Daga Rabiu Ali Indabawa.
Wani al’amarin da ya shayar da mutane mamakin gaske, kuma lamarn ya yi kama da wasan kwaikwayo shi ne, jana’izar wata mata da aka yi kwanan nan, da aka gudanar. Jana’izar ta zama abin ban al’ajabi, bayan da wani mutum ya yi tsalle ya afka saman gawar kuma ya yi kokarin yin lalata da ita a gaban danginta.
Big Sipiliano, mai shekara 49 daga Epworth a Zimbabwe, ya je wurin jana’izar Melisa Mazhindu jim kadan misalin 1 na dare a ranar 2 ga Janairu tare da wani abokin aikinsa, wanda daga baya abokin nasa ya hana ‘yan uwanta shiga tsakanin abokin nasa abin da zai aikata cikin mummunan harin da ya kai wa gawar.
Sipiliano ya shiga cikin wani daki da inda aka shimfide gawar Melisa Mazhindu, sannan abokin nasa ya toshe kofar dakin, shi kuma ya yi tsallake kan gawar Melisa ya fara kokarin yin jima’i da ita a gaban danginta.
Sipiliano, wanda aka fi sani da “Bigman” an ruwaito cewa, ya gaya wa mahaifiyar Melisa mai suna Phillipa a yayin da a ke makoki cewa, da jimawa ya so ya kwana da ‘yarta mai shekaru 20. Ya gaya wa masu makokin cewa yana son Melisa kuma yana bakin ciki cewa ta mutu kafin su yi jima’i.
Phillipa Mazhindu ta shaida wa manema labarai cewa “Ya fada mata ko da ta mutu, babu wani abin da zai same shi idan ya cika burinsa.” Ta bayyana cewa: “Ya ci gaba da gano gawar, wacce ke kwance a dakin, ya kwanta a kanta, kuma ya yi ta yin motsi da dabarun yin jima’i yayin da abokin nasa ya hana mu shiga.”
Misis Mazhindu, mai shekara 47, ta ci gaba da cewa ta yi imanin cewa za a iya samun wata manufa ta sihiri bayan wannan mummunan harin.
Ta ce: “Ta yaya zan gudanar da rayuwa tare da irin wannan damuwa? Ina zargin wadannan mutane suna da wata manufa ta tsafi saboda lokacin da makwabta suka bincika Bigman wadanda suka kawo min dauki, sun gano mataccen bera, jan kyalle, da kuma wani ganye a cikin aljihunsa. ”
Iyalin Melisa sun yi kokari ba tare da nasara ba don jawo, da suka ga abin ya gagare su sai suka yi kururuwa domin a kawo musu dauki daga sauran masu makoki, inda daga baya aka zo aka fitar da da su shi da abokin nasa.
An tsare Big Sipiliano tare da abokin aikin nasa inda aka shirya kai su kotu a ranar 8 ga Fabrairu kan zargin cin mutunci da lalata gawa, a cewar rahotanni na cikin gida.