Connect with us

MAKALAR YAU

Yadda A Ke Hayaniyar Rabon Kudi Tsakanin Gwamnatocin Nijeriya

Published

on

‘Yan Nijeriya da daman gaske ba su da

masaniya kan yadda gwamnatocinsu

ke rabon arzikin da kowa a kasar

yake da hakki a kai. Kawo bayani

game da yadda ake rabon kudin zai

kara wayar wa da ‘yan kasa kai da

kuma auna ko shin tsarin rabon

yana bukatar garambawul ko a’a?

A cikin satuttukan da suka gabata,

na karanta litattafai biyu da ba su da

nasaba da juna. Littafi na daya shi ne

da ake kira a Turance (China’s Great

Wall of Debt by Dinny McMahon) da

kuma na biyun da ake kira a Turance,

(Fighting Corruption is Dangerous)

wanda tsohuwar ministan kudi

Ngozi Okonjo-Iweala, ta rubuta.

Duk da haka kamar yadda litattafan

ba su da nasaba da juna, na kasance

na tsinci kaina a kan rashin samun

sukuni wajen kwatanta litattafan

biyu.

Bari in fara da na kasar China,

inda marubucin litatafin ya yi

kokarin ya yi bayanin tagomashin

da ‘yan siyasa na gida da shugabanni

suke da shi idan aka zo maganar

tara kudi da kuma yadda za a kashe

kudin. Ba kamar a Nijeriya ba, inda

wani irin hanyar tara kudin shiga,

kamar haraji na gwamnatin tarayya

da sauran haraji da za ka biya na abin

da kake samu yake zama na jihohi,

dukkan harajin kudin shiga na haraji

matakan gwamnati su ne suke

rabawa a kasar China a bisa kasafi

daban-daban.

A aikace, karamar hukuma tana

yin amfani da ikon da take da shi

wajen yin komai don kasuwanci

ya dore saboda ta san cewar in har

wannan kasuwancin nata yana

samarwa da kuma sayarwa, za ta

karbi kasonta na haraji a kan kayan

da ta sayar kuma za ta dauki wannan

ribar da ta samu ta sake zubawa a

cikin jarinta don kara karfafa tattalin

arzikinta na gida wanda dama shi

ne babbar manufar ciyar da kasarta

gaba a hukumance. Alal misali,

idan kasuwanci yana durkushewa

tagomashin ga shugaban karamar

hukumar, kodai a kara samun wani

sauki ga kamfani don saye ko kuma

a samu wasu bankuna mallakar

gwamnati da za a zuba kudin don a

cigaba da juya kudin. Akwai dinbin

matsaloli game da wannan tsarin

amma wannan shi ne yadda ya fi

dacewa a kan yadda za a iya kwatance

a kan yadda aka tsara tagomashin

siyasar kasar China.

Yanzu kuma a kan littafin Okonjo-

Iweala, a zuciya ta littafin nata a

hakikanin gaskiya da ‘yan Nijeriya

take tana tsokaci ne a kan kasashen

duniya, inda take samun na tuwo.

Amma ainahin tsokacinta yana cikin

sashe hudu na littafin nata ne, inda

ta bayyan murdadden hanyar kasafin

kudi.

Har ila yau, a cikin wannan

sashen na hudu, za ka iya ganin

komai a kan abubuwa da ba su yiwa

Nijeriya kyau ba. A cikkin littafin

nata, ta tattara bayanai da dama da

suka shafi fada da kuma hayaniya da

yawa a tsakanin matakan gwamnati

daban-daban a kan magana daya da

kuma yadda za a raba kudade. Abin

da wannan zai sanya ka fahimta shi

ne, Nijeriya tana da jiga-jigan ‘yan

siyasa da ba wanda ya san yadda a

hakikanin gaskiya ake habaka kudin

shiga ko tattalin arzikin kasar ba

kamar kasar China ba kamar yadda

aka zayyana a sama.

Tsarin cike yake da yadda ake

rabawa, in har ka san yadda za ka

habaka, ba za ka yi wani nisa ba a kan

kwarewar ka sai dai ka durkushe baki

daya. Lamarin bai da kyau ga kowa

ganin cewar, tun daga bangaren

‘yan majalisa har zuwa bangaren

zartarwa, a yanzu sun san a cikin

sauki daga kasafin kudi na farashin

danyen mai zuwa dala daya, ya kai

karin Naira biliyan 50 don rabawa

a cikin kasafin kudi. Kamar yadda

za ka iya yin tunani, wannan daga

baya ya zamo fagen fama. Wannain

shirmen da kuma rashin tabbatar da

tsari, za ka iya gani idan jigogin ‘yan

siyasa na Nijeriya suke yi kanjiki

kankarfi a kan wani abu da ba su da

iko a kai.

A shekarar 2013, bangaren

zartarwa sun yi kirdadon Dala 72

na gangar danyen mai. Majalisar

dattatawa sun bijiro da batun sanya

dala 76 a matsayin kudin gangar mai

wanda kari ne na Naira biliyan 200

da za a raba, amma majalisar wakilai

a lokacin shugabancin Aminu

Tambuwal,ta bijiro da Dala 80, wani

karin Naira biliyan 200 da za a raba,

a bisa cewar yaya za ka adana kudi

alhali kana fama da jin yunwa? A

karshe dai bayan kai ruwa rana da

akai ta yi da cacar baki, sun amince

a kan dala 79.

Bugu da kari, a shekara ta gaba,

nan ma an yi cacar baki, inda Dala

ta kai 76.50, kuma bayan fadan da

aka sha faman yi, Dalar ta kare a

kan 78. Sai dai wani hanzari ba gudu

ba, farashin mai ya fara karyewa a

cikin watan Agustan shekarar 2014,

inda aka dawo da kudin zuwa Dala

73 daga baya kuma ya sauka zuwa

Dala 65. Farashin mai a Nijeriya har

yanzu abin dariya ne ganin Nieriya

ta kare a karshen shekara a kan Dala

58. Babu wata nasara da aka samu a

kan fasa wajen hako mai da Nijeriya

ta kirkiro. Nijeriya karamar kasa ce a

duniya wajen sarrafa mai.

Hanya daya da Nijeriya za ta iya

samar da canji a kan farashinta na

mai a lokacin da ‘yan tsagerun Neja-

Delta suke tashen farfasa bututun

mai a yankin, inda hakan ya janyo

Nijeriya ba ta amfana da komai ba.

Dokar masana’antar mai mai yuwa

zata iya samun dama wajen habaka

kudinta na shiga saboda shekaru

masu zuwa nan gaba. Komai a kan

farashin mai, ba a kan iya tafiyar

da shi baki daya a Nijeriya. Duk da

haka, jigajigan ‘yan siyasa, suna da

kwarewa daya ce a kan yadda za a

raba kudi. Wannan abin mamaki

ne a ce Nijeriya da ke da yawan

al’umma da suka kai yawan miliyan

180, mutane in sun farka dukkan

safiya suna bin wadannan da ake

kira shuwagabanni.

Shin ina suke son su jefa

makomar kasar nan? Kuma Nijeriya

kamar jaririya ce. Za su iya yin shiru

a yanzu saboda babu kudi da yawa

da za a raba amma za ka iya tsimayin

karin yawan yin fada a kan rabar da

kudi, musamman ganin cewar kudin

nan ba da jimawa ba, farashin mai

yana kara hawa.

A wasu kasashen idan suna fama

da matsalar kudin shiga, sukan

zauna su tattauna a kan ko su kara

haraji zuwa kashi kaza koda kuwa

karin harajin zai haifarwa al’ummar

kasar matsala. Shugabanin Nijeriya

ba sa nuna damuwa a kan zama don

su tattauna irin wannan matsalar.

Yadda kudin zai kara habaka shi ne

babban ciwon kan. Lallai Allah yana

son Nijeriya domin saboda hakan ne

ya sa kasar ta ci gaba da dorewa duk

da cewar shuwagabannin ba su san

akalar da suke ja ta kasar ba.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: