Dakta Jamilu Yusuf Zarewa" />

Ya Ya Kamata Na Yi Da Ribar Banki Da Na Amsa? 

Tambaya:

Assalamu alaikum malam Menene ra’ayin malaman Sunna akan kudin da banki suke karawa mutane a cikin Saving account? Ya yakamata ayi amfani dasu? Allah ya karemu daga aikata kuskure.

Amsa:

Wa’alaikum assalam Farko dai ya haramta ga musulmi ya bude account din da za’a dinga saka masa kudin ruwa a ciki, saboda Allah ya haramta cin riba ya kuma yi shirin yaki da Wanda bai daina ci ba à cikin aya ta 275 a Suratul Bakara da ayoyin da suka zo bayanta.

Annabi S.A.W ya la’anci mai cin riba da wanda ya rubutata da wanda aka wakilta da wanda ya yi shaida akanta. Kamar yadda Tirmizi ya rawaito a hadisi ingantacce.

Idan mutum ya amshi Interest din Banki to ya wajaba ya tuba ga Allah da niyyar ba zai sake amsa ba, tun da Allah ya Hana.

A zance mafi inganci zai iya amfani da kudin wajan yin aikin da zai amfani jama’a kamar gina Asibitoci ko kwatar da ruwa zai wuce ko kuma hanyoyin da mutane za su bi su wala, saidai ba shi da ladan wannan aikin da ya yi, saboda ba dukiyarsa ba ce.

Wannan ita ce maganar manyan malaman musulunci na wannan zamanin kamar Sheik Ibnu Bazz da sauransu.

Allah ne mafi sani.

Ina So Na San Siffofin Jinin Haila

Tambaya:

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakaatuhu. Don tambaya gare ni Kan wani ruwa ke fitomin amma kuma ba jini bane .INA ganinsa kasa kasa .babu wari ko karni tare dashi .INA ganinsa idan nayi Azumi ko nayi aiki sosai .se marata tayi ciwo .shine yake fitomin. Yaya Azumi na da sallah ta take shin zan cigaba da yansu ? .sannan yana fitomin wajan karfe 3 na rana ne .

 

Amsa:

Wa alaikum assalam, mutukar ba jini ba ne, kuma ba baki ba ne, ba shi da karni, to ba zai hana sallah da azumi ba, zai yi kyau ki je wajan likita don ya  duba lafiyarki, saboda abin da kika gani zai zama ba jinin haila ba ne, tun da ya rasa daya daga cikin siffofinsa.

Allah ne mafi sani.

Na Sha Nonon Matata, Yaya Auranmu?

Tambaya:

Don Allah malam ya matsayin mutumin da ya sha nonon matarsa,  ya aurensu  yake ?

Amsa:

To dan’uwa Allah madaukakin sarki ya halatta maka jin dadi da dukkkan bangarorin jikin matarka, in ban da dubura ko kuma saduwa da ita lokacin da take haila,  don haka  ya halatta ka tsotsi nononta mutukar babu ruwa a ciki, amma idan akwai ruwa a ciki, to malamai sun yi sabani akan halaccin hakan zuwa  maganganu guda biyu :

  1. Ya halatta, saboda kasancewar nonon da yake haramta aure shi ne wanda aka sha kafin yaro ya cika shakaru biyu, saboda fadin Annabi s.a.w. “Shayarwar da take haramtawa, ita ce wacce yaro ya sha saboda yunwa” , Bukhari lamba ta : 5102, ma’ana lokacin da ba zai iya wadatuwa ba daga nono, saboda shi ne abincinsa, shi kuma wannan ya faru ne bayan mutum ya girma don haka ba zai yi tasiri ba wajan haramta aure,  wannan ita ce maganar mafi yawan malamai .
  2. Bai halatta ya sha ba, saboda ko da yaushe mutum ya sha nonon mace to ta haramta a gare shi, domin Annabi s.aw. ya umarci matar Abu-huzaifa da ta shayar da Salim, don ta haramta a gare shi, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 2636, tare da cewa a lokacin Salim ya riga ya girma,  wannan sai yake nuna cewa idan babba ya sha nono to zai yi tasiri wajan haramcin aure .

Zancen da ya fi karfi shi ne ya halatta miji ya sha nonon matarsa, saidai rashin shan shi ne ya fi, saboda fita daga sabanin malamai yana da kyau.

Don neman Karin bayani duba : Bidayatul-mujtahid 2\67

Allah ne mafi sani.

Zaman Gulmar Shuwagabanni Da ‘Yan Siyasa

Tambaya:

Assalãmu Alaykum, Yaa Shaykh, menene hukuncin magana akan shugabanni da ‘yan siyasa?  Shi ma gulma ne ko akwai banbanci idan mutumin yana da nauyin yiwa al’umma shugabanci da hidima?  Jazakumullahu Khayran

Amsa:

Wa’alaikumussalam, To dan’uwa Allah da manzonsa sun haramta cin naman mutane, sannan malamai suna cewa: gulmar shuwagabanni da malamai ta fi tsananin haramci, saboda cin naman shuwagabanni zai jawo ayi musu tarzoma, kamar yadda cin naman malami zai jawo a raina ilimi, saidai akwai wuraren da ya halatta a ci naman mutane saboda maslaha, kamar idan aka zalunci mutum to ya halatta idan zai kai kara ya bayyana zaluncin da aka yi masa, haka nan idan ya ga wani sharri yana so a taimaka masa wajan gusar da shi to ya halatta ya fadi sunan mai laifin, kamar yadda kuma ya hallata ayi gulmar mutumin da ya shahara da aikata sabo da fasikanci, don a guji sharrinsa. Duba Azkar: 489 da kuma Majmu’ul fataawa 28\221.

