Hamza Bello">

Yadda Aka Gudanar Da Tallafin Kiwon Lafiya Na Hon. Garba Datti Babawo A Karamar Hukumar Sabon Gari Zariya

Al’umma da dama ne suka yi tururuwa daga birane da kauyukan karamar hukumar Sabon Gari dake jihar Kaduna, don amfana da shirin bayar da kiwon lafiya ga masu fuskantar larurori daban daban a gangamin bayar da kulawa na musamman da dan majalisa mai wakilar mazabar Sabon Gari a majalisar wakilai ta kasa Hon Garba Datti Babawa.

Ranar Litinin din makon jiya ne zababben dan majalisar dokokin tarayya mai wakiltar karamar hukumar Sabon Gari ta jihar Kaduna, Hon. Garba Muhammad Datti Babawo ya jaronranci bikin kaddamar da bayar da magunguna karkashin jagorancin wasu kwararrun likitoci a karo na uku domin warkar da masu larurorin cuttutuka daban daban kamar su ciwon Ido kunne Hawan Jin, ciwon siga, Kaba, Gwaiwa da larurorin mata daban daban wanda ana kuma sa ran za a kwashe tsawon mako guda ana yi, a Asibitin Sa’idu Dange dake cikin “Railway” da Asibitin Kantoma da ke GRA duk a cikin karamar hukumar Sabon Gari.

Daga cikin jawaban da ya gabatar, dan majalisar ya bayyana cewar babban burinsa shi ne, kafin kammala wa’adin wannan kujeran da yake kai shi ne, ya samar da romon dimokradiyya ga duk wani mutum dake mazabarsa musamman ta fuskar ganin babu sauran masu irin wadannan lalurorin a mazabarsa, tare da inganta jin dadin al’ummar ta kowanne Janibi na rayuwa, haka nan ya dauki alwashin samarwa da Asibitin Sa’idu Dange dake “Railway” da Asibitin Kantoma dake GRA da Asibitin ‘Yan Ayaba da ke cikin Sabon Gari da kuma wasu guda biyu da ke yankin gundumar Basawa da kayan aiki irin na zamani domin kara inganta su.

Haka nan  bai yi kasa a gwiwa ba wajen yaba wa dukkanin daukacin ‘yan Nijeriya dangane da jajircewar da suka yin a nuna hakuri da yadda suka tsinci kan su a a halin yanzu na tsadar rayuwa, ya ce, gwamnati na sane da halin da ake ciki tana nan tana kokarin shawo kan lamarin ba tare da dadewa ba, babban abinda da ake bukata kawai a gun al’ummar shi ne karin hakuri da addu’a ga shuwagabanni domin gaggawar shawo kan matsalar cikin kankanin lokacin, don Malam Bahaushe na cewa, “Aski idan ya zo gaban goshi yafi zafi”.

Daga karshe  ya shawarci wadanda suka amfana da wannan shirin da su yi iya  iyawarsu wajen ganin sun kiyaye duk wani sharadi da likitoci suka gindaya masu, domin yin haka ne kawai zai bada nasarar aikin da akai masu.

Shima a nasa jawabin da ya gabatar a taron, shugaban tawagar likitoci da za su gudanar da bayar da magungunan, Dakta Joseph Haruna Kigbu, ya bayyana cewar wannan aikin da Hon. Garba Muhammad Datti Babawo ya dauki kudirin yi, aikin ne wanda zai lashe Milyoyin kudi kafin a kammala shi, kuma wannan shekarar ita ce ta uku da fara wannan aikin alkairin, wanda ba wani dan majalisar da ya taba yi sai shi, haka nan ya ce, shekara biyun da suka wuce mutanen da suka amfana da wannan shirin basu wuce 4,000, to Amma a Bana muna sa ran kimanin mutane 7,000 ne za su ci gajiyar shirin, sakamakon ganin wasu da yawan al’umma basu sami kulaba a shekaran da ta gabatar, don haka ne bana muka kara gayyato wasu likitocin fiye da na bara don ganin mun sami saukin aikin. Sannan kuma a shekarun da suka wuce kimanin mutane 200 muka yi wa tiyata a cututtuka Daban daban, to amma a Bana ga dukkanin alamu za su fi haka yawa.

