Hamza Dawaki" />

Yadda A Ke Sauraron Mace

Hanya mafi girma da namiji zai iya samun soyayyar mace, ita ce ta hanyar sadarwa. A wurin mace, sadarwa tana da matukar muhimmanci fiye da tsammani. Idan har mutum ya nakalci yadda ake sauraren mace, to hakika zai samu dukkanin soyayya da yarda da kulawarta gare shi.

Babbar matsalar da maza suke samu yayin sauraren mace, ita ce, nan da nan za su yi fushi, su bata rai, su kuma kasa fahimtarta. Saboda sun manta cewa mata daga wata duniya ta daban suke. Wadannan misalan na kasa misalan irin yanayin da kan faru ne yayin tattaunawa tskanin miji da mata. Wadanda suke bayyana yadda akan samu bambancin fahimta a tsakaninsu.   

Hanyar Saurare Ba Tare Da An Fusata Ba.

1. Abu na farko shi ne, magidancin ya  sani cewa bacin rai yana faruwa ne idan aka gaza samun fahimtar juna a tsakaninsu.

2. Namiji ya kudure a ransa cewa,tabbas a cikin kalamanta dole za ta bata masa rai. Saboda zai ji kamar dana nema ta dora masa laifin da ba nasa ba. To ya yi hakuri, ya ci gaba da saurare, a hankali zai fahimce ta.

3. Maigida ya sani cewa, ba wai koda yaushe ne burin zuciyar mutum zai kasance a kan daidai ba. Amma tabbas a kowane lokaci burin zuciya yana da muhimmanci. Saboda haka (kenen) ya kamata ya tsaya ya saureri duk abinda yake cikin ranta ko da kuwa ya kasance ya saba da ka’ida. Domin ba wa wannan burin nata lokaci a saurare shi abu ne mai matukar girma a wurinta.

4. Ya danne zuciya, ya kuma kwantar da hankali. Sannan ya tuna bambancin dake tsakaninsu. Sai ya kwatanta yadda  take  ji, kasancewrta mai yi wa rayuwar kallo ta wata mahanga da ban.

5. Kar kuma ya manata, a can cikin ransa cewa shi fa riciki yana faruwa ne idan mutum bai san yadda zai tunkare shi ba. Don yana ya rika kaddarwa cewa daga karshe dai zai ya shawo kan matsalar. Za kuma a samu daidaito tsakaninsu. Domin idan ma ya gaza yin wani abu da zai kwantar mata da hankali daga karshe, wannan sauraren nata da ya yi kawai ya isa wani abu mai muhimmancin da zai tafi da kaso mai tsoka na damuwarta.

6. Kar maigida ya damu don ta ki karbar shawarar da ya ba ta don warware matsalarta. Ya tuna cewa ita fa ba wai wannan shawarar take nema ba. Ya danne zuciyarsa, ya dena gaggawar bayar da shawara.

7. Magidanci ya tuna cewa, ya kamata ya nuna ya fahimci manugfarta, ko da dai ba zai ce ya yarda da ita kai tsaye ba.

8. Idan yana da wata mahanga  da ban , wadda yake ganin ita ce ta fi wadda take son bayyanawa, to kar ya kawo tasan, ya bari sai ta gama kawo tata din.

9. Kar ya daga murya yayin da suke tattaunawar.

10. Kar ya manta cewa ba wai dole ne sai ya fahimce ta dari bisa dari sannan zai zama cikakken mai sauraro ba. Fahimtar wani bangare (musamman mafi tsoka) daga cikin kalamanta ma yana da muhimmanci.

11. Idan bai fahimci wani bangare na abin da take fada ba, ya sanar da ita cewa bai fahimta ba. Ya kuma yarda cewa kasa fahimta ta yi, ba wai ita ce ba ta iya maganar ko bayanin da za a fahimce ta ba.

12. Ya tuan cewa bas hi ne sanadin bacin ranta ba. Amma  tare da haka zai ji kamar tana dauko duk laifin tana kokarin dora masa.  To hakan kar ya saa ya ki ko ya dena sauraren ta.

