Shafin TASKIRA shafi ne da ya saba zakulo muku batutuwa daban-daban wadanda suka shafi al’umma. Tsokacinmu na yau zai yi duba ne game da irin matsalolin da wasu ‘yan matan ke fuskanta a wajen samarinsu.
Wasu daga cikin ‘yan mata na kokawa game da yadda suke kashe kudadensu ga samarinsu, wajen yi musu girki me dadi don kyautatawa. Yayin da su kuma samarin suke kade jiki su tafi bayan sun kammala cin girkin da aka yi musu, ba tare da sun bawa budurwar ko fucika ba.
- Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
- An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Dalilin hakan ya sa wannan shafi jin ta bakin wasu daga cikin mabiya shafin game da wannan batu; “Ko me ya sa wasu samarin ba sa bawa ‘yan mata kudi bayan sun yi musu girki?, Shin kin taba fuskantar irin hakan wajen samarinki?, Haka kai ma, ka taba haduwa da budurwar da ta yi maka girki, amma baka taba bata kudi ba ko kuwa ka taba bata?, Shin yi wa saurayi girki a cikin soyayya, wane tasiri yake da shi ga masoya?.
Ga dai bayanan nasu kamar haka;
Sunana Na’ima Jamilu Jihar Kano:

Wannan abu ba mai bullewa bane, don masu iya magana kan ce yaba kyautà tukwici. Kuma sam-sam ba abin da ya dace bane, ko da ace ba za su bayar kullum ba, amma su dan rika bayar wa kodan su rika karfafawa ‘yan matan gwiwa. Eh tabbas yi wa saurayi girki yana tasiri a soyayya sosai ta hanyoyi da yawa, kamar shaho kan namiji wajen kariwar soyayya dà sauransu.
Sunana Sammani Yusif:

Su in muka kyautata musu wani abin suke bamu tukwici, godiyar arziki ma sai kayi da gaske za ka samu mai maka godiya in ka kyautata mata. Wata budurwar gani take ma tun kafin ka aure ta ya zama dole ka kashe mata kudi, sai kace a bola muke samun kudin.
Sunana Sa’idu Haruna Abdulkadir:

Gaskiya ba capacity a cika maka ciki ka tashi ka fece ba tare da ihsani ba, amman ya danganta da irin yadda ‘relationship’ na ku yake da ita ‘maybe’ ko tana ‘benefiting’ da kai ta wani ‘side’ din. Amman kyauta tana kara dankon kauana.
Sunana Aminu Ilyas Isah (Farfesa):

Hakan ai ‘normal’ ne, ita budurwar ai ba don a biya ta tayi ba. Idan dole sai ka dauki kudi ka bata ne to gara ka je ‘restaurant’. Tunda take min girki ina ci ban taba bata ko sisi ba, amma haka kawai sai in kyautata mata ta hanyar siyo mata wani abu me kyau. Soyayya fa ba kasuwanci ba ce ba. Yana kara dankon soyayya, kada ka kuskura ka saba mata da bata kudin in tayi maka girki, amma dai ka rika kyautata mata akai-akai. Haduwar zuciyoyi guda biyu ne soyayya ba kasuwanci ba.
Sunana Khadija Zahraddin Jihar Kaduna:

Gaskiya muna fama da wannan matsalar, tsakani da Allah mace ta takarkare ta yi wa namiji goma ta arziki amma sai yayi zuwa goma bai iya zaro komai a aljihu sau daya ba, tun daga waje muke gane namiji me mammako ba macen da take son namiji me mako, in tana so ta kyautata masa wata har ranto kudin take a ganinta zai iya bata wani abu ta mayarwa masu shi. Kuma hakan ai ba wai son kudi yake nunawa ba, ita ma ai kyautatawa ta yi masa kuma kashe kudi aka yi, dan me shi ba zai kashe ba kenan ma ba so na kake ba.
Sunana Muhammad Uba Tsoho:

Shawara ga ‘yan mata a rika yin komai tsakani ga Allah sai aga daidai. Samari kuma a rika ragewa mata ‘subcide’, sabida wasu iyaye ne suke basu.
Sunana Fatima Nura Kila Jihar Jigawa:

Wasu samarin ba wai basa bayarwa bane, idan suka bayar za a raina shi ya sa ba sa bayar wa. Sannan su ma matan wani lokacin mun kasance sai mun yi abu na karya wanda ya fi karfin mu. Gaskiya ta bangare na ban taba haduwa da wannnan ba, domin komai na kan yi daidai karfi na. Shawarar da zan bayar matukar saurayi ba a gari yake ba dan an yi masa ba wani abu bane kyautatawa ce, me yuwa shi ma yana kyautatawa ta wani fannin.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary) Jihar Kano Rano LGA

Ke budurwa ki sa a ranki za ki yi wannan girkin ne domin kyautatawa, Haka kai ma saurayi ka yi mata ihsani ko da bai kai kudin wannan girkin ba domin yabawa. Eh na taba cin karo da hakan amma gaskiya ni dai na bata kudin. Yanada tasiri sosai domin ta nan ma za ka gane ta iya girki ko bata iya ba. Shawarata a nan kuma ita ce ‘yan mata kudaina yin girki wai domin a biya ku, abin da ku ka kashe haka kuma samari bai kamata ku ci girki ku cika riga da iska ba













