Tare da Jummai Ibrahim
GSM: 08097160554 (tes kawai)
saasanaa@yahoo.com
Muna kara gode wa Allah da ya nuna mana babbar rana, wato Jumma’a. Da fatan an sauko Sallah lafiya. Tare da hakan nake mika godiya a gare ku masu karatun wannan shafi ‘Na ‘Sana’a Sa’a’ a tsawon lokaci. Idan ba a manta ba mun faro shafin da wannan sunan sabili da koyawa ‘yan’uwana mata sana’o’in hannu. A lokacin mun gabatar da darussa daban-daban kan yadda mata za su alkinta wa kansu sana’o’i don su raya kansu da iyalansu. Na san ba a manta da darussa kan yadda ake hada sabulan wanka da wanki, sinadaran kashe kwari, har da kayan shayi da sauransu ba. Amma a lokacin da muka dora darasin hada turare, har ya kai mu ga turaren jiki, wato ‘Humra,’ inda a nan ne salon shafin ya sauya.
A yanzu kuma mun wayi gari babban editanmu ya ga dacewar sauya sunan shafin zuwa ‘Taskira.’ Na san uwargida ta san ma’anar wannan kalma. Ke nan za mu dawo da hankalinmu kacokan zuwa da ‘Asirin Dakin’ uwargida.
Wannan sakon ya fito ne daga Malam Abubakar Ibn Sarky memba a Majalisar Burin Zuciya reshen Jihar Adamawa:
Zuwa ga edita, ina mika gaisuwata gare ka da Iyalanka da sauran abokan aikinka da dukkanin masu karatun wannan jarida mai farin ji a ko’ina a fadin duniyar nan. Ina yi wa kowa fatan alheri.
Mai girma edita na dade da wani abun cewa a zuciya ta game da wani shafi da ke da farin jini a cikin wannar jarida mai albarka, shafin da ake cewa ‘Sana’a Sa’a’ wanda wata Malama Jummai Ibrahim ta ke jagoranta.
Lallai wannan shafi yana tabo abubuwa da dama da suka shafi mata wani lokaci ma har da mazan, to amma a wannan rubutun, zan yi tsokaci ne akan abun da ya shafi iyayenmu matan, da fatan Allah (SWT) ya haska kirjina na fadi abin da zai amfane mu amin.
Hakika wannan shafin sau da yawa ya kan bawa mata shawarwari a game da yadda za su tsaftace zamantakewarsu a cikin gidajen mazajensu wanda hakan yana tasiri sosai a wurinsu, za ka iya gano hakanne kuma, ta yadda za ka ga irin tambayoyin da suke aikowa a shafin, ake kuma ba su amsoshi daban daban. To amma a inda gizo ke sakan shi ne mafiyawan lokuta za ka ji suna aiko da tambaya a kan cewa ya za su yi su karawa kansu Ni’ima? Kuma hakika shafin, musamman marubuciyar tana iya kokarinta wajen ba su shawarwari masu nagarta ta yadda za su samu biyan bukata, sai dai me? Ba nan gizo ke sakar ba, don kuwa ba za ka yawaita ji ko ganin suna tambaya a kan me ke kawar musu da Ni’imar ba? Ballantana shafin ya yi kokarin samar musu da rigakafin kamuwa da matsalar rashin Ni’ima a kinsu.
Shakka babu akwai bukatar Iyayenmu mata susan me ke kawar da Ni’imar jikinsu, kuma ina son mata su sani cewa akwai wasu matan da Ni’imar jikinsu take zubewa tun suna yara kanana, kuma da yawa daga cikin irin wadannan matan har karshen rayuwarsu Ni’imar jikinsu ba za ta taba dawowa ba. An kiyasta kashi 90 daga cikin 100 na wadannan matsaloli ana samunsune daga rashin sani da kuma sakaci na Iyaye mata. Musani cewa masana suna cewa gaban mace (al’aurarta) yana saurin cafkar kwayoyin cuta ne kamar yadda mayen karfe yake cafkar karfe da zarar karfen ya kusance shi, kuma da zarar cututtuka sun yi yawa a al’aurar to ni’imar jikinta ya rika wargajewa kenan.
Iyayena mata kusa ido ku ga wasu daga cikin abubuwan da ke haifar da wargajewar Ni’imomi a gareku, na farko shi ne hanyar da kuke bi wajen tsaftace yaranku, misali yarinya ta yi bayan gida, ta gama, ida za a wanke mata, to maimakon a sata ta tsuguna sosai, kawai sai dai a yi mata tsarkin ta ko wane hali take. Wanda in ana wanke mata a hakan, an manta cewa ruwan daudar wannan kazantar yana tafiya kai tsaye zuwa cikin jikinta, musamman ma idan ta yi goho, zai iya komawa cikin al’aurarta, shi kuma bayan gari shi akarinkansa cuta ne, mai tattare da wasu kwayoyin cutar da ke dauke da shi, don haka kun ga tun daga nan, an fara gurbata irin ni’imar da irin wadannan yara za su ta su da ita.
Haka zalika barin gashi ya yi yawa a matsematsin ma’aurata wato, su rika safar junansu da shi a lokacin saduwa, shi ma yana haifar da matsala ga ma’aurata kuma yana kauda sha’awa. Malamai suka ce, wannan ne ma dalilin da ya sa aka ce namiji duk bayan kwana 40 ya aske gashin gabansa, ita kuma mace duk bayan kwana 20 ta aske nata.
Iyayenmu mata in so samu ne ana son mace ta zamo ko a bayan daki ta bambanta wajen da take tsuguno ta yi fitsari da inda take wanka, haka nan an so mace duk lokacin da za ta yi tsarki ta samu ruwa mai tsafta sosai, in so samu ne ta yawaita yin tsarki da ruwan dumi, yin hakan yana taimakawa sosai wajen gujewa kamuwa da cututtuka da dama da kuma magance wasu cututtukan. Iyayen ma mata ku daina shafa duk wani mai a gabanku, duk sana gurbata Ni’imar ‘ya mace. Maimakon hakan ku samu man Zaitun ku rika shafawa a duk lokacin da kuka yi wanka ko kama ruwa musamman da ruwan zafi. A guji barin jikakken kaya a jikinku masamman wandunan ciki (Pants ko Underwear) hakan shi ma yana haifar da wargajewar Ni’imar da ke jikin ‘ya mace. Sannan ku tabbatar kun goge jikinku sosai bayan kun fito daga wanka ko kama ruwa kafun ku maida kaya jikinku, kiyaye yin hakan zai taimaka gaya yajen gujewa kamuwa da cututtuka a gare ku.
Daga karshe ina mai baku shawara da cewa ku yawaita shan ‘ya’yan itatuwa domin karin Ni’ima gare ku, maimakom shan wasu kwayoyi da ba ku san asalinsu ba.