A yau aka kama wani mutum mai shekaru 28, Chukwuemeka Obijofa da ake zargi da kashe matarsa da danta mai shekaru hudu a kauyen Ofufe Nza da ke karamar Hukumar Ekwusigo a Jihar Anambra. An rahoto cewa wanda ake zargin ya aukawa matar, Chisom da dansa, Amanda a kawunansu da shebur.
Jaridar Nation ta tattaro wanda ake zargin ya kuma raunata wani dan banga da ya yi kokarin ceton wadanda abin ya shafa da wannan abin. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda, Haruna Mohammed ya ce an cafke wanda ake zargin yayin da aka ajiye gawarwakin a dakin ijiye gawarwaki na asibitin bayan likita ya tabbatar da cewa sun mutu.
Ya ce: “A ranar 27/1/2021 da misalin karfe 7:45 na yamma,‘ yan sanda da ke aiki a ofishin ‘yan sanda na Ozubulu, sun cafke wani Chukwuemeka Obijofa, mai shekara 28, na kauyen Ofufe Nza da ke karamar Hukumar Ekwusigo ta Jihar Anambra. “Wanda ake zargin ya gudu a cikin wani yanayi amma an gano shi bayan da ya auka wa matar sa, Chisom Chukwuemeka,‘ yar shekaru 26, da kuma danta mai suna Amanda Chukwuemeka, dan shekaru 4, dukkansu an samu shedar guda, tare da su ta duka da shebur a kawunansu.
“Wanda ake zargin ya yi amfani da abu guda kuma ya raunata wani dan banga wanda ya yi kokarin ceton wadanda abin ya shafa.
“Jami’an ‘yan sanda sun ziyarci inda lamarin ya faru inda suka garzaya da wadanda lamarin ya rutsa da su zuwa asibitin hadin gwiwa, Ozubulu, domin kula da lafiyarsu inda likitocin suka tabbatar da cewa maman ta ‘ya’ya da danta mutu.
“Yan banga da suka samu rauni suna asibiti suna karbar magani, yayin da aka ijiye gawarwakinsu a dakin ijiye gawarwaki na asibiti don gudanar da bincike.”
Mohammed ya kara da cewa, kwamishinan ‘yan sanda, John Abang ya umarci DPO da ya tura lamarin zuwa ofishin CID na jihar a Awka, domin gudanar da bincike cikin tsanaki don gano hakikanin abin da ya faru.