Daga Idris Umar, Zariya
A ranar alhamis din da ta gabata ne Hukumar Jami’ar ABU Zariya ta yi bikin dashen itatuwa na shekarar 2017, tare da gudanar da taron karawa juna sani kan muhimmacin dasa itace da kuma illar sare shi ga rayuwar bil’Adama.
Taron dai an gudanar da shi ne babban dakin taro na Jami’ar wato Assembly Hall da ke a harabar jami’ar, inda aka gabatar da kasidu da suka shafi muhimmanin dashen itacen.
Cikin malaman da suka gabatar da kasidun akwai Farfesa Jibril Jibril, Daraftan (Center for Dryland) na jami’ar Bayaro, Kano, sai shaharanren masanin harkar kimiyyar dazuka da shuka itace, Cif Giwa Radife na (Pribate Forest Demonstrtion Plantation).
Da yake karanta nasa jawabin, Farfesa Kabir Bala, wanda ya wakilci Shugaban ABU, Farfesa Ibrahim Garba, ya ce wa, Farfesa Kabir ya bi sahun shugabannin jami’ar da suka shude wajen jajircewa don ganin an ci gaba da taron dashen shuka duk shekara, kuma ya nuna cewa, dole ne a tashi tsaye don tunkarar duk matsalolin da ake samu a sakamakon sakaci da ake yi na dashen itatuwa a duk fadin Nijeriya.
Ya ce duk da matsalar da jami’ar take da shi na rashin kudi, takan dage wajen raya tarukan dashen itatuwa a duk shekara saboda tunawa da Nijeriya.
Farfesan kuma ya gargadi al’umma da su guji sare itace ba gaira babu dalili. Ya ce, idan wani dalili yasa an sare, to a shuka wani akan lokaci don ya maye gurbin wanda aka sare.
Ya kuma nuna irin hadarin da duniya ke fuskanta a sakamakon rashin wadatattun itatuwa masu sarrafa iska a dangantakar mutane da sararin samaniya. Ya ce, da yawan manyan guguwa da ake fama da ita ko kuma ambaliyar ruwa, suna faru ne dalilin karancin itatuwa a doron kasa. Saboda haka ce al’umma su tashi tsaye a marawa tsarin dashen shuka itatuwa a duk fadin kasar nan.
A nasa bangaren, wakilin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru el-Rufa’i, Shugaban Hukumar Kula da Muhalldi, Malam Yusif Abdullahi, ya ce gwamnatinsu na bada gagarumar gudunmawa wajen dasa itatuwa, domin kowace shekara ana dasa itatuwa milyan biyu a fadin jihar.
Har ila yau, ya gabatar da sakon Gwamna el-Rufa’i na bukatar da yake da ita na a ba shi hadin kai domin dasa a duk fadin jihar. A cewarsa, gwamnan ya ji dadin wannan taro da ake gabatarwa, kuma yana fatan zai dore kamar yadda aka tsara.
Shi ma tsohon shugaban jami’ar ta ABU Farfesa Shehu Usman Abdullahi ya yaba matuka ga tsarin gudanarwa jami’ar a hannunta jagoranta na yanzu, inda ya ce duk mutumin da ya ci gaba da irin wannan aiki, ya nunawa duniya cewar ya san darajar halitta a doron kasa.