Mustpha Abdullahi" />

Ya Kamata Shema Da Mutanen Umaru Musa Su hada Kai – Kwamared Imrana

Kamar yadda wakilinmu ya tattauna da wadansu ‘yayan jam’iyyar PDP na Jihar Katsina game da halin da ake ciki a jam’iyyar, wakilinmu ya fahimci cewa akwai wata gagarumar matsala da ke addabar jam’iyyar tare da ‘yayanta baki daya na rashin hadin kai tun daga sama har kasa wanda wadansu da aka tattauna da su ke bayyanawa a matsayin wani babban cikas da ke hana jam’iyyar samun nasara a Jihar Katsina duk da cewa PDP ta samu nasarar yin Gwamna a Jihar na tsawon shekaru 16 da suka gabata a can baya.

 

Duk da irin wannan nasarar da PDP ta samu na tsawon shekaru amma ‘yayan jam’iyyar musamman a tsakanin manya manyan da suka samu nasarar dorewa a bisa mukamai daban daban tun daga matakin Jiha zuwa kasa wato a cikin Gwamnatin tarayyar Nijeriya a halin da ake ciki akwai wadansu bangarorin da basa ga Maciji da Juna sakamakon tsananin sabanin da suke fama da shi a tsakaninsu.

 

Bangarorin da suka fito fili kamar yadda wadansu ‘yayan jam’iyya suka shaidawa wakilinmu cewa akwai matsalar rashin jituwa tsakanin tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema tare da wasu mutanensa da kuma bangaren tsohon shugaban kasar tarayyar Nijeriya Marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’aduwa, wato ainihin mutanensa da ya yi aiki tare da su tun daga matakin Jiha wasu ma sun samu nasarar ci gaba da dare wadansu manya manyan mukamai a matakin Gwamnatin tarayya.

 

Amma kuma a halin yanzu wadannan bangarorin biyu na mutanen Marigayi Umar Musa da kuma na Barista tsohon Gwamna Ibrahim Shehu Shema dukkan bangarorin basa ga maciji da Juna, saboda tsananin son rai kawai.

 

Saboda binciken da wakilinmu ya gudanar a tsakanin ‘yayan jam’iyyar sun tabbatar masa da cewa wannan halin rashin hadin kai na kawo wa duk wani kokarin samun nasara koma baya ga jam’iyyar tare da ‘yayanta baki daya.

 

Kamar yadda mambobin jam’iyyar PDP da ke da katin rajistar jam’iyyar suka shaidawa wakilinmu cewa, duk wani yunkurin da suke yi na samun nasara a lokutan zabe da kuma wadansu harkokin da za a gudanar ba su samun nasara saboda rarrabuwar kawuna tsakanin jiga Jigan jam’iyyar.

 

Babban dalilin da yasa bamu ambaci sunayen da wadansu ‘yayan jam’iyyar suka shaida mana ba a lokacin gudanar da wannan bincike sai sunan tsohon Gwamna da kuma mutane irinsu Muttaka Rabe da ya taba zama tsohon Kwamishina a Jihar Katsina lokacin Marigayi Umaru Musa na Gwamna da kuma zama Jagoran hukumar PTDF a lokacin marigayin na Shugaban kasa amma rashin jituwa ya Sanya sun kasa hada kawunansu domin PDP ta ci gaba da samun nasara kamar yadda suka samu a can baya tsawon shekaru duk da cewa akwai dangantaka mai karfi tsakanin bangaren Shema da na mutanen Umaru Musa, domin ci gaban jam’iyya tare da ‘yayanta baki daya amma a irin wannan tsarin na rashin jituwa a tsakanin Juna, hakika ba zai taimaki kowa ba.

 

Koda yake kamar yadda wakilinmu ya tattara bayanai a tsakanin mutanen da ya tattauna da su akwai wadanda suka rika gaya mana cewa a cikin yanayin da jam’iyyar PDP reshen Jihar Katsina ta shiga akwai wadanda suke amfana da halin da ake ciki.

