Bilkisu Yusuf Ali" />

Yadda Aka Gudanar Da Taron Gamayyar Kungiyoyin Gidan Arch. Dangiwa

Wannan taro ne da masoya wadanda suka yi kirkiri kungiyoyi daban-daban fiye da 40, don tallata da tafiyar da ayyukan Arch. Ahmed Musa dangiwa yake yi don hidimar al’umma tare da hadewa wuri guda, wato dai ‘Coalition of dangiwa Organization’.

Taron da aka gabatar ranar 31 ga Janairu, 2020, a babban dakin taro na gidan shugaban ksaa da ke tsohon gidan gwamnatin jihar Katsina. Bayan kammala taron ne sakataren kungiyar na wannan gamayyar Kwamared Nura Aliyu Batsari ya karanta a maddin kungiyoyin inda ya bayyanawa manema labarai makasudin wannan haduwar da gamewar kungiyoyin wuri guda. Ya fara bayyana wa ye Arch Ahmed Dangiwa inda ya nuna gogewarsa a siyasa da iya mu’amalarsa da al’umma. Ya bayar da gudumawa a siyasa tun daga jam’iyyar ANPP da CPN da kuma APC. Mutum ne jajirtacce da yake wanda ba ya gajiyawa da hidima al’umma tun kama daga jaharsu ta Katsina da arewacin Najeriya da ma Najeriyar baki daya. Wannan zuciyar tasa ta son taimakawa al’umma ya sa a yau suka taru don kafa wata gamayyar kungoyi don tallafawa da yada wadanan ayyuka na alheri da yake gudanarwa. “A tunaninmu wannan ce kadai hanya da za su iya tallata da yada kyawawan manufofinsa don al’umma su yi koyi”
Matasa sune ruhin al’umma wannan ta sa Arch Ahmed ya mayar da hankali kwarai wajen taimakon matasa da ba su tallafi don dogaro da kai da rage tunanin dogaro da aikin gwamnati. Ko a kwana kwanan nan ya yi irin wannan tallafin na karfafa gwiwa ga fasihan marubuta don nuna musu mