Connect with us

TATTAUNAWA

Ya Kamata Wammako Ya Mayar Da Zanen Goyo Ga Sakkwatawa – Abdul’aziz Sagera

Published

on

Tun daga lokacin da batun tsayar da ‘yan takarar gwamna ya kunno kai a jihar Sakkwato, a jam’iyyar APC, matsaloli da yawa sun kunno kai, musamman ma yadda wasu jiga-jigan jam’iyyar da kuma wasu ‘yan takarar gwamnan suka fito suka nuna rashin gamsuwarsu da yadda dan majalisar tarayya kuma tsohon gwamnan jihar Sakkwato  Alhaji Aliyu Magatakarda Wammako yake neman ya kakaba wa magoya bayan jam’iyyar APC da kuma aje ‘yan takarar gwamna a jihar Sakkwato gefe guda ya yi.

Gaban kansa wajen tsayar da dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Sakkwato a zaben shekara ta 2019. Wakilnmu, BALARABE ABDULLAHI ya sami damar tattaunawa da wani fitaccen siyasa dan jihar Sakkwato da ke zaune a Zariya mai suna ALHAJI ABDUL’AZIZ  SAGERA – DIKKO,karamar hukumar Gada, inda ya warware wa wakilinmu zare da kuma abawar matsalolin da APC ke ciki da ya ce, tsohon gwamna Wamako ya dace ya lura da su, domin fadawa rami mai gaba dubu a zaben shekara ta 2019.

Ga dai yadda tattataunawarsu da wakilinmu ya kasance ta kasance,

Me za ka ce kan maganar fitar da dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a jihar Sakkwato?

Babu ko shakka a matsayin tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Alhaji Aliyu Magaji Wamako, shi ya dace ya tashi tsaye, ya dauki matakan ganin ba a sami matsala ko kuma matsaloli a cikin jam’iyyar APC a jihar Sakkwato, sai kuma aka wayi gari, matsalar ta faru ta wajensa, wanda duk mai kishin jihar Sakkwato mai kuma kishin jam’iyyar APC, ya na girmama Wamako, sai aka sami akasin abin da ba yi zato ba, wato ya yi gabankansa wajen fitar da dan takarar gwamna ba tare da bin tsarin da jam’iyya ta tsara ba.

Duk wanda ya san Wammako, kyawawan halayensa a lokacin da yake mataimakin gwamna, shi ya zama silar shigarsa takara gwamna ya ci,bayan ya yi mataimakin gwamna na shekara takwas, aka zabe shi gwamna ya yi shekara takwas, a yau kuma ya na dan majalisar tarayya zai yi shekara hudu, kin Allah ya yadda. Ka ga a nan ya dace Wammako ya gane Sakkwatawa sun yi ma sa asin-da-asin na siyasa, kuma sun yi ma sa bikin da ya kamata shi kuma ya yi wa Sakkwatawa zanen goyo.

Kuma a shekara ta 2015, Sakkwatawa na da wadanda suke so su zama gwamna, sai ture bukatar al’ummar jihar Sakkwato, ya tursasa wa al’umma, dan takarar gwamna, suka bi abin da yake so, amma sai aka wayi gari ya bar jam’iyyar ya koma wata jam’iyya, wanda duk dan jihar Sakkwato na kuka a kan wannan matsala,kuma shi Sakkwatawa suke tsoron kar tarihi ya maimaita kansa, Wammako ya sake tsayar da dan takarar gwamnan da zai koma wata jam’iyya a nan gaba, bayan zaben shekara ta 2019.

Ko ya lura babu dan takara nagari ne da zai karbu a daukacin jihar Sakkwato, ya tsayar da wanda kuke kuka a kansa?

Ai bahaka ba ne, a yanzu muna da mutane nagari, masu kishin jihar Sakkwato da kuma tunanin jihar Sakkwato a zukatansu, har ma sun sayi takardar takarar gwamnan a zaben shekara ta 2019, amma bai dubi daya daga cikinsu ba, wanda kuma wanda ya tsayar, inan kasa mutanen jihar Sakkwato goma, ba shi da mutum biyu da suke tare da shi, ka ga za a iya samun matsala ke nan a jam’iyyar APC a zaben shekara ta 2019. Cikin wadanda al’ummar jihar Sakkwato ke muradin daya daga cikinsu ya zama gwamna a shekara ta 2019, akwai Alhaji Ahmed Aliyu da Alhaji Bello Jibrin Gada da kuma Alhaji Faruk Malami, duk sun cika fom,ya dace ya dubi wannan matsala kafin dare ya yi.

Ka na ganin a yau tun da gwamnanku ya koma wata jam’iyya , a matsayinsa na dan majalisar tarayya, bai dace ya yankehukumcin wanda ya dace ya zama dan takarar gwamna ba a jam’iyyar APC ?

Babu shakka, wannan mataki da Wamako ya dauka, zai iya yi wadimkuradiyyar da ake ciki karar tsaye, a wannan halin da mu ke ciki, na mun zabi wanda ba shi ne mu ke so ba a shekara ta 2015, bayan zabe ya bar mu, ya koma wata jam’iyya. Abin da ya kamata mai girma Wamako ya yi a matsayinsa uba a siyasar jihar Sakkwato, ya bar al’ummar jihar Sakkwato su zabi wanda suke a matsayin dan takarar gwamna a zaben shekara ta 2019, shi kuma in an kammala batun fitar da dan takara, sai ya sa albarka ga wanda aka zaba.

Ina son in bayyana ma ka, har gobe in Allah ya kai mu, Alhaji Wammako shi ne jagorar jam’iyyar APC a jihar Sakkwato kuma kamar yadda na ce ma ka a baya, uba ga duk wani dan siyasar jihar Sakkwato, sai dai wannan matsala ta tsayar da dan takarar gwamna a APC, za ta iya kawo wushisshire  gyara zama a siyasar jihar Sakkwato, wato kila na gaba ya koma baya. Yanzu lokacin Karen tsaye ga siyasa ya wuce, domin kan al’umma ya kammala bude wa a siyasa, kuma hakan zai tabbata da zarar an zo zaben shekara ta 2019.

Ko domin ba a fitar da gwaninka ba ne, shi ya sa kake cewar dan takarar da Wammako ya ce ku Sakkwatawa da kuke APC  ku zabe shi a shekara ta 2019 ?

Ba sai na rantse ba, ba ni da wani gwani a cikin mutum hudun da suke takara, gwanin na shi ne wanda al’ummar jihar Sakkwato suke so, Ka fahimta, Alhaji Wammako ubanmu ne a siyarasr jihar Sakkwato, duk abubuwan da na bayyana, na bayyana su ne domin gyaran jam’iyyar APC da kuma ganin jam’iyyar APC  ta ci zaben shekara ta 2019, ba a fadi zabe ba.

A karshe, wane  tunani kake yi wa jam’iyyar APC a jiharSakkwato a zaben shekara ta 2019 musamman a wannan rikicin fitar da dan takarar gwamna da jam’iyyarku ta shiga?

Ai wannan matsala za a iya kawo karshensa kafin zaben shekara ta 2019, in Allah ya yadda, domin na san Wamako dan siasa ne da ke sauraron shawarwari, tun a farko ko kuma a kurewar lokaci.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: