Wani dan fansho da ke zaune a jihar Kaduna, mai suna Musa Aga, ya girgiza makwabtansa a yankin Gonin-Gora na shahararren makarantar firamare ta LEA da ke Kaduna, ta hanyar kona rukunin gidansa mai dakuna biyu don hana matarsa da suka rabu sama da shekaru 20, dawowa zama dashi.
‘Ya’yansa wadanda suka nace kan mahaifiyarsu ta dawo ta zauna tare da mahaifin nasu, duk da nacewar Musa kan akasin hakan, da karfi suka kutsa cikin gidan ta cikin rufin don shigar da kayan mahaifiyar tasu.
Musa, ya yi ritaya daga ma’aikatar ci gaban al’umma ta Jihar Kaduna a shekarar 2015, kuma dan asalin garin Kagoro ne da ke Kudancin Jihar Kaduna.
Da yake bayyana dalilin da ya sa ya kona gidansa, Musa ya ce, “Na rabu da matata kimanin shekara 20 yanzu. Amma yanzu yaran suna tilasta min in zauna tare da mahaifiyarsu. Amma na ce a’a saboda lokacin da dattawa da fastocin cocinmu suka roke ta da ta dawo wurina a baya ta ce a’a.
Da aka tambaye shi ko ya gina gidan ne daga kudin shi na barin aiki, sai ya ce, “Ee, daga kudin ne. Amma saboda bacin rai da iyalina, na yanke shawarar kona shi.
Lokacin da aka tambaye shi idan yaran ba za su ji haushin abin da ya aikata ba, sai ya ce, “Ee, ina son su ji haushe ne yasa na yi hakan. Suna so su tilasta ni in zauna tare da mahaifiyarsu amma ba na so. Sun ce gidan ubansu ne, amma yanzu gidan mahaifinsu baya nan. Kun ga dalilin da yasa na kona gidan?
A lokacin da Musa yake cewa irin wadannan abubuwan ba su cika faruwa ba ga mutane masu irin shekarunsa, wadanda a kullum burinsu shine su bar wa ‘ya’yansu gado a lokacin ba ba su nan, ya ce, “Ee amma idan ‘ya’yan su da kirki bai kamata a bar masu komai ba, sai dai idan suna da kirki kuma suna sauraron ka.”
“Idan suna da kirki za su iya tilasta mahaifinsu ya kasance tare da mahaifiyarsu ko? Na tarbiyantar da su akan su kula da ni lokacin da na tsufa, amma yanzu suna wulakanta ni.
Kokarin da makwabta suka yi na kashe gobarar ya ci tura sakamakon wutar da ke kamawa da iska mai karfin gaske.
Iskar ta kara tsoratar da makwabta na kusa cewa gidajensu na iya shafar wutar, saboda haka suka bada karfi wajen hana wutar yaduwa.
Yayin da wasu ke gwagwarmaya don shawo kan gobarar, masu ba da agajin gaggawa na kauyukan yankin sun himmatu wajen tara zinc na konawa, karfe da tarkacen bakin karfe, kamar yadda wasu ke kallo, wasu suna sharhi, wasu kuma suna bakin ciki.
An kuma samu labarin cewa, an zargi daya daga cikin ‘yan matan da ta dage cewa dole ne uba ya karbi sadakinta duk da cewa bai yarda da sadakin sauran ‘yan matan ba, saboda haka dole ne mahaifiyarsu ta koma gidan mahaifinsu ta kuma karbi sadakin nata.
Wasu majiyoyi sun fadawa manama labarai cewa, wata mata ‘Yar shekara 40 ta ji ana cewa tsohuwar matar tana son dawo ne tun lokacin da ta ji cewa Musa yana kokarin gina gidan kansa, domin ita tana zaune ne a gidan haya tsawon shekaru.