 

Kamar yadda mutanen suka bamu misalai cewa a wasu lokutan idan za a yi wadansu abubuwa na jam’iyya da ake amfana to, kowane ke samun irin wannan amfanin ba kamar yadda aka san jam’iyyar PDP na aiwatar da tsarinta ko me za a yi idan abin ya taso daga sama zai dire har kasa, wato kowa zai iya amfana.

 

Amma mambobin na PDP sun koka da irin yadda a halin yanzu lamari ke tafiya tun da babu hadin kai tsakanin manyan jam’iyya, koda an yi wani tsari na samun amfani ba kowa zai shaida ba tun da ana zaman yan marina ne wato kowa da inda ya Sanya gaba.

 

Saboda haka yan jam’iyya na can kasa ne ke shan wahala duk da cewa suke yi wa jam’iyya aiki kasancewa su ke tare da jama’a, koda lokacin zabe su za su tabbatar an samu nasara tun daga matakin akwatin da ake Jefa kuri’a kuma cikar dan siyasa ya zama wani abu shi ne ya tabbatar ya kawo akwatinsa da yake kada kuri’arsa a ranar zabe.

 

Akwai wadansu da suka shaida ma wakilinmu cewa, ko a lokacin zabukan da suka gabata tun daga na shugaban kasa da sauran zabuka hakika wasu sun samu abin duniya don haka su gaba ta kaisu wai Gobarar titi. Domin ko ba samu nasarar lashe zabe ba to su abin da suka samu ruwa ta sha, ma ana Gafiya ta tsira da na bakinta.

 

Haka nan akwai wadanda suka shaida mana cewa daga cikin bangarorin da manyan ‘yayan jam’iyya suka ja daga babu mai sauraren wani balantana ayi aikin ci gaban jam’iyya akwai wani bangaren da ya ce wa dan takarar zaben cike gurbi a zaben dan majalisar karamar hukumar Sabuwa, kasancewa ba a yin harkar duniya musamman irin aiwatar da zabe sai da kudi amma lamarin ya zama abin da ake cewa ba kuka ba Guda saboda ana saran za a bayar da gudunmawar da ta kai naira miliyan akalla Goma, amma sai aka buge da samun kudin da ba su kai miliyan daya ba a daren da za a gudanar da zaben.

 

To ga kuma a halin yanzu za a yi zaben cike gurbin karamar hukumar Bakori biyo bayan rasuwa da dan majalisar ya yi a kwanan baya to, ko manyan ‘yayan PDP za su iya hada kansu ko kuma za a kara yin ‘yar gidan jiya duk girma da kasaitar manyan ‘yayan PDP da wasunsu aka yi shekaru 16 ana damawa da su a cikin gudanar da mulkin tarayyar Nijeriya sun samu dama kuma Allah ya yi masu budi sosai amma sun bar PDP ba ta iya kawo zaben dan majalisar karamar hukuma duk da haka wani bangare na ganin cewa shi bai rasa komai ba tun da dai muradunsu yana nan daram, kwalliya a ganinsu na biyan kudin sabulu, to, dabara dai ta rage ga mai shiga Rijiya, kamar yadda masu magana kance.

 

Saboda haka ne wasu ke kokarin fadakar da ‘yayan PDP cewa su Sani fa akwai wadanda ke samun riba a cikin halin rabuwar kawunan da manyan ‘yayan PDP ke ciki don haka kowa idanunsa ya bude kada a garin kallon ruwa Kwado ya yi wa ‘yayan PDP a Jihar Katsina kafa.

 

Wani daga cikin ‘yayan PDP ya bayar da misalin cewa, akwai wadansu lokuta irin na babbar Sallah a karama da kuma wani lokaci irin na Azumi da mutane ke bukatar taimako tsohon dan Takarar Gwamnan Jihar Katsina karkashin tutar PDP Sanata Yakubu Lado Dan Marke ya tallafa wa jama’a da gwargwadon abin da zai iya, domin sanarwa jama’a cewa ana tare kuma jama’a manya da kanana duk sun yi murna da farin ciki sun kuma yi masa addu’o’I na alkairi, amma ta yaya wasu za su tsaya haka nan kawai suna cikin hali na rashin jituwa da kuma kin rumgumar jam’iyya da yayanta?

 

Exit mobile version