Shugaban hukumar kula da nada alkalan wasa na kasa, Alhaji Ahmed Yusuf ya yabawa alkalan wasan da suka yi alkalancin wasannin gasar firimiya da aka kammala a karshen satin nan, inda yace alkalan was an sun yi alkalanci yadda ya ka mata kuma ya basu maki 70% cikin 100%.
Alhaji Ahmed yace, jajircewa da sadaukarwa ce ta sa har hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afrika ta zabi alkalan wasa daga Nijeriya suka yi alkalancin wasa a wasannin share fagen shiga wasannin nahiyar Afrika da na shiga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya wanda za ayi a kasar Rasha a shekara mai zuwa.
Shi ma a nasa bangaren shugaban alkalan wasa na kasa, Mista Tade Azeez ya yabawa alkalan wasan inda yace sun yi abin a zo a gani. Sai dai dole akwai wasu ‘yan matsaloli wadanda sai a hankali za a yi maganinsu.
Ya ce “Alkalin wasa shi ne wanda yake kula da dukkan abubuwan da suke faruwa a cikin fili kuma yayi alkalanci ba tare da nuna bambanci ba sannan kuma yayi alkalanci kamar yadda dodokin wasa suka tanadar”.