taimaka da addu’ah da bayanai na lallashin jama’a don a samu cin nasara, da fatar Allah ya kawar mana da kowane bala’i ya zamo labari. Idan muka duba abin da ya faru a jihar Borno su Yobe da Adamawa da Nasarawa a shekarun baya inda wani bala’i na kashe-kashe ya riƙa aukuwa fiye da yanzu, wannan abune mai ciwo. Gaskiya akwai buƙatar mutane da gwamnati kowa ya zo mu faɗaɗa tunani wajen ganin ba a sake samun wani abu makamancin haka ba. Gaskiyar Magana akwai mutanen da ba a san suna mugun aiki ba amma suna yi a ɓoye domin abin da ke faruwa a yankin arewa ke aukuwa saboda mutanene masu imani da yarda da addini da ƙaddara mai kyau da maras kyau muna sallamawa Allah komai, amma ya jarrabe mu da wannan bala’i, alhali a can baya wannan baya faruwa.

Kuma idan muka duba za mu fahimci cewa matsallolin ba duka ne suka zo ba, saboda idan ka ɗauki yin garkuwa da mutane har yanzu baƙo ne a arewa sai yanzu ya matso sosai, don haka mu yi la’alkari da misali, ‘yan Boko Haram ina suke samun makamai? Saboda harsashin da ake harbawa saye ake yi kuma idan sun yi karo da jami’an tsaro za su yi asarar harsasan har bingigogin su manya da ƙanana to duk ina suke samo wasu, kuma har yanzu basu ƙare ba. Mai yiwuwa akwai waɗanda ta yiwu suna da hannu da shuni ko wata dama suna tallafa musu don ganin ba a zauna lafiya ba. Don haka waɗanda ke cikin gwamnati ya kamata su taka

muhimmiyar rawa wajen gano yadda waɗannan matsaloli suke, saboda a wasu wurare akwai waɗanda suka mayar da tashin hankali a matsayin hanyar su ta samun nasara a kan a bin da suka sa a gaba.

TAMBAYA: Me za ka ce kan matsalar Boko Haram a Nijeriya?

USTAZ MUHAMMAD SARKI: Bai kamata a ce matsalar Boko Haram har yanzu tana nan a Nijeriya ba, ya kamata a ce ta ƙare gaba ɗaya,  gwamnati ta faɗaɗa tuni kan wannan lamari don a kawo ƙarshen sa. Saboda wuraren da ake kai harin sojojin da ya kamata a ce sun bamu kariya, to suma da kansu ba su tsira ba har yanzu bugawa ake yi, amma mun gode Allah da irin nasarar da wannan gwamnati ta samu abin ya ragu sosai, mutanen wurin da abin ke ci gaba da faruwa sai su sa ido su temaki hukuma don ganin wannan abu ya zo ƙarshe. Don haka muke gani kamar akwai wani munafurci cikin lamarin kowa ya faɗaɗa tunaninsa da addu’a don Allah ya nuna mana gaskiyar masu hannu cikin lamarin.

Misali abin da ya faru a Nasarawa an kashe kusan ‘yan sanda tas’in cikin kayan aiki da SSS sun kai goma amma har  yanzu ba abin da aka yi kuma abin mamaki Daraktan SSS ya fito ya ce sun yafe musu to fisabilillahi ya za a ce ƙasa ta zauna lafiya. Kuma lokacin da aka kashe waɗannan jami’an tsaro ina bindigogin su, anya ba wasu mutane ke haddasa wannan bala’i domin neman biyan buƙatun su ba a lokacin gwamnatin da ta gabata?

TAMBAYA: Menene shawarar ka ga shugabanni?

USTAZ MUHAMMAD SARKI: Shawarata ga gwamnati da shugabanni a taimaka kar wani mutum ya kasance ya fi ƙarfin doka, don haka ya kamata majalisa su ci gaba da aikin da aka fara a baya na niyyar fito da doka wacce za ta iya kiran kowa gabanta duk wanda ya aikata laifi a masa Magana shi ne zai kawo ci gaba a samu zaman lafiya a ƙasa,  mu fita a wannan mummunan yanayi. Kuma su masu riƙe da madafun iko na sani ko musulmi ne ko kirista kowa ya yi imani aikin da yake yi Allah zai tambaye shi.

Kuma kowa ya sani duk abin da ya aikata zai je gaban Allah ya amsa tambayoyin da za a masa idan ya aikata mai kyau ko mummuna Allah zai tambaye shi.

Kuma a gefen talakawa, Allah yana son talaka saboda ba wai Allah ya hana shi abin duniya saboda ba ya son sa bane, a’a wanda Allah ya ba abin duniya idan da ya san matsalar da ke ciki shi ne zai fahimci ba a son sa an ɗora masa nauyi mai yawa, Allah yana son wanda yake cikin mawuyacin hali don ya yafe masa zunubbansa, idan ka yi ƙoƙarin ƙuntata masa Allah yana kallonka kuma zai iya ɗaukar kowane mataki na hana ka sukuni kan mulkin ka kasa dangana ga kuɗi amma  ka kasa zama lafiya.

Duk karatun musulunci ya fahimtar da mu wannan tun tuni. Idan muka ɗauki labarin Annabi Musa da Fir’auna za mu ga akwai darasi mai yawa Allah ya halakar da Fir’auna da mutanensa mulki ya dawo hannun Bani Isra’ila. To haka lamarin zai kasance a ko ina talakawan za a wayi gari mulki ya dawo hannun su. Ya kamata kowa ya sani Allah yana jin zafi kan hakkin talaka idan an tauye.

Misali abin da ke faruwa a jami’o’i duk manya sun fitar da yaran su ƙasar waje amma na talakawa suna gida, masu mulki basa tunanin sauke hakkin talaka da ke wuyansu. Yaya za a fahimci juna?  Don haka ya kamata ‘yan arewa su riƙe martabar su don  martabar kowa ta dawo, musamman mutanen mu waɗanda suke cikin gwamnati kuma Allah ya basu mulki a yanzu, suna wasa da damar su yadda wasu har za su ƙare basu taimaki mutanen su ba. Kuma duk irin matsayin da mutum ya hau ya kasance da masaniyar dole a kwana a tashi zai bar wannan kujera. Don haka idan bai yi abin a zo a gani ba haka zai kasance ya sauka ya lalace.

Musamman a wannan lokaci da duk wata fatar ɗan Nijeriya ta samun ingancin rayuwa ta dogara kan wannan gwamnati, amma kuma sai aka samu akasi matsaloli da cututtuka da yunwa da fatara da rashin aikin yi suka shigo suka raba tunanin mutane kan fatar samun inganci rayuwa. Don haka ya kamata shugaban ƙasa da muƙarrabansa su tashi tsaye wajen yin sassauci a kan wasu manufofin gwamnati don mutane su samu sauƙin gudanar da rayuwa yadda ya kamata. A farfaɗo da darajar kuɗi a samar da kayan aikin gona da tallafi kan noma da sana’a don ba mutane don su

inganta rayuwar su komai ya wadata.

Kuma abin mamaki ne yadda ‘yan siyasa a Nijeriya waɗanda kwaɗayin talaka na kan su, amma an wayi gari yau su ne ke faɗa a majalisako a kafafen labarai, abin da ke nuna alamun akwai kamar wuya gyaruwar al’amurran da ake ciki na wahala a Nijeriya, shi yasa kullum komai sai

ƙara taɓarɓarewa ke yi.

Da fatar kowa zai hankalta ya yi wa kansa faɗa ya kuma gyara duk wani abu na aiki da ke tattare da shi domin Allah ya gyara mana, da fata Allah ya mana jagora ya bamu ikon gyarawa.

 

Exit mobile version