Wani ango ya mari matar sa a gaban bakin da ke wajen bikin aurensu.
A cikin faifan bidiyon da abin ya faru wanda aka yi amannar cewa hakan ya faru ne a yankin Asiya ta Tsakiya, a inda aka ga angon a fusace yana caccakar amaryarsa bayan ta yi masa zolaya ta hanyar janye masa kek daga baki. Ya buge matar da ba a ambata sunan ta da karfi har sai da ta yi tuntube zuwa wurin zama a bayanta.
Wani mutum da ke tsaye a bayansa ya kama shi yayin da dayan bakin da ya firgita ya ta’azantar da amaryar yayin da take kokarin dawowa kan kafafunta.
Hotunan sun fara ne da nuna wata mata da kayan amare kafin angon ya ba ta wani kek a baki. Amma da ta dawo za ta sanya masa shi ma a bakinsa, sai ta yi masa wasa tana zolayarsa kamar tana janye kek din daga bakinsa, kafin dakika na uku ya nuna fushinsa ya mari amarya a fuska har sai da ta matsa baya. An nuna ta tana rike da fuskarta bayan ya mare ta yayin da baki suka gigice.