Daga Abubakar Abba, Kaduna
Farfesa Binta Abdulkareem, daya daga cikin ‘ya’yan da su ka kirkiro da Kungiyar Kiwon Lafiya mai zaman kanta wato Population Reproductibe Health Initiatibe, ta yi kira ga Gwamnatin jihar Kaduna, nusamman da kuma sauran takwarorinta da ke a yankin Arewacin kasar da su dinga bai wa horas da ‘ya’ya mata kan ilimin kiwon lafiya domin a cike gibing da ake da shi na karkncinsu a yankin.
Binta ta bayar da wannan shawarar ce a tattaunawar ta da da manema labarai a Kaduna kan aikin da kungiyar ta kirkiro da shi na horas da ‘ya’ya mata kan ilimin kiwon lafiya a daukacin jihohin da ke yankin.
Binta, ta kuma jinjina wa Gwamnatin jihar Kaduna kan daukar matakai wajen fara kafa damba kan shirin a shekara mai zuwa, inda ta ci gaba da cewa, ” Idan har bamu da ‘ya’ya mata a karkara da za su gudanar da aikin kiwon lafiya, musamman kan kiwon lafiyar mata, wasu matan ba za su iya fito wa fili su fadi cuwukan da ke danunsu ba, domin a bisa al’adarsu, ba sa bukatar ma’aikacin kiwon lafiya namji ya duba su ba”.
In za’a iya tunawa, Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya ruwaito cewa, aikin na horas da ’ya’ya mata kan ilimin kiwon lafiya wato Girls for Health (G4H), an kirkiro da shi ne bisa nufin ciki gibin da ake da shi na karancin ‘ya’ya mata a bangaren ilimin kiwon lafiya da aka jima ana fama da shi a Arewacin Nijeriya.
Bugu da kari, aikin wanda ba a cikin akumma ake gudanar da shi ba, ana gudanar da shi ne, a makarantu Boko, inda kuma tuni, aka wanzar da aikin a wasu makarantu, an kuma faro aikin ne, a shekarar 2016 a jihohi hudu da su ka hada da, Kebbi, Sokoto, Jigawa da kuma Kaduna, wanda kuma Gidauniyar Bill and Melinda gates ce ta ke daukar nauyi.
Farfsa Binta ta ci gaba da cewa, “Aikin ya taimaka wa ‘ya’ya mata ‘yan makaranta da jimlarsu ta kai 375, inda hakan ya kai kashi 125 a cikin kashi dari, inda kuma wasu 113 tuni, aka samar ma su da guraben karatu a jami’oi da ban da ban kuma daga ciki, 375 da su ka amafa, 113 tuni an samar ma su da guraben karatun a wasu jami’oi da ke kasar nan”.
A cewar Binta, “42 tuni, kuma sun samu guraben bayar da horo kan ilimin kiwon lafiya a wasu cibiyoyin bayar da horo kan ilimin kiwon lafiya, inda 22 su ka samu guraben karo ilimi, 28 kuma a Kwalejin Ilimin, 10 a makarantun kimiyya da fasaha wato polytechnic 11 kuma a sauran manyan makarantu”.
Ta bayyana cewa, daliban ‘ya’ya mata da su ka amfana, ma fi yawancinsu, ‘ya’yan marasa karfi ne kuma daliban ‘yan ajin karatu matakin sakandare na SS2 ne, kuma duk munyi hakan ne bayan gudanar da bincike domin gano iya kokarinsu kafin bayar da daukin domin samar ma su da kyakyawan yanyi, samun horon tare da kuma wanzar da shirin biyan kudin zana jarrabawarsu ta WAEC da JAMB.
Binta ta ce, ” Mun gudanar da gasa tsakanin makaranta da makaranta, a karkashin aikinmu na horas da ‘yan makaranta ‘ya’ya mata ga makarantu biyar tare da kaisu ziyara a wasu asibitoci, inda su ka koyi yadda kwararrun kiwon lafiya su ke gudanar da ayyukansu, yadda in sun koma cikin alumominsu za su iya bayar da taimako a fannin kiwon lafiya akalla a shekaru biyu, inda bayan sun zamo kwarrun jami’an kiwon lafiya za su taimaka sosai”.
Ta ce, ” Mun kuma gudanar da ginshikin bayar da horo kan ilimin kimiyya domin kara ba su reno kan gudanar da gasar zana zama jarraba wa ko kuma zana jarrabawar aure, tare da kuma gudanar da bincike domin tabbatar da alfanun aikin kan kokarin daliban, inda ta kara da cewa, tare da goyon bayan aikin, hakan ya sanya wa iyayensu zimmar tura ‘ya’yansu mata zuwa makaranta domin su ma su kara jajirce wa wajen yin aiki tukuru domin fuskantar kalubalen da ke gabansu da kuma bai wa ‘yan baya kwarin gwaiwa.
Binta ta yi kira ga ‘ya’ya mata ka da su fitar da rai, amma su tashi tukaru, wajen cimma mafarkansu, inda kuma ta yi kira ga iyaye da su ci gaba da kara wa ‘ya’yansu mata kwarin gwaiwa, musamman wajen neman ilimin kiwon lafiya yadda su ma za su bayar da ta su gudunmawar a fannin.
A karshe, Binta ta yi kira ga masu bayar da dauki a bangaren kwon lafiya ka da su gajiya wajen tallafa gwamnati, musamman wajen bai wa ‘ya’ya mata horo kan ilimin kiwon lafiya, inda ta kara da cewa, mun lura cewa, da aikin irin wannan, za a kuma iya wanzar da shi a cikin alumma ganin cewa, za a Iya janyo shugabannin alumna domin amfanin ‘ya’ya mata da su kabfito daga gidajen marasa karfi.