A bisa abin da ya gabata za mu fahimci cewa: duk kasar da ake kafa shugaba ta hanyar zabe, to ya hallata mutane su tattauna matsalolin shugaban da yake kai, domin tunanin kawo canji a zabe mai zuwa, musamman idan shugaban ya kasance azzalumi kuma fasiki mai yawan aikata sabo, saidai ya wajaba maganar ta su ta zama gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani.

Hukuncin Aske Wa Yaro Gashi Ranar Bakwai Ga Haihuwa

Tamabaya:

Assalamu alaikum, inawa dr, fatan alheri tambaya ta itace: ina matsayin askin suna a Musulunci?

Amsa:

Wa’alaikum assalam, Aski ranar bakwai ga wata sunna ne saboda fadin Annabi (SAW) (Dukkan abin haihuwa za’a hana shi ceton iyayensa har sai an masa Akika an sanya masa suna, an kuma yi masa aski ranar bakwai ga wata) kamar yadda Tirmizi ya rawaito daga hadisin Hasan daga Samurah sahabin Annabi (SAW)

Allah ne mafi sani.

Jinin Haila Yana Zuwa Min A Yayyanke, Ya Zan Yi?

Tambaya:

Assalamu alaikum Idan mutum yana jinin haila yana mashi kwana shidda. Amma sai yayi kwana biyu ya dauke, bai ganshi a kwana na ukku ba. Sai kwana na hudu ya ganshi. Toh wannan yana cikin kwanukan hailar shi na asali. Kuma zaiyi lissafin kwanan da bai zoba a cikin kwanakin hailar tashi ko YAYA zaiyi

Amsa:

Wa’alaikum assalam Yayyankewar jinin haila, ta yadda yau mace za ta ga jini, gobe kuma ta ga tsarki ko makamancin haka, ya kasu kashi biyu:

  1. Idan kodayaushe haka take gani, to wannan hukuncinta hukuncin mai jinin istihala, ta yadda hakan ba zai hana ta ibada na.
  2. Idan ya zama wasu lokutan take ganin hakan, yawancin lokutan kuma tana samun tsarki, to wannan malamai sun yi sabani akan wannan tsarkin, shin tsarki ne ko kuma yana daukar hukunce- hukuncen jinin haila ne?

A mazhabar malikiyya duk sanda ta ga jini to yana daukar hukuncin jinin haila, haka ma tsarki yana daukar hukunce-hukuncen tsarki, ta yadda za ta yi wanka duk yinin da ta gan shi, saidai idan an hada su sun wuce mafi yawancin haila, to sai jinin da ya wuce ya zama istihala.

Sai dai idan yana yayyankewa kusa kusa, to tana iya jinkirta wankan, sai ta hada sallolin da ba ta ga jini ba a lokutansu, saboda yin wanka a kowanne lokaci akwai wahala a ciki, kuma Allah yana cewa: “Bai sanya muku kunci a cikin addini ba”

Don neman karin bayani duba  Hukunce-hukuncen jinanen al’ada shafi:15.

Allah ne mafi sani.

 

Shin Mece Ce Riba?

 

Tambaya:

Assalamu alaikum Don Allah Malam Mece ce riba a Musulunci?

 

Amsa:

Wa’alaikum assalam To malama riba ta kasu kashi biyu:

  1. Akwai ribar jinkiri, kamar ka ba mutum bashin naira hamsin, ka nemi ya dawo maka da naira sittin, ko kuma idan ka bawa mutum bashi, ya yi jinkirin biya, ka ninninka masa kudin da ka ba shi, irin ribar da ake amsa a banki, za ta shiga cikin wannan bangaren.
  2. Ribar fi-fiko, kamar yanzu, ki bada naira 1100 tsofafi, a ba ki naira 1000 sababbi, ko kuma ki bayar da shinkafa ‘yar gwamnati kwano uku, a ba ki shinkafa ta gida kwano hudu.

Duka wadannan nau’oin guda biyu Allah ya haramta su, kuma ya kwashe musu albarka.

Allah ne mafi sani.

 

Fatawar Rabon Gado (169)

Tambaya:

Assalamu Alaikum Malam dafatan alkhairi Allah yakara lafiya Amin. Macece ta mutu bata taba haihuwa ba.Bata da kowa sai yayanta kuma shima ya rasu amma yabar yayansa maza da mata.Malam yazaa raba gadonta? Wassalam

Amsa:

Wa alaikum assalam. Za a bawa ‘ya’yan yayanta maza kawai ban da mata.

Allah ne mafi sani

 

Exit mobile version