Ya Zan Yi Idan Mijina Ba Ya Iya Biya Min Bukata?

auntybaby790@gmail.com 08028586967

’Yan uwana mata barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jinni, wato SIRRIN IYAYEN GIJI… a jaridarku ta LEADERSHIP A YAU LAHADI.

Kamar yadda ku ka sani, shi wannan shiri a na yin shi ne, don matan aure zalla, domin ba su shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zamantakewarsu da mazajensu da mu’amalarsu ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki, irin abubuwan da su ka kamata mu mata mu dinga ci domin karin ni’imarmu da gamsuwar mazajenmu da ma duk wani abu da ya shafi rayuwar ’ya mace.

Da fatan za ku dinga bibiya ta a cikin wannan shafi. Gurin da na yi kuskure, sai na ce Ina neman afuwar ubangiji da afuwarku, domin ajizanci irin na dan adamtaka, gurin kuma da na yi daidai sai na ce Allah Ya hada mu a ladan bakidaya.

A wannan makon zan amsa tambayoyin da wasu daga cikin masu karatu su ka aiko ne. Bismillah:

Tambaya: Assalamu alaikum. Anty Baby, tambayata a nan ita ce, ni mijina ba ya biya min bukata a shimfida. Ma’ana; ta wajen jima’I; mu na fara saduwa idan ya samu biyan bukatar kansa shikenan sai ya daga ni ko da kuwa ban ji dadi ba. Ba ruwansa da sha’awar da zan kasance a ciki kuma ba ruwansa da damuwar da zan yi. Shi kansa kawai ya sani. Haka ma gobe idan ya zo zai kuma yi. Abin nan ya na matukar damu na har na ji na fara tsanar sa a raina. Meye shawararki, Anty Baby?

Amsa: ’Yar uwa ya na daga ilimin da ya kamata a dinga sanar da mutanen da su ka mallaki hankalin kansu shi ne ilimin jima’i a Musulunci. Manzon Allah (saw) ya ce, kada dayanku ya afka wa matarsa, kamar yadda jaki ya ke afkawa jaka. Idan dayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika dan aike, wato ya kamata a ce kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha’awa, domin samun gamsuwar su kansu ma’auratan. Sannan idan mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gare shi, saboda wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata gamsuwar.

Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne karshen rashin adalci. Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba. Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashun kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da ya ke yi ma ta dadi, kuma wannan ke sa mace ta dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa dalili. Nan kuwa rashin ba ta hakkinta a shimfida ne ya jawo ma sa.

Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai karfin sha’awa, wacce idan ba ta sami daidai ita ba, akwai damuwa. Sai dai ka ga auren ya na kai kawo. Karshe dai sai an rabu hankalinta zai kwanta. Ba yin ta ba ne; haka Allah Ya yi ta. Haka su ma mazan, wani idan ya sami wata matar, da kanta za ta gudu. A-yi-a-yi ta dawo, ba za ta dawo ba, amma wata ta na kokari ta sanar da ’yan gidansu cewar ya fi karfinta.

Shawara ga mata da mazan da ba sa iya biya wa junan bukata; su sani ba sai ta kai su ga rabuwa ba. Idan ka san ba ka da juriyar da za ka iya biya wa matar ka bukata a shimfida ba, to ka dinga wasanni da ita sosai kafin ka shige ta, kuma ka tabbatar ka gane guraren da idan ka tattaba ma ta ta ke jin dadi sosai yadda kafin ku zo saduwa ka gama tayar ma ta da sha’awarta, ta fara jin dadi sosai. Ka ga ka na shigar ta, kafin ka biya bukatarka, ta gama jin dadinta. Za ka ji ta sharkaf; komai ya yi daidai. Shawara ta biyu; ka kasance mai neman maganin karin karfin mazakuta da darin kuzari yadda matar taka za ta ji ka gagau.

Uwar gida idan mijinki ya na fama da rashin karfin mazakuta ko ba ya biya miki bukatarki a shimfida sai ki yi ma sa wannan hadin, ki samu:

Bakin gagai

Jan gagai

Namijin goro

Tsintsiyar maza

Tatarida

’Ya’yan Dabino

Citta mai yatsu

Masoro

Barkono

A hade, a dake su a tankade lukwui a dinga zuba ma sa a farfesu ko gasashshen nama ya na ci ko ki tafasa ma sa ki sa zuma ya dinga sha kamar shayi.

 

 

Tambaya: Anty Baby, mene ne maganin warin baki da yadda zan magance shi?

Amsa: A abubuwan da ke janyo warin baki akwai rashin wanke baki bayan an ci abinci, domin a yadda a ke so, duk sa’adda mutum ya ci abinci da dare ne ko rana a na bukatar ya wanke bakinsa. Babu shakka duk yadda bakin mutum ya ke da tsafta, to idan ya ci abinci ya bar bakin tsawon awa guda bai wanke ba, to fa kwayoyin cuta ne za su taru, don su cinye guntun abincin ciki. Idan sun gama kuma su fara cin hakora. Daga nan sai bakin mutum ya rika wari. Sannan da yawa daga cikin mutane sun dauka wanke baki sai an tashi daga barci ne kawai, tunda a lokacin ne ake jin bakin ba dadi. To, bincike ya nuna wanke baki da dare kafin kwanciya ya fi amfani fiye da wankewa da safe.

Shawarar da zan ba ki a nan ita ce, ki nemi man kanumfari ka rika wanke baki da shi sau uku a rana, haka ma duk lokacin da ki ka ci abinci ki nemi ruwa ki wanke bakinki, sannan ki nemi citta ki rika tauna ta a lokacin da za ki yi barci tsawon kwana bakwai. Haka kuma ki nemi gawayi ki dandaka shi, ki hada shi da gishiri ki rika wanke baki da shi ko sau biyu a rana. Sannan shi kansa gawayin a na tauna shi da hakori a tsotse ruwansa, don ya na maganin warin baki.

Haka a na zuba danyen wake guda uku a abi a tauna a tsotse ruwan a zubar da tukar. Hakan ya na maganin warin baki. Bayan nan ki nemi Apple Sider Benger ki rika shan cokali uku a lokacin da za ki yi bacci.

Haka a na watsa kanumfari guda uku ko sama da haka a baki a dinga tsotsa. Ya na kawar da warin baki kuma ya na saka kamshin jiki. In sha Allahu idan ka bi wadannan hanyoyi za ka samu waraka da yardar Allah.

’Yan uwana mata, baki ya na taka rawa wajen mu’amalar soyayya a wajen mijinki; kar ki bari mijinki ya zo zai sumbace ki ya ji bakinki ya yi ba dadi. Ki kasan ce mai kula da bakinki yadda duk sanda angonki ya so ku hada baki, domin ku ji dadin rayuwa; ya ji daddadan kamshi na fitowa daga bakinki. Amman idan ki ka bari ya ji banki ya na wari, za ki fita daga ransa. Take sha’awarsa za ta dauke daga kanki, kuma zai ji ya fara tsanar ki.

 

Bari na bar ku haka, sai wani makon idan Allah ya kai mu

Exit mobile version