Me Ya Kawo Lalacewar Harkar Ilimi A Arewacin Kasar Nan?

Tare da

Musa Muhammad08148507210   mahawayi2013@gmail.com

Akwai Karin maganar Hausawa da ke cewa ‘kowa ya tuna bara, bai ji dadin bana ba.’ Na kawo wannan karin magana ne saboda batun da nake son in yi, wanda ya shafi harkar ilimi a kasar nan, musamman a nan Arewaci.

A kwanakin baya na kawo bayanin yadda Gwamnatin jihar Kaduna ta dauki damarar ganin ta dawo wa da harkar ilimi martabar da ta kamata a ce tana da ita, duk da yake wannan yunkuri na fukantar wasu matsaloli masu nasaba da siyasa, wanda ya da nuhimmanci duk bangarorin biyu su bi wadannan matsalolin.

Amma dai ko ma mene ne, lallai akwai bukatuwar yanzu a yi wa wannan harkar gyaran da ya kamata, musamman idan aka yi la’akari da irin gibin da ke tsakanin Kudanci da Arewacin kasar nan ta wannan harka mai muhimmanci ta ilimi.

Yana da muhimmanci mu dubi yadda harkar nan ta ke a shekarun baya, sannan mu kwatanta da yadda abin yake a halin yanzu, shin ina matsalar ta ke, a wajen al’umma ne ko kuwa daga shugabanni ne?

Wannan al’amari haka yake, musamman idan aka yi la’akari da yadda wasu bangarorin ilmi suka durkushe, wanda hakan ya sa aka shiga wannan halin da ake ciki da dadewa. Shi ya sa ake ta samun koma-baya, musamman ma a makarantun Firame, wadanda ake ganin su ne manyan ginshikan ilmi, musamman na yara tun suna kanana, saboda abubuwa sun fi saurin shiga kwakalwarsu.

Idan aka yi rashin sa’a wannan lalacewa ta faro daga Firamare, to lallai an yi baya ba zane, domin komai daga Firamare ake fara shi, wanda da zarar an samu matsala daga can, to shi ke nan fa tafiya ta tafi, sai dai a yi a hankali.

Idan har aka fara samun matsala daga can, to ai kuma shi ke nan, sai dai a ce Allah ya kiyaye. Wannan ne ya sa a wancan rubutu da na yi a makwani biyu da suka gabata na yabi wannan yunkuri na gwamnatin jihar Kaduna, duk da dai akwai wasu matsalo da suka dabaibaye batun, amma lallai kam akwai bukatar a zo a sake duba batun, dukkan bangarorin da abin ya shafa, su zauna a duna yadda za a kawo wa harkar gyara.

Idan kuma aka waiwaya baya, yadda al’amuran suke shekarun baya, lokacin da akwai Makarantun koyon sana’o’I, wadanda aka fi sani da Technical schools, sai kuma Commercial Colleges na harkar kasuwanci, sai kuma babbar cikinsu, Kwalejojin horar da Malamai, wato Teachers Colleges.

Shi ya sa na ke cewa abubuwa da yawa ne suka haddasa tabarbarewar harkar ilimi a Arewacin kasar, wanda daya daga cikinsu shi ne soke Kwalejojin horar da Malamai da ake da su, haka kuma da rage manyan Kwalejojin, wadanda a lokacin da suke aiki, ba karamin ci gaba su ke bayarwa a wannan harka ba.

Za a iya yarda da ni idan mutum ya tuna yadda kusan duk wani babba a kasar nan, makarantun gwamnati ya yi, kuma ya samu ilimi mai inganci. Ba wani abu ya jawo haka ba, illa yadda su shugabannin na wancan lokacin suka ba harkar ilimin muhimmanci. Wanda kuma a yanzu an rasa wannan a shugabannin yanzu, domin yanzu za mu iya cewa babu wani daga cikin ’ya’yansu da ya yi, ko yake yin makarantar gwamnati, musamman a Firamare da Sakandare.

A tsarin da ake gudanarwa a wadancan Kwalejoji da nake magana a kai, wanda kuma alhamdu lillahi, ya kasance ni ma irinta na yi, wato ‘Zaria Teachers College,’ akwai dabaru da horo na musamman da ake koya wa mai shirin zama Malami, wanda har idan mutum ya shiga aji, to lallai zai kasance dalibi ya fahimci abin da ake koya masa. Wanda cikin wannan ma akwai gwajin koyarwa sau biyu aka tura dalibai kafin su kamala Kwalejin.

Haka kuma akwai matakai da ake bi a tsarin baya da na sani, ban san na yanzu ba, domin abubuwa na ta canjawa, wanda kuma hakan, kamar yadda na ce yana daga abubuwan da suke kawo wa harkar koma-baya. Inda da farko idan dalibi yana aji biyu yana kusa ya shiga aji na uku, akwai wata jarabawa da ake yi, mai suna aptitude test, daga wannan jarabawar ce ake ware daliban da aka ga za su fi dacewa a ce sun tafi makarantun horon Malamai, wasu a kai su Tehnical Schools, wasu kuma Commercial Colleges, wasu kuma sai Science Schools.

Bambancin da ke akwai shi ne, akwai wasu tun lokacin da ake masu interbiew bayan Common Entrance Edamination, shugabannin interbiew ke yanke shawarar su kai su Makarantun horon Malamai, ko ta maza ko mata. sai kuma Makarantun Koyon Sana’a, da kuma wasu Makarantun koyon kasuwanci. Akwai Government Commercial College.

Shi ya nake kara nanata cewa soke wadannan Kwalejoji ya bayar da gagarumar gudumawa wajen durkusar da harkar ilimi a kasar nan, musamman a nan Arewa, domin ire iren wadannan makarantu da ake ce masu na musamman, sun taka muhimmiyar rawa wajen samar wa kasa da kwararru, musamman a harkar koyarwa, domin tun suna ‘yan yara ake koya masu, ilmin ya shiga cikin jikinsu sun kuma saba, domin abin da za ka yi shekaru biyar, ana koya maka.

A taya ni dubawa ko akwai wasu daga cikin wadannan Kwalejoji da ake da su a da, ko akwai masu motsi a yanzu? Irin su Katsina Teaahers College, wacce wannan makaranta ta bada gagarumar gudunmawa wajen samar da Malamai, musamman a nan Arewacin kasar nan, muna iya daukar shugabannin siyasar farko na Nijeriya, wadanda can suka yi karatu, kamar su Marigayi Sir Ahmadu Bello Sardauna Sakkwato, Sir Abubakar Tafawa Balewa, Malam Aminu Kano, Alhaji Umaru Sanda Ndayako Etsu Nupe, Alhaji Isa Kaita, Sir Kashim Ibrahim, da dai sauran mashuran mutanen da suka taba taka rawa wajen ciyar da kasar nan gaba.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa in Allah ya yarda a wannan batu namu mai muhimmanci na muhimmancin harkar ilimi ga al’umma.

 

Exit mobile version