Yadda A Ka Gudanar Da Jana’izar Shugaba Umara Scissors A Maiduguri

Da yammacin Alhamis 8 ga Agusta, 2019 a ka gudanar da jana’izar Shugaba Umara Gana Scissors bisa tsarin addinin Musulunci a gidansa da ke unguwar Damboa Road cikin birnin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Shugaba Umara ya rasu ne bayan ’yar jinyar da ya yi fama da ita.

Kafin rasuwarsa, Shugaba Umara ya kasance daya daga cikin giga-gijen jam’iyyar APC mai mulki a jihar Borno. Sannan kuma shi ne shugaban jami’yyar APC a Arewancin jihar Borno.

Shugaba Umara ya rike mukamai iri daban-daban a karkashin gwamnatin jihar Borno.

Duban dubatan al’ummar jihar ne suka halarci jana’izar nasa da aka gudanar da yammacin ranar Alhamis a gidansa dake Damboa road.

Jama’a da dama na ci gaba da aike wa da ta’aziyya ta kafafen watsa labarai da ma na soshiya midiya.

Mu na rokon Ubangiji Allah ya gafarta masa kura-kuransa yasa mutuwa hutu ce garesa ya albarkaci zuriyarsa, mu kuma idan tamu tazo ya kyautata karshenmu. Amin.

Exit mobile version