Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta ziyarci abokiyar hamayyarta wato kungiyar kwallon kafa ta Liverpool domin buga wasan Premier League karawar mako na 29 da suka fafata a filin wasa na Anfield ranar Alhamis.
A wasan farko da suka buga a kakar bana, Liverpool ce ta doke Chelsea 2-0 a Stamford Bridge ranar 20 ga watan Satumba kuma yanzu Chelsea tana mataki na biyar a kan teburin Premier League da maki 44, ita kuwa Liverpool mai maki 43 ita ce ta shida.
Liverpool tana da mai koyarwa Jurgen Kloop dan kasar Jamus, itama Chelsea mai Thomas Tuchel dan Jamus ne sannan kuma masu horarwar sun fafata a junansu sau 14 a tsakaninsu, inda Kloop ya yi nasara a wasa tara da canjars uku, Tuchel ya ci wasa biyu.
Karawa a tsakaninsu:
Liverpool za ta iya cin wasa na biyar a jere a kan Chelsea a karon farko tun bayan 1972/73 kuma wasa daya kacal Chelsea ta yi nasara a kan Liverpool a fafatawa 12 baya a Premier da canjaras uku aka doke ta fafatawa shida har ila yau Chelsea ta sha kashi sau 23 a gasar Premier League a hannun Liverpool, kungiyar da ke kan gaba a doke ta a Ingila.
Kwazon Liverpool:
Liverpool ta yi rashin nasara wasa hudu a jere a Premier League a gida a bana kuma watakila ta sha kashi a karo na biyar a jere a Anfied da zai zama na farko a tarihin kungiyar saboda karawar karshe da Liverpool ta yi nasara a gida a kakar nan, ita ce ranar 16 ga watan Disamba da ta doke Tottenham 2-1 har ila yau Chelsea ba ta yi nasara a kan Jurgen Kloop a wasa biyar din farko a lig a gida ba, inda ya yi nasara a fafatawa biyu da canjaras uku.
Kwazon Chelsea:
Thomas Tuchel ya ja ragamar wasa tara a Chelsea ba a doke shi ba a dukkan fafatawa, inda ya ci karawa shida da canjaras uku kuma Chelsea ta zura kwallo 10 a raga tun bayan da Tuchel ya karbi aiki a watan Janairu aka ci kungiyar ta Stamford Bridge guda biyu kawai.
Manchester City ce kan gaba wajen hada maki a Premier League, sai Chelsea da ta biyu da ta samu 15, tun bayan da Tuchel ya koma kungiyar sannan Tuchel bai ci wasa bakwai da ya ziyarci takwaransa Kloop ba, inda ya yi canjaras biyu da rashin nasara biyar a wasannin waje.