Rabiu Ali Indabawa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home JAKAR MAGORI

Ya Watsa Wa Matarsa Asid Bisa Kin Abokansa Su Yi Ma Ta Fyade

by Rabiu Ali Indabawa
January 5, 2021
in JAKAR MAGORI
2 min read
Fyade
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wani dan caca a Indiya da ya saka matarsa a caca kuma ya rasa, ya watsa wa matar ruwan batir saboda ta bijire wa yunkurinsa na mika ta ga abokansa, wadanda suka yi mata fyade a wani bangare na yarjejeniyar, kamar yadda wani rahoto na ‘Independent News’ ya ruwaito.

Lamarin ya faru ne a jihar Bihar da ke arewa maso gabashin kasar, kuma hakan ya kara yawan lamura na tashin hankalin cikin gida yayin takurawar cutar korona a Indiya.
A cewar Rajesh Kumar Jha, wani babban jami’in ‘yan sanda na ofishin ‘yan sanda na Muzahidpur, “Ma’auratan sun yi aure kimanin shekaru 10 da suka gabata. Mijinta ya kasance cikin caca kuma ya rasa ta a cikin cacar a karshen Oktoba. Bayan haka ne ya aika ta zuwa ga masu caca ba da son ranta ba, inda maza za su yi mata fyade. Idan har ta bijirewa yin lalatar da ita, mijinta zai buge ta ya kuma yi garkuwa da ita. A ranar 2 ga Nuwamba, lokacin da matar mai shekara 30 ta bijirewa yunkurin mijinta na sake tura ta ga ’yan cacar ne ya watsa mata ruwan batir.”
“’Yan sandan jihar sun kama mijin a karkashin sassa daban-daban na dokokin Indiya, wadanda suka hada da watsa ruwan batir, fyade a cikin kungiya, cin zarafi, da tsarewa mutum ba a kan son kan sa ba ba, kuma a yanzu haka yana hannun hukuma, ”in ji jami’in.
Ba za a iya ambata sunan ma’auratan ba saboda dokokin da ke kare wadanda laifukan lalata ya shafa. Har yanzu ‘yan sanda ba su gano sauran mutanen da ake zargi ba. Kullen korona ya haifar da ninki biyu na rikice-rikicen da ya shafi jinsi, a cewar Hukumar Kula da Mata ta kasa (NCW), wacce ke karbar korafe-korafen tashin hankalin cikin gida daga ko ina cikin fadin kasar Indiya.
Kwamitin matan ta samu korafi 587 na cin zarafin mata tsakanin 23 ga Maris da 16 ga Afrilu, wanda ya karu da kashi 45 daga na 25 na baya tsakanin 27 ga Fabrairu da 22 Maris. An danganta wannan ga damuwar rashin kudi na kullen korona, da rashin samun isassun barasa.

samndaads
SendShareTweetShare
Previous Post

Yadda ’Yar Shekara 60 Ta Kada ’Yan Mata A Gasar Sarauniyar Kyau

Next Post

Takwaran Hitler Ya Lashe Zabe A Kasar Namibiya

RelatedPosts

Na'urar ATM

Yadda Ya Makale A Dakin Na’urar ‘ATM’

by Rabiu Ali Indabawa
14 hours ago
0

A ranar Laraba da yamma ne wani dan kwangila a...

Masarauta

An Yanke Mata Shekara 43 A Gidan Yari Saboda Bata Sunan Masarauta

by Rabiu Ali Indabawa
14 hours ago
0

An yanke wa wata tsohuwar ma'aikaciyar gwamnati hukuncin daurin shekara...

Mabaraciya

Hoto Daya Ya Sanya Mabaraciya Zamo Wa Mashahuriya

by Rabiu Ali Indabawa
14 hours ago
0

Shekaru hudu da suka gabata, Rita Gabiola wata yarinya ce...

Next Post
Takwaran Hitler Ya Lashe Zabe A Kasar Namibiya

Takwaran Hitler Ya Lashe Zabe A Kasar Namibiya

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version