Haka nan shi ma a nasa jawaban shugaban karamar hukumar Sabon Gari Hon. Eng. Muhammad Usman, ya yaba wa dan majalisan da irin namijin kokarin da yake yi a wannan mazabar tasa, inda ya kamanta shi da kalmar “Uwa mabada Mama” ga jama’ar sa, daga bisani ya roki al’ummar ta Sabon Gari, da su ci gaba da yin kyawawan addu’a tare da fatan alkairi ga dan majalisan don ci gaban sa, da ci gaban karamar hukumar Sabon Gari da jihar Kaduna tare da kasarnan baki daya.

Wannan shirin ya taimaka mutane da dama sun warke daga cuttukar da suke fusanta  shikenan sun rabu da ciwo har abada insha Allahu. Misali na farkon da aka yi, akwai Mata da aka Yi musu aiki aka ciccire musu abun da ake ce ma kabar ciki Fybroid. A kalla dai cikinsu da duka basa haihuwa amma yanzu tunda aka yi musu duk sun haihu mutum wajen biyar biyar a cikin su. A saboda haka kaga ba wani follow up sun warke gashi sun samu ciki sun haihu wadanda da basa gani aka yi musu aiki nan take suke ci gaba daga nib a wata matsala, ana kuma basu maganin da za su ci gaba das ha har zuwa wani lokaci.

Da aka yi masa tambayar cewa, ga wadanda bas u samu danar halatar wanna gangamon ban a wannan karon, yaushe ake saran sake gudanar dashi irin wannan gangamin na bayar da kulawa na kiwon lafiya, musamman ganin kuma wannan shi ne karo na uku? .

Sai ya bayyana cewa saboda mahimmacin lamarin ga al’umma da kuma yadda aka lura cewa, mutene na amfana da lamarin baya da magungunan sai ya bayyana cewa, “To muna dai Saran dai, ‘Zamu zamar dashi kowanni shekara yanzu muka yi alkawari za mu yi. In muka ga da dama, zamu shirya a rinka yi akalla sau biyu a shekara insha Allah” inji Hon. Garba Datti Babawo.

Abn sha’awa kuma shi ne yadda al’umma suka yi tururuwa wajen gudanar da bayar da kiwon lafiyar, bayani ya nuna cewa, an samu halartar jama’a daga sassan karamar hukumar da kuma wasu ma da suka zo cini arziki daga wasu kananann hukumomin jihar sa wanTambaya: to ranka Shi dade ta zaka ga turn up din jama’a yadda Alu’mma suka karbi Shi wanna, dukkan wanda ya su halarta kima ana bashi kulawa ba age da banbanci ba.

“Alu’mma sun karbbi lamarin da hannu biyu-biyu kuma Kai ka je da kanka kanga wakilinku ma ya kaga irin mutanen da suka zo. Da aka je mutanen da aka ba magunguna, na cututtuka irinsu malaria, typhoid, da sauransu akalla da an ba 5,000. Akalla mutane dubu biyar an ba su magani, kuma an yi wa mutum fiye da 200 biyu tiyatar ta ido, an kuma yi mutum 100 aikin fitar da wasu cuttutuka a jikin su. Kamar su kaba kari, an kiuma ba fiye da mutum 2,000 tabarau don inganta ganin su”.

Sannan Kuma akwai mutanen da yawa da yi gwaji daban daban don gano cuttukar da suke dauke das hi don sanin irin magungunan da za a ba su.

Hon Garba Datti Babawo ya kuma yi kira na musamman ga al’umma da kuma shugabannn yankin Sabin Gari don bayar da hadin kai ga duykkan wasu ayyuka na ci gaba da za a bullo da su a nan gaba.

“Kira na musamman ga al’umma da shugabannin yan Sabon Gari a halin yanzu shi ne, farko godiya ne a ka yadda suka amsa kiran da a ayi musu na fitowa don karbar maganin da kumayadda sukanatsrau a ka gudanar da aikin bag tare da wani hayaniya ba, haka kuma ya anfane su, muna kuma wadanda bas u samu zuwa ba a wannan karon da su yi hakuri nan gaba ma za a sake irin wannan gangamin” inji

Ciki wadanda suka yi jawabi a wajen taron sun hada da Shugaban karamar hukumar Sabon Gari Honorabul Muhammad Usman da Darakta mai kula da harkokin addini na jihar Kaduna Shiek Jamilu Albani Samaru, da saura masu ruwa da tsaki a siyasar sabon Gari Zariya. Alumma kuma sun nuna godiya ga wannan shirin sun kuma yi fatan wasu ‘yan siyasar za su yi koyi ga wannan aikin alhairi na Hon. Garba Datti Babawo.

Exit mobile version