Yadda Aka Gudanar Da Maulidin Bana Na Abuja

Daga Rabiu Ali Indabawa

 

Al’ummar Musulmi daga ciki da wajen Babban Birnin Tarayya Abuja sun yi dandazo a ranar Talata, a tsohon dandalin fareti na kasa domin murnar zagayowar Maulidin Fiyayyen Halitta Annabi Muhammadu (SAW).

Maulidin wanda ya fara da zagayen daliban makarantu da kungiyoyin zakirai da sha’irai da sauran ‘yan agaji tun daga Mabushi zuwa filin faretin wanda yake tsakiyar Birnin Abuja, ya kunshi karatuttuka da jawabai daga manyan baki da sauran malamai da suka halarta.

12 ga Rabi’ul Auwal rana ce da aka haifi Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama, wadda masoya a duk fadin duniya ke gudanar da Idi na musamman domin tunawa da wannan rana mai matukar mahimmanci.

Kamar yadda kowace shekara masoya shugaban halitta sukan fito domin a zagaya cikin birnin tarayyar domin nuna na su wannan farin cikin, inda dakarun agaji na Munazzamatul Fitayanul Islam, reshen FCT Abuja, ke shirya wannan Mauludi a duk shekara, a karkashin jagorancin Mukaddam Alhaji Abubukar S. Yakub, da mai taimaka masa Babban Limamin Masallacin Karshi, wanda kuma wannan shi ne karo na tara da fara wannan Mauludi.

A wannan shekara ma kamar yadda aka saba, an fara zagayen ne daga Unguwar Mabushi zuwa ‘Old Parade Ground’ inda a nan ne aka gudanar da wannan Mauludi mai albarka.

Da isa filin an samu manyan baki sun cika wurin ci kuwa har da wakilin Shugaba Buhari, Ministan Abuja Muhammad Musa Bello.

Bayan bude taro da addu’a, sai karatun Al’kur’ani Mai girma, da kasidu daga mahalarta, sai karatun Diwani daga ‘yan kungiyar.

Bayan sun kammala sai dakarun Munazzama suka shigo suka gabatar da fareti a gaban manyan baki gami da rera taken Nijeriya da harshen Larabci. Daga nan sai aka gabatar da daliban makarantun Islamiyya, sannan aka shiga gabatar da malamai na da suka hada da Shehu Abubakar Saddik Shu’aibu, Shugaban kungiyar na FCT, da Malam Ibrahim Khalili Na’ibi na Masallacin Dantata dake Abuja. Akwai kuma wakilin Ambasadan Kasar Misra a Nijeriya, Sheikh Muhammad Abdu’aziz.

A jawabin da ya gabatar, wakilin shugaban kasar, Ministan Abuja Muhammad Bello, ya fara da karanta kalmar Tauhidi “La’ila ha illallah”, sannan ya ce, “Wannan lokaci ne da Allah ya nufa FIRS AID Group na Munazzamatul Fityanul Islam Abuja, suke yin taronsu na shekara ta tara Alhamdu lillah. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wakilta ni na zo wannan taro mai muhimmanci na 12 ga watan Rabi’ul Auwal, lokacin da muke alfahari da Mauludin Nabiyyina Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, ya ce na gaishe ku na yi masa godiya da aka gayyace shi, kuma yana godiya saboda taimako da ake yi masa game da addu’a da shawara.

Allah ya saka muku da alheri, Allah ya saka wa shugabanninku da alheri, Allah ya jikan magabatanmu mu kuma Allah ya sa mu cika da imani

Bayan kammala jawabin Mai Girma Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja ne, aka gabatar da wakilin Ambasadan Jamhuriyyar Egypt Shekh Muhammad Abdul’aziz, inda shi ma ya yi bayani cewa. Dukkan Musulman duniya a yau suna cike farin cikin zagayowar wannan rana ta haihuwar shugaban halitta Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama. Annabi mai girma, Annabi mai gaskiya da rikon Amana, Annabin da ranar da zai sauka a duniya sama da kasa suka dauki haske, haske da ba’a taba ganinsa kafin zuwansa ba.

Shekh Khalifa Abubakar Saddik Shu’aibu, ya gabatar da na sa jawabin, inda ya nuna godiyarsa ga duk jama’ar da suka halarci wannan majalisi mai albarka, sannan ya gabatar da addu’o’i ga kasa da kuma al’ummar kasa baki daya kan Allah ya tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

A karshen taron, Babban Kwamandan kungiyar Mukaddamar ya ba da sanarwar rasuwar daya daga cikin Hafsat daya daga cikin dakarun kungiyar da Allah ya karbi ranta a yayin gudanar da Mauludin, ya ce Allah ya karbi ranta a lokacin da take kai kawo, inda ta shaida wa wata abokiyar aikinta cewa ta ji kafarta ta dan yi nauyi, inda a wannan yanayi ne ta dan sunkuya don ta samu dan hutu, daga nan kuma aka sanar da likitocin da suke filin taron, da suka ga halin da take ciki aka kira motar hukumar kiyaye hadura FRSC, don a kai ta asibiti, ko da isarsu sai likitoci suka sanar da rasuwarta.

Daga nan ne ýan kungiyar suka dunguma zuwa jana’izar Hafsat, Kwamandan ya yaba wa hukumar kiyaye hadura inda ya ce, bayan suka dauke ta zuwa gida har sai da suka ba wa iyayenta kudi masu yawa. Kwamandan ya yi addu’ar Allah ya gafarta mata ya ba wa iyayenta hakuri da juriyar rashinta.

Exit mobile version