Yadda Abubakar Malami Ya Ciri Tuta A Cikin Ministocin Shugaba Buhari

Daga Yusuf Shuaibu

Ministan shari’ar Nijeriya, Abubakar Malami ya yi fice wajen yaki da cin hanci da rashawa tun fil’azal. Wanda hakan ne ma wasu ke ganin hakan ne ya sa suke da kyakkyawar alaka da fahimtar juna a tsakaninsa da shugaban kasa Muhammadu Buhari har kuma suka jima a tare ba tare da ana jinsu ba, kasancewar kowa ya san Buhari wajen yaki da cin hanci da rashawa.

Kasancewarsa kwararren lauya, Abubakar Malami ya yi aiki a matsayin lauyan majistire a jihar Kebbi, hakazalika ya kasance mashawarci a kan harkokin shari’a ga tsohuwar jam’iyyar CPC ta kasa, wanda ake kira ‘Congress for Progressibe Change’ a Turance.

Wanda shi ne mai tsaya wa shugaba Buhari a kotu a matsayin lauyansa bayan zabe.

Malami ya bayar da gudunmuwa mai yawan gaske wajen kafa jam’iyyar APC a shekarar 2013, inda ya kasance cikin sahun wadanda suka shiga kuma suka fita a gwagwarmayar da aka yi ta hade tsaffin jam’iyyun CPC da kuma ANPP.
Bayan samun nasarar shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban zaben kasa na shekarar 2015, ya nada Malami a matsayin Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnati. Nadin mukamin da Malami ya samu a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2015, ya sanya shi ya kasance mafi kankanta ta fuskar shekaru a cikin jerin ‘yan majalisar zantarwa ta gwamnatin Buhari. Bayan lashe zabensa a wa’adi na biyu da aka gudanar a shekarar 2019, shugaban kasa Buhari a ranar Laraba, 21 ga watan Agusta, ya rantsar da Malami a matsayin ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnati karo na biyu cikin jerin ministoci 43 da ya nada a sabuwar gwamnatinsa.

A matsayin Malami na Ministan Shari’a kuma Babban lauyan gwamnati ya gudanar da bincike kan wasu fitattun ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar nan. Wanda Ministan ya tabbatar da cewa tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a a kan rawar da suke takawa wajen haifar da tashin hankali sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa Boko Haram kudade.

Haka kuma a karkashin Ministan Shari’a, Abubakar Malami, Majalisar zartawar Nijeriya ta amince da kafa wata sabuwar hukumar yaki da rashawa baya ga hukumomin EFCC da kuma ICPC da ke yaki da rashawa a kasar nan.

Aikin sabuwar hukumar ta yaki da rashawa ya shafi kulawa da kuma daidaita dukkanin kadarorin da aka kwato a cikin gida da kuma kasashen waje bayan gudanar da bincike.

Ministan ya tabbatar da cewa kafa sabuwar hukumar ya zama wajibi domin karfafa nasarorin da gwamnati ta samu a yaki da rashawa a Nijeriya.

Gwamnatin Nijeriya ta ce galibi kudaden da aka kwato suna hannun hukumomin gwamnati daban-daban da suka hada da ‘yan sanda da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da EFCC da kuma ICPC.

Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta himmatu wajen zabar wadanda suka fi cancanta ga alkalai na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya(ICC). Wanda wannan kokarin babban lauyan gwamnatin tarayya ne, Abubakar Malami don fito da kima da darajar Nijeriya a idon duniya kamar yadda shi kansa ministan ya taba bayyanawa a wani zaman taro na majalisar dokokin kasashe zuwa manyan laifuka ta duniya karo na 19 da ya gudana a Hague cikin kasar Netherlands.

Malami ya kuma lura da cewa hare-haren da ake kai wa kotun manyan laifuka ta duniya da jami’anta na ci gaba da raunana tsarin dokar Rome da goyon baya a duk duniya.

A nan ne kuma ya kara jaddada cewa, gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi Allah wadai da duk ayyukan da aka tsara don lalatawa da kuma raunana ikon kotun manyan laifuka ta duniya na yin aikinta yadda ya kamata.

A shekarar da ta gabata, wata gagarumar nasara a babbar kotun tarayya a kan kamfanin P & ID wanda a baya kamfanin ke naman gwamnatin Nijeriya ta biya shi taran dalar Amurka biliyan 9.6.
Idan nana son a san mutum ciki da bai a dubi abubuwan da yake yi wa al’ummarsa, wato sashin da ya fito, kasancewar Abubakar Malami dan asalin Jihar Kebbi ne bai bar al’ummarsa a baya ba wajen ganin ya tallafa masu, a shekarar da ta gabata mai girma ministan shari’a na Nijeriya, Alh.

Abubakar Malami SAN, ya tallafa wa talakawa masu sana’ar kiwo tallafin iri na akuyoyi, don tallafawa sana’arsu.Tallafin an gudanar da shi ne a Jihar Kebbi karkashin Gidauniyar Khadimiyya Foundation wacce ta saba tallafawa al’umma a Jihar Kebbi karkashin jagorancin ministan shari’a.

Akwai sama da matasa 405 wadanda sama da kaso 85 ‘yan Jihar Kebbi ne sun samu aikin yi a ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayya wanda Abubakar Malami ne sanadiyya. A matsayinsa na dan Jihar Kebbi mai kishin ganin matasa sun yi nisa a fagen neman ilimi ingantacce, ministan ya sama wa ‘yan Jihar Kebbi da dama gurbin karatu da gwamnatin tarayya ta dauki nauyin karatunsu a nan gida Nijeriya da ma kasashen waje domin zurfafa karatunsu. A bangaren ci gaban kasa da kuma samar da ababen more rayuwa ga Jihar Kebbi, Malami bai yi kasa a gwiwa ba wajen bin ma’aikatu da hukumomin gwamnatin tarayyar da suka dace don tabbatar da cewa Jihar Kebbi ba a barta a baya ba wurin amfana da dinbin ayyukan ci gaban kasa da gwamnatin Buhari ke yi. A matsayinsa na mamba a Majalisar Zartarwa ta Tarayya, ya bada goyon baya dari bisa dari wurin gwamnati ta sakin kudade don ci gaba da aikin titin Yauri zuwa Kontagora.

Idan aka ce za a rika zayyano ayyukan da mai girma ministan shari’a yake yi, sai a cika shafukan jaridar nan ba a kammala ba, wani abu ba Jihar Kebbi kadai wannan aiki zai tsaya ba, har ma da sauran jihohin Arewa maso Yamma su ma za su amfana da kokarinsa da kuma wakilcinsa a majalisar zartarwa ta tarayya.

Exit mobile version