Daga Abdulrazaq Yahuza Jere, Abuja
Likitan magungunan Musulunci, Dakta Jamil Nasir Bebeji ya shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya hada da yin magani na Musulunci domin karfafa lafiyarsa.
Ya bayyana haka ne a sa’ilin da yake godiya ga Allah bisa samun lafiyar shugaban kasan bayan doguwar jinyar da ya yi a Ingili.
Ya ce, “Muna godiya ga Allah (SWT) da ya bashi lafiya a waje kuma mu ba mu daga cikin masu cewa don me zai je waje neman magani? Domin yin hakan ba laifi ba ne. Sai dai mu a matsayinmu na likitocin Musulunci da muke da amanar al’umma; shi ma yana cikin amanarmu. Don haka muna baiwa masu kula da alhakin lafiyarsa shawarar cewa akwai bukatar su karfafa dorewar lafiyarsa da irin magungunanmu na Musulunci. Manzon Allah (SAW) ya ba da hanyoyi da dama na waraka wanda kwararrun likitocin Musulunci ne kawai suke da masaniya a kai.
Dakta Jamil Bebeji, ya kuma kwatanta irin muhimmancin da bin hanyoyin Annabawa wurin warkad da marasa lafiya yake da shi, inda ya ce, “Jalu Yunus (Aflatoun ko Pluto) wanda duk likitocin bature na duniya a karkashinsa suke saboda kwarewarsa, da ya ga irin abubuwan da Annabin zamaninsa (wasu na cewa Annabi Isah (AS) ne) yake amfani da su na magunguna sai ya ce lallai babu wani mutum mai ilimi ko kwarewa da ya isa ya yi irin abin da wani Annabi zai iya yi. Kuma ka ga Malamai sun gaji wannan din daga Annabawa.
“Ita waraka a hannun Allah take, addini bai hana mutum zuwa wurin wani walau Musulmi ne ko wanda ba Musulmi ba neman magani matukar ba za a yi shirka a ciki ba. Bisa kaunar da muke wa wannan shugaba namu ya sa muke ganin fa’idar hadawa da magungunan Musulunci domin lafiyarsa ta dore. Ba zan manta ba, a lokacin da tsohon shugaban kasa Umaru Musa ‘Yar’Aduwa bai da lafiya ina kara karatu a Saudiyya, kallonsa kawai na yi a talabijin yana bayani kafin ciwon ya tsananta amma na fahimci irin ciwon da yake damunsa kuma ina da abin da zan iya taimaka masa da shi a lokacin na magani, sai dai rashin samun damar isar da abin gare shi.
“Duk inda alkhairi yake mutum ya yi kokarin janyo shi. Ba laifi ba ne a yi wancan maganin na asibiti amma zai fi kyau a hada da namu na Musulunci. Kowane yana da karfinsa da tasirinsa kamar yadda muka gani daga magabata na kwarai. Muna sha.”
Da ya juya kan batun halin da Shugaba Buhari ya dawo ya tarad da Nijeriya a ciki, ya ce akwai ‘yan shawarwari ga shugaban kasan da zai bayar.
“Shugaban kasa a matsayinsa na babanmu kuma masani da ya yi gwagwarmaya sosai a bangarori da dama, muna da yakinin zai yi amfani da basirarsa wajen gyara cigaban al’amuran kasar a halin yanzu. Sai dai duk da haka, za mu iya bashi shawara bisa mahanga ta yadda Allah ya umurci shugabanni su rika yin shawara. Game da sha’anin kasa, muna karfafa masa gwiwa wajen daukar matakan rigakafin aukuwar wani abu, kasancewar an ce ‘rigakafi ya fi maganai’. Kamar yadda ya jajirce wajen kawar da abubuwan da ke barazana ga kasar kar ya bari gwiwarsa ta yi sanyi. Muna goyon bayansa dari bisa dari a kan umurnin da ya bayar ga shugabannin rundunonin tsaro a kan su kawar da duk wata barazana ga rayukan jama’a da dukiyoyinsu da addininsu da mutuncinsu.
“Shari’ar Musulunci ta yarda a yi maganin duk wani mai kunnen kashi ko kungiya da ke neman halakar da mutane koda ya kai ga za a kashe shi kuwa. Tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a abu ne wajibi da ya zama nauyi a wuyan shugaban kasan.
“Ta bangaren abubuwan da za su janyo amfani kuma, muna bashi shawara ya bullo da matakan da za su tabbatar da cewa kudi na yawo a hannun al’umma. Daga lokacin da mutane suka fara samun kwanciyar hankali; to babu abin da suke nema kuma illa kamar yadda za a yi su ji dadin rayuwarsu. A halin yanzu an samu tsaro illa kara karfafa shi kawai sabanin a baya kafin Shugaba Buhari ya hau mulki da kowa yake cikin tashin hankali da fargaba har ta kai mutum ba neman kudi ko gina gida ko wani abu ne a gabansa ba illa tsaron kawai. To amma yanzu da hankali ya fara kwanciya, fargabar ta ragu da kusan kashi 90 a cikin 100 ta fuskar hare-hare da satar shanu da sauransu, hankali kuma ya karkata a kan yadda za a yi kudi ya rika yawo a hannun jama’a. Shugaba Buhari da Majalisarsa su kara bada himma sosai kan bullo da hanyoyin bunkasa tattalin arziki wadda galibin jama’a za su shaida”.