An gurfanar da wani mutum mai suna Festus Stephen a gaban kotu bisa zargin daba wa abokinsa Abbas Mohammed Gudus wuKa har lahira bayan takaddama kan wayar ‘iphone’.
Stephen mai shekaru 27, ma’aikaci ne a ma’aikatar lafiya ta jihar Adamawa, hade da hukumar kula da lafiya a Mubi, an gurfanar da shi a gaban Mai Shari’a Helen Hammajoda da ke babbar Kotun na 2 da ke Yola, saboda kashe Abbas.
Yana fuskantar tuhuma guda biyu, wadanda suka shafi cin hanci da rashawa, sabanin haka kuma za a hukunta shi a karkashin sashi na 1 (2) (b) na fashi da makami (Special Probidence) Dokar R11 ta dokokin tarayya, 2004.
A bayanin da ya yi na furci, Stephen ya ce, ya fara haduwa da Abbas ne a shekarar 2011, kuma tun daga wannan lokacin, suka zama abokai.
Wanda ake zargin ya kara da cewa, ya sayi iphone din wanda aka kashe a kan kudi Naira 40,000, kuma ya biya kudin gaba daya hannu-da-hannu, amma mamacin ya ki ba shi.
A cewarsa, ‘yan mintoci kadan bayan shan syrop dinsu na maye, marigayin ya fito da waya daga aljihunsa don yin kira. Yayin da yake kiran, wanda ake zargin ya fito da wuka ya daba masa a wuya.
Stephen ya ce, ya dauki wayar, ya tsoma hannayensa a aljihun mamacin ya dauki fakitin sigari, ya hau babur mai kafa uku ya fece ya gudu daga wurin, inda ya bar Abbas cikin jini.
An kai rahoton lamarin ga hukumar tsaro da abin ya shafa kuma daga karshe binciken ya kai ga cafke wanda ake zargi da kisan. An daga karar zuwa 24 ga Fabrairu 2021.