13. Kar ya kare kansa, har sai ya bari ya saurare ta, an kai wani bigire da ta tabbata cewa ya fahimce ta. Idan ta zo wannan gabar, to babu laifi daga baya ya nusar da ita nasa dalilan a hankali. Ko kuma kawai ya nemi yafiyarta.

14. Kar ya manta cewa, sau da yawa idan ya kasa fahimtarta, tsora ne ya hana ta iya fito da wasu bayanan, wadanda da ta fito da su da zai fahimta. Domin a can cikin zuciyarta yana daukan kanta tamkar wata karamar yarinya ce. Wadda take cike da tsoron kar ta yi wani abin a ga baikenta, ko kuma a wulakanta ta. Wadda kuma take matukar bukatar kyautatawa da tallafinsa wurin karfafar gwiwarta.

15. Kar ya damu da musanta wasu daga cikin maganganunta wadanda ya tabbatar da cewa ba gaskiya ba ne. Maimakon haka, idan ya fuskanci ta dau zafi sosai, zai iya cewa a bar tattaunawar zuwa an jima kadan. Ta hanyar fita zuwa masallaci ko sayen wani abu. In ya dawo su dora. A lokacin ta dan kara  samun saukin damuwa, zuciyarta ta yi sanyi, yadda za a fi samun saukin tattaunawa cikin lumana.

Idan har namiji zai saurari mace ta bayyana dukkan damuwarta, ba tare da ya katse ta ba, to tamkar ya ba ta wata gagarumar kyuata ce. Wadda ita kuma samun wannan ne zai ba ta dama ta bude dukkanin kofofin kyautata masa da nuna masa dukkanin soyayya da yarda. Kuma idan har magidanci zai iya bin wannan matakan babu abin da zai sa ya iya sauraren matarsa. Kuma babu abin da zai sa sauraren nata ya karke da rikici tsakaninsu.

Mutane da yawa suna da tunanin zama a saurari mace ma shi ne abin da yake haddasa fada. Daya daga cikin abubuwan da na ji daga bakin mutane wadanda ake zargin suna haddasa rikici tsakanin ma’aurata kenan. Har ma wasu suna ganin zama a gida sam ba shi da amfani. Saboda da zarar ka zauna kun ci gaba da hira, to tabbasa za a kawo wata magana wadda daga karshe za ku kasa fahimtar juan, har kuma ta kai ku ga samun sabani. Idan muka tafi bisa wannan fahimtar kuwa, to babu shakka mun ragewa kanmu jin dadin rayuwa irin ta aure. Kuma mun rage wa kanmu samun ainishin ladan da a ke samu a cikin auren.

Domin idan muka dauka a ranmu cewa wannan mutumin in dai har an zauan da shi na wani lokaci sai an samu matsala. To ba za mu iya kallon sa a matasyin amini ko ma aboki ba. Kuma ba za mu taba iya sakin jiki da sakankancewa yayin da muke tare da shi ba. Sai dangantakarmu da shi ta kasance tamkar ta wani tsuntsu da yake kiwo a  wata  gona, wadda kuma ya tabbata a cikin gonar akwai tarko. Daga ya yi sakaci kadan zai iya cafke shi.

Wannan tsuntsu ba zai taba iya sakin jiki ya more dukkan wani kalaci da zai samu a wannan gonar ba. Komai dadinsa kuwa. Idan matar mutum kuwa ta kasance kamar haka a gare shi, to babu abin da zai hana ka ce, ba su yi sa’ar auren ba. Domin daga cikin mafiya girman abin da ake tsammanin samu daga ma’aurata akwai nutsuwa da juna. Yayin da kuwa da a ka rasa nutsuwa, to aure ya samu tasgaro kenan.

Har wa yau, an samu nakasa ko tawaya a cikin tarin ladan da ya kamata ma’auratan su samu sakamakon auren. Domin a ka’ida shi ne, ana  auna zaman da mutum ya yi don hira da matarsa ma a matsayin wata ibada mai girman gaske fiye da tsammaninmu.

Exit mobile version