Wani mutumin garin Kalifoniya da ya yi hijira zuwa garin Chicago na kasar Amurka saboda gudu kada cutar korona ta kama shi ya zauna a cikin tashar jirgin saman O’Hare na duniya tsawon watanni uku ba tare da kowa ya ankaro shi ba.
Ba a san dalilin da ya sa Aditya Singh, dan shekaru 36 wanda ba shi da aikin yi ya tafi garin Chicago ba da farko, amma hukumomi sun ce ya yi nasarar buya a wani yankin da ke da tsaro na Filin jirgin saman O’Hare na tsawon watanni uku, kafin a kama shi, a cikin makon nan. Singh ya yi zaman dirshan a tashar jirgin tun tsakiyar watan Oktoba, kuma ana zargin wara kila ma ya dade fiye da hakan. Ma’aikatan filin jirgin sun je wurinsa a ranar Asabar, a inda suka nemi da ya nuna shaidarsa ta tafiya.
A duk lokacin da ma’aikatan filin jirigin suka tambaye Singh da ya nuna katin shaidarsa, yana sanye da abin rufe fuska yake nuna masu katin wani manajan ayyuka na filin jirigin wanda ya ba da rahoton bacewa a ranar 26 ga Oktoba, mako guda bayan jirgin saman Singh ya sauka a O’Hare, a inda aka kira ‘yan sanda suka kama wanda ake zargin.
A lokacin da yake amsa tambayoyi a wajen ‘yan sanda, mutumin mai shekaru 36 ya bayyana cewa, ya sauka a O’Hare ne a ranar 19 ga watan Oktoba, amma yana matukar tsoron korona don haka ya ki karasawa gida ya kuma yanke shawarar labewa a tashar jirgin.
An tuhumi Aditya Singh, wanda ba taba samunsa da laifi ba, ana tuhumar shi da aikata laifin haure a tahsar filin jirgin sama da sata. A ranar Lahadi, aka gabatar da Singh a gaban alkali, wanda ya kadu bayan jin zargin da ake yi masa.
“Idan na fahimce ku daidai, kuna gaya min cewa wani mara izini, mara aikin yi ana zargin yana zaune a cikin wani amintaccen yanki na tashar jirgin saman O’Hare daga Oktoba 19, 2020, zuwa Janairu 16, 2021, kuma ba gano shi ba? Ina so in fahimce ku daidai,” in ji Alkali Cook County Susana Ortiz.
An sanya belinsa akan kudi Dala $1,000, amma har yanzu Singh na hannun ‘yan sanda.