Wani ɓarawon mota ya shiga fadar Gwamnatin Jihar Kano da safiyar ranar Litinin, tare da sace wata mota ƙirar Toyota Hilux da ke cikin jerin ayarin mataimakin gwamnan jihar.
Daily Nigerian ta ruwaito cewa ɓarawon ya shiga fadar ta ƙofa ta 4 kuma ya fita da motar da misalin ƙarfe 5 na safe.
- Bayan Ganawa Da Tinubu, COAS Ya Tabbatar Wa ‘Yan Nijeriya Samun Ingantaccen Tsaro
- CIIE Ya Kasance Gadar Sada Tattalin Arzikin Kasar Sin Da Na Duniya
Bidiyon na’urar tsaro ta CCTV da aka duba daga baya ya nuna cewa ɓarawon ya fita ne ta ƙofar shiga ta gaba ba tare da an tsayar da shi ba.
An ce motar da aka sace tana cikin jerin motocin da mataimakin gwamnan jihar ke amfani da su.
Wata majiya ta bayyana cewa ana bai wa yankin ofishin mataimakin gwamnann tsaro ne kawai a lokacin aiki ko kuma idan yana aiki.
An kama diraben da ke jan motar Shafiu Sharp-Sharp, domin yi masa tambayoyi.
“An riga an fara bincike. Ana yi wa direban tambayoyi, yayin da Babban Jami’in Tsaro (CSO) ke duba bidiyon CCTV,” in ji wata majiya.
“An miƙa bayanan motar ga jami’an tsaro domin su gano motar da kuma kama ɓarawon.”
Kakakin gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, bai amsa kiran waya da saƙonnin da aka tura masa ba.













