Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home WASANNI

Yadda Aka Fafata A Wasannin Zakarun Turai A Matakin Kusa Da Karshe

by Sulaiman Ibrahim
April 8, 2021
in WASANNI
2 min read
Abubuwan Da Suka Faru A Shekara Ta 2020 Data Gabata A Bangaren Wasanni

Editorial Use Only Mandatory Credit: Photo by Javier Garcia/BPI/Shutterstock (10577674db) Goalkeeper Jan Oblak of Atletico Madrid Liverpool v Atletico Madrid, UEFA Champions League, Round of 16, 2nd Leg, Football, Anfield, UK - 11 Mar 2020

WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

An koma fagen gasar cin kofin zakarun Turai matakin gab da na kusan karshe, inda Real Madrid da Liverpool suka maimata irin haduwar da suka yi a wasan karshe na gasar shekaru uku da suka gabata, lokacin da Sergio Ramos ya balla kafadar Mohamed Salah, abin da ya tilasta wa dan wasan ficewa daga fili tare da share tsawon lokaci na zaman jinya.

Sai dai a wannan karo, Ramos babu tabbas idan zai iya buga wasannin da kungiyarsa za ta fafata da Liverpool na gida da waje hakan yana nufin babu damar ya sake balla hannun Salah a karo na biyu sakamakon raunin da shi ma ke fama da shi yanzu haka.
A wancan lokacin dai, Real Madrid ce ta dauki kofin gasar bayan ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1 sai dai daga baya a shekara ta 2019 kungiyar kwallon kafar ta Liverpool ta sake dawowa inda ta lashe kofin ta hanyar doke Tottenham a wasan karshe.
Magoya bayan kungiyar Liverpool sun zura idanu don ganin gwanayensu sun rama abin da Real Madrid ta yi musu a wasan da aka buga a ranar Talata a kasar Sipaniya sannan suna fatan ramuwar gayyar bayan Real Madrid din ta haramta musu daukar kofin gasar zakarun Turai a wancan lokacin.
Sai dai kocin Liverpool Jurgen Kloop ya ce, yaransa ba za su buga wasan na sati mai zuwa a kasar Ingila da sunan ramuwar gayya ba amma za suyi iya yinsu domin ganin sun rama kwallaye ukun da aka zura musu a Sipaniya.
A bangare guda, an barje gumi tsakanin kungiyoyin Manchester City da Borussia Dortmund a filin wasa na Etihad duk dai a matakin na kwata fainal a gasar ta zakarun Turai kuma masu masaukin bakin ne suka samu nasara da ci 2-1.
Karawar kungiyoyin biyu na zuwa ne a daidai lokacin da kocin Manchester City Pep Guardiola ke jinjina wa dan wasan Borussia Dortmund Erling Braut Haaland wanda ake danganta shi da komawa Manchester City a kakar wasa mai zuwa.
Haalanda mai shekaru 20, shi ke kan gaba wajen yawan kwallaye a gasar zakarun Turai ta wannan kaka, inda ya zura guda 10 a raga kuma a yanzu haka ana ci gaba da alakanta Haaland da komawa Manchester City domin maye gurbin Sergio Aguero .
Sai dai Guardiola na ganin cewa, farashin da aka sanya kan dan wasan na yuro miliyan 150 ya yi tsada, yana mai cewa, Manchester City ba za ta iya biyan abin da ya zarce euro milyan 100 kan dan wasa guda daya ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Bambancin Hon Sama’ila Yakawada Da Sauran ‘Yan Siyasar Kaduna – Mai Martaba Giwa

Next Post

Zargin Tagayyara ‘Yan Wasa: Guardiola Ya Caccaki Hukumomin EUFA Da FIFA

RelatedPosts

Klopp

Muna Cikin Gagarumar Matsala – Klopp

by Muhammad
1 day ago
0

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta je gidan kungiyar kwallon...

Super League

Me Ya Sa Manyan Kungiyoyi Suka Kirkiri European Super League?

by Muhammad
1 day ago
0

Kungiyoyin Arsenal, Chelsea, Liverpool, Manchester City, Manchester United da Tottenham...

Mourinho

Shin Karshen Mourinho Ya Zo A Kwallon Kafa?

by Muhammad
1 day ago
0

A ranar Litinin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta sanar...

Next Post
Guardiola

Zargin Tagayyara ‘Yan Wasa: Guardiola Ya Caccaki Hukumomin EUFA Da FIFA

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version