Ya Kamata Mbaka Ya Mayar Da Martani Game Da Zargin Neman Kwangila – Omokri

Mbaka

Tsohon mashawarcin tsohon shugaban kasa Good luck Jonathan, Reno Omokri, ya yi kira da babban limamin kirista na Jihar Inugu, Ejike Mbaka ya mayar da martani a kan zargin da fadar shugaban kasa take masa na neman Kwangila.

Mbaka ya bukaci a tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon halin rashin tsaro da ake fuskanta a Nijeriya.

Da yake mayar da martani, mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Garba Shehu ya zargi Mbaka da nema kwangila daga wajen shugaban kasa. Shehu ya yi ikirarin cewa, Mbaka ya huce ne a kan shugaban kasa lokacin da ba a ba shi gwangila ba.

Da wannan ne Omokri ya bukaci fasto da ya mayar da martani a kan zargin neman Kwangila daga hannun shugaban kasa Buhari.

A shafinsa na tweeter, tsohon mashawarcin shugaban kasa ya rubuta cewa, “fasto Mbaka ya yi gum game da zargin da fadar shugaban kasa take masa. Shin ka nemi Kwangila daga wajen shugaban kasa Buhari ko kuma baka nema ba?

“Har bayan awanni 24 ban sami amsar daga wajen Mbaka ba a kan ya bukaci neman kwangila ko kuma bai nema ba.

“Mai magana da yawun shugaban kasa ya Tabbatar da haka, yanzu saura Mbaka ya fito ya kare kansa a kan ya nema ko kuma bai nema ba.”

Mbaka wanda ya goyi bayan Buhari a zaben 2015 da 2019, a yanzu kuma ya nemi Buhari ya sauka ko kuma a tsige shi, saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan.

Jam’iyyar APC ta ragargaji babban limamin kirista, Mbaka, wanda bayan ya shafe shekaru yana goyon bayan shugaba Muhamamdu Buhari, a wannan karon kuma ya kware masa baya, ya ce ba ya iya samar da tsaro a Nijeriya, don haka ya sauka kawai. APC ta ce kalaman da Mbaka ya yi amfani da su sun yi tsaurin da za su iya haddasa tarzoma a kasar nan. Kakakin APC Yekini Nabena, ya yi barazanar kai karar Mbaka a babban cocin katolika, idan ya ci gaba da kinkimo danyar magana yana dankara wa gwamnatin tarayya.

Mbaka wanda shi ne shugaban cocin Adoration Ministry da ke Inugu, kwanan nan ya yi kira ga majalisar tarayya ta tsige Sshugaba Buhari idan ya ki sauka saboda ya kasa samar da tsaro a kasar nan. Mbaka dai ya yi wannan furuci a cocinsa, inda ya yi kira ga fadar shugaban kasa ta gaggauta kawo karshen matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Yekini Nabena ya ce kamata ya yi Mbaka ya maida hankalin da wajen ibada a cocinsa, maimakon ya rika tsoma baki cikin siyasa, wadda babu abin da ya sani a cikin ta ko a wajen ta.Ya kalubalanci Mbaka ya yi amfani fa cocinsa wajen yin addu’o’in neman zaman lafiya a kasar nan.Ya nemi Mbaka ya yi koyi da Yesu Almasihu, wanda ya ce ya bi hukuma sau da kafa a rayuwarsa, har zakka ya rika biya. Ya nemi Mbaka ya maida hankali a coci, ya kyale ‘yan siyasa su yi siyasar su.

Exit mobile version