Ya Kamata Mutane Su Zabi Wadanda Ba Za Su Guje Su Ba – Kwamishinan INEC A Bauchi

Hukumar zabe mai zaman kanta a Nijeriya, INEC, na ci gaba da gudanar da shirye shirye don tunkarar zaben shekara ta 2019, inda ranar 8 ga Janairu, 2018 ta fitar da jaddawalin shirya zaben gama gari a Nijeriya wanda a ke sa ran za a gudanar da dukkan shirye shirye daga wannan shekara har zuwa shekarar zaben. Ganin yadda ofisoshin hukumar suka himmatu don rijistar masu yin zabe da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan yadda zaben zai gudana, don haka wakilinmu a Bauchi, MUAZU HARDAWA, ya tattauna da Kwamishinan hukumar zabe ta kasa INEC a jihar Bauchi, ALHAJI ABDULLAHI IBRAHIM, a lokacin da ya zauna da masu ruwa da tsaki kan siyasa da zabe don ganin an yi komai cikin nasara da bin doka da oda. Don haka ga yadda tattaunawar ta kasance:

Wane shiri wannan hukuma ta INEC ke yi wajen ganin ta samu nasara a zabuka masu zuwa?

Na kira kwamitin masu ba da shawara kan jam’iyyun siyasa don na fayyace musu halin da ake ciki game da shirin zaben 2019, da jan hankalin su don su kasance masu bin doka ganin an saki jaddawalin zabe, saboda tun shekarar da ta wuce muke kiran su fito su wayar da kan jama’a don su  su fara shirin zabe, inda suka koka da karancin wurin sabunta rijista a yankunan karkara.  Don haka muka mika kukansu ga manyan mu kuma sun amsa an samar da karin wurare a helkwatar kananan hukumomi da kauyuka inda ake bin mutane ana musu rijista, don mun fahimci a Jihar Bauchi akwai wurare masu nisa, saboda haka ake bi daga wannan kauye zuwa wancan, don haka ya zamo wajibi mutane su himmatu wajen ganin sun je sun sabunta ko sun yi sabuwar rijista sau daya bisa yadda doka ta tanada. Don haka muke son shugabannin al’umma da malamai da ‘yan siyasa da sauran mutane su wayar da kan jama’a don a samu mutane su fito su yi abin da ya dace game da shirin zaben. Ba ma son mutane su yi sakaci sai lokacin zabe ya zo sannan su tashi a gaggauce suna yin abin da ya kamata a ce sun yi da jimawa, don haka mu ke son kowa ya shirya wajen yin abin da ya dace don a samu yin shiri a lokacin da ya dace saboda kowa ya zabi wanda ya  ke so ba tare da samun korafi ko wani tashin hankali ba, fatar gwamnati shine kowa ya yi zabe lafiya ya zabi wanda ya ke so don a samu jagoranci na gari da mutane ke ganin zai  samar da inganci rayuwa da ci gaban da suke so.

 

Wace shawara ka ke da ita ga ’yan siyasa da masu zabe don ganin an samu nasara?

Shawarata ga wanda suke son tsayawa takara shi ne su bi doka su bi tsarin mulki kamar yadda kowace jam’iyya ke da shi idan an bi gaskiya an bi tsari to ba za a samu zubar jini ko tashin hankali a lokacin zabe be. Su kuma masu zabe su tabbatar sun zabi wanda zai share musu hawayensu da lura da matsalolin su kar su zabi wadanda idan sun hau sun tafi kenan ba za su sake ganin su ba sai ko su tafi sai lokacin da suke so a sake zabar su kafin su dawo suce suna neman goyon bayan mutane don haka sai ka ga mutane cikin wahala gwamnati na samar da ci gaba amma idan ba ku da wakili na gari kullum yankin ku sai ko ya ci baya shi kuma yana ta tare dukiya daga shi sai iyalensu, don haka mutane su lura su yi abin da ya dace don ci gaban su da na yankunan su.

 

Ko ka na da wata shawara ta musamman ga jama’a kan wannan aiki naku?

Shawarata ita ce mutane su zauna lafiya su gudanar da siyasa cikin tsabta da bin ka’ida da nuna sanin ya kamata, su nisanci kwadayi da zalama ko tayar da hankli, su bi dokokin hukumar zabe ta kasa da dokokin jam’iyyun siyasarsu yadda ya dace komai ya tafi cikin tsari, shine za a samu ci gaba. Gwamnati a kullum tana son ganin an zauna lafiya an yi zabe lafiya an samu sakamakon da kowa zai gamsu da shi a samar da shugabannin da mutane suka yi rinjaye wajen samun nasarar su, don haka ba a bukatar magudi ko tashin hankali game da zabe sai zaman lafiya da yin abin da mutane za su yarda da juna su kuma zauna da juna lafiya. Kuma a sani gwamnati a shirye ta ke wajen hukunta duk wanda ya taka dokar zabe ko dokar kasa ko wanda ya tayar da hankulan jama’a. Kuma mutane su sani fitar da jaddawalin zabe da aka yi muhimmin lamari ne da ke nuna komai ya kusa kammala nan ba da jimawa ba lokaci zai zo wanda za a gudanar da zabuka kamar yadda gwamnati ta tsara. Da fatar mutane za su ci gaba da nuna halin sanin ya kamata da kishin kasa da bin doka don kare lafiya da mutunci, Allah ya temake mu yasa a samu nasarar wannan aiki kamar yadda aka shirya gudanarwa.

Exit mobile version