Haruna Akarada" />

Yadda A Ka Nada Wa Wanzaman Nassarawa Sarauta A Birnin Kano

A wannan makon ne wasu wanzamai da ke karamar hukumar Nassarawa a yankin Kaura Goje su ka amfana da rawunan mukamai na sarauta, wanda Galadiman Nassarawa na Wanzamai wanda wakilin Maitafari kuma Sarkin Bindigar Kano ya ba shi umarnin yin nadin.
Wannan nadi an yi shi ne a unguwar Kwana Hudu ta Rimin ’Yan Soye da ke karamar hukumar Nassarawa a birnin Kano, inda tarin masoya su ka halarci wannan nadin da a ka yiwa sama da wanzamai 15.
Wannan nadi wasu da ma sun gaje shi ne, wasu kuma shi ne farkon samun wannan sarauta.
Wakilinmu ya samu ganawa da kadan da wadanda su ka amfana da wannan matsayin. Mutum na farko shi ne Shehu Sa’adu, wanda a ka ba wa shamakin askar Nassarawa. Ya shaidawa wakilinmu asalin wannan sarauta.
Malam Shehu ya ce, wannan nadi da a ka yi ma sa da ma shi ya gada ne da shi da wansa, kuma su sun gaji wannan wanzanci ne.
Shi ma wani da ya samu wannan matsayi na mataimakin Sardaunan Nassarawa ya godewa duk wanda su ka samu zuwa wannan biki. Akwai Garba Sa’adu, wanda wanzan ne da ke Shingen Bulkaki ya ce dama wannan sarauta gado su ka yi.
Ya ce, “akwai wani gari a kasar Hadeja wanda a ke ce ma sa Dakaiyawa, to a wannan gari kakana shi ne Madaki. Da Allah ya yi ma sa rasuwa sai a ka ce babana ya zo a nada shi wannan matsayi, sai ya ce a’a, tunda ni Ina nan Kano, to ga dana nan a nada shi.
“To, Allah da iko sai ya yi mar gajeren kwana. Daga nan sai ta komo kan babana. To, Allah da ikonsa ga shi yanzu Ina nan Kano na samu wannan sarauta ta Madakin Wanzaman Nassarawa.”
Shi kuwa Kabiru ya samu matsayin Makaman Askar Nassarawa ne. Shi kuwa Usman ya samu Wakilin Askan Nassarawa ne a jerin mukaman da kowa ya amfana. Shi kuwa Musa Abdulkadir ya yi godiya ga duk wadanda su ka zo wannan guri.
Danladi Muhammad wanda shi ne shugaban kungiyar wanzamai na jihar Kano, ya nuna farin cikinsa da wannan nadi, inda ya ce, duk wadannan matasa ’ya’yansa ne. Don haka babu abinda za su yiwa Allah sai godiya.
Bashir Abdillahi shi ne Madakin Bindigar Jihar Kano kuma shi ne shugaban wannan biki; ya ce, ya na jagorantar wannan biki ne a karkashin Sarkin Askar Nassarawa, kuma ya yi farin ciki da wannan biki.
“Babu abinda za mu ce da Allah sai godiya,” in ji shi.

Exit mobile version