Wata yarinya ‘yar shekara 26 daga garin Ningbo, lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin, ta biya farashi mai yawa kan abincin da ta umarta a kawo masu ita da saurayinta wanda farashinsa ya kai Dala 3,064, bayan saurayin tsare daga wajen cin abincin.
A cewar saurayin wanda ake wa lakabi da Lin, wani mutum ne da ya yi ikirarin cewa, shi attajiri ne wanda kuma a zahiri yake aiki a wani wurin sayar da motoci, ya ce wai ya tafi ne saboda ya ji kamar za ta yaudare shi.
Lin ya hadu da budurwar ne mai suna Yang, kafar sadarwa. Sun amince da sanya ranar haduwa a wani gidan cin abinci mai tsada da ke yankin wanda Yang ya zaba. Sannan ta yi odar abincin Dala 3,064 a cikin kwano da kuma kwalban barasa na kusan dubu 12. Anan take Lin ya ce yana jin jikinsa ba dadi kuma yana son zuwa bandaki.
Ba zato ba tsammani, yang ta jira fiye da awa guda amma saurayin bai dawo ba. Cikin damuwa, ya karbi takardar kudin ta biya kudin abincin da kanta.