Idris Aliyu Daudawa" />

Yadda Aka Gudanar Da Binciken Kan Bullar Ebola A Congo Da Makotanta

Cututtukan da suka kunno kai a halin yanzu za su iya yin tasiri cikin al’umma da iyalinsu. Mazauna gida sun fi kwarewa da abin da suke aikatawa a muhallansu, wadanda suke kawance da su tare da su kansu za su iya zama su magance irin cutukan da suke addabarsu a muhallinsu, kuma hakan zai zama kamar wani mabudi ne da za su yi amfani da shi wajen dakatar da cututtuka domin ceton kansu da iyalansu daga kamuwa daga miyagun cutuka.

Binciken da aka gudanar na ilimin kimiyyyar jama’a ya samu daraja da basira cikin kwarewa a idanun jama’a da ya shafi bullar cuta ga rayuwar al’umma.

Basirar ilimin kimiyya na jama’a shi ke alamtawa mutane dabarun da za su kare kansu daga kamuwa da cutuka, da zai taimaka wajen samun ikon yin amfani da daidaita allurai, da kuma taimaka wa al’umma kan riskuwar cututtuka gare su a yankunansu, wajen mallakar abin da za su yi a kan kula da bullar cututtaka da mayar da martani.

A martani da aka mayar kan binciken da aka gudanar dangane da bullar cutar Ebola a yankin

Arewacin Kibu da Ituri, Dimokuradiyyar Congo (DRC), da Hukumar Lafiya Ta Diniya uwar cutara ta WHO, da abokiyar hadin gwiwarta, sun gudanar da bincike na musamman mai ninkawa kuma ya gudana cikin nasara.

Kazalika masu binciiken kan ilimi kimiyya da kwarewa game da abin da cutar da Ebola ke haifarwa, binciken ya nuna abubuwa da dama a burin da ake so a cimma na kawo karshen yaduwar cutar, tare da nusar da mutane illolinta.

Binciken ya nusar da jama’a yadda za su mayar da hankali kan yadda za su abin da ya dace abubuwan da suka hada da tafiyar da jagoranci a tsakaninsu, da kuma yadda za su taka rawa wajen kula da al’adu da batutuwan yadda za su inganta muhallinsu, don su kaucewa kamuwa da cutar Ebola, da kuma sassauci.

Sauran sun hada da bayar da bayanai ga kan shigowar bakin haure, domin hange ko hasashen baza cuttuttuka, da gudanar da ayyukan tseratar da abubuwa masu kima, don tantance yankuna da suke daf da kamuwa da cutar ‘ Manhaja.’ Abin da aka samo daga binciken kamar yadda rahohotanni suka nuna shi ne, an bayar da kwatance na tarukan cikin gida tare da gamsar da tawagar binciken.

Kazalika makullin binciken lokaci-lokaci ake takaita shi a babban mataki don takaice daftarin aikin, wanda zai rika zagayawa a tsakanin abokan tarayya.

Binciken-GOARN- (kimiyyar zamantakewar al’umma) da biyan kudi na cibiyar sadarwar al’umma na EU da aka yi masa lakabi da SONAR-Global, wannan ta samu ci gaba a taswirar binciken fasahar mutane, da aka gudanar a mayar da martanin da aka yi wa cutar ta Ebola a baya-bayan nan a Dimukradiyyar Congo, kamar yadda aka gabatar a Kasashen Uganda, Rwanda, Burundi, da kuma Sudan Ta Kudu.

Burin taswirar shi ne, ta bayar da wata alama ta siyasa, mayar da martani, da fitar da hanyar biyan kudi ta hanyar da binciken kimiyyar zai kammala cikin nasara, ko ina da kuma wurin ya aka mikashi.

Wannan himma za ta kara kwarin gwiwa ga binciken domin gano dabarun mayar da martanin.

Ya zuwa yanzu mafi yawan himma da binciken da mutane ke gudanarwa sun kammala, wasukuma ana ci gaba da yi, an kammala a Kibu Ta Arewa (Beni, Butembo, Katwa, Lubero, Bunia, Kayna, Masereka, Buhobi da kuma Mabalako), daga cikin yankunan da a halin yanzu da bullar Ebolan ta shafa. Da yawa ana kammala ayyukan ana nan ana duba su, sannan ana ta sanarwa kan kishiyantar bullar Ebola din da kuma riga-kafinta.

Misali, ta hanyar wayar da kan al’umma ganar da su muhimmancin jagorori (Sarakuna, Malaman addini, ‘yan siyasa) da sauransu.

Sauran ayyukan da aka kammala don a gane kwayar cutar ta Ebola da kuma yadda za a tare bullar cutar a Arewacin Kibu sun hada da misalin, sun hada da tantance imani da ita da kuma jita-jita a kan Ebolar, da kuma neman lafiyar, tare da gane halayyar kungiyoyi mabanbanta, da suka hada da yi wa iyaye da mata masu masu una biyu lakcoci.

Sauran abubuwan da aka kammala aikinsu sun hada da, wayar da kan al’umma wajen nuna masu muhimmancin zaman lafiya a junasu ba tare da an samu nuna banbancin addini ba, da kuma yadda za su taka rawa wajen neman yadda kare kansu daga kamuwa da cutar Ebola, da kuma yadda za su magance ta a yayin da aka samu wani ya kamu da ita, a cibiyoyin sada zumunci.

Ilimi ra’ayi da kuma jarrabawa (KAP) Kazalika bincike ya nuna bayyanar samar da shiyyoyi na cikin gida a fadin Kasar nan, tare da fahimta game da yadda ake zaton bullar cutar da kuma magance ta, da suka hada gano ita kanta cutar, da yadda za a yada ayyukan riga-kafinta, da fahimtar alamominta cikin bayar da labari da wa’adin da take dauka a halin yanzu.

Tsahon lokacin da aka shafe na himmatuwa wajen gudanar da bincike an samu nasarar fahimtar ta, amma dai burin aikin shi ne fahimtar jama’a kan himma wajen kyautata al’adu da muhalli don kada su zama masu taimakawa wajen yaduwar cutar ta Ebola a mazaunansu.

Sannan kuma aikin yana da burin sanar takaice kididdigar adadin mutane masu halartar taron binciken a yayin da annobar.

Wadannan ilimai masu daraja su ne aka yi alkawrin fito da su a fahimtar da mutane alamun bullar Ebola.

Haka zalika, Ayyukan Binciken Kimiyyar mutane da aka gabatar a makotan Kasashe don ceto kan iyakoki ya taimaka wajen yada sani tare da farkawar mutane sanin bullar cutar Ebolar.

A Uganda, aikin binciken an riga an kammala shi, za kuma a fara rangadin tabbatar da ingancinsa nan ba da dadewa ba.

Tare da haka, wannan tsarin samar da hanzari ne na kokarin yakar cutar, da ya hada da halaratar taron gami da ran-gadin tantance mahalartan, da samar da labarai, tattaunawa, da kuma mayarda hankali wajen taruwa a tattauna, girmama al’adu, duk an yi amfani da wadannan hanyoyin don su zama madubin dubawa gami da amfani da su wajen samar da halayya mafi inganci ga jama’a ta yadda za su fuskanci kalubalen da ke gabansu.

Exit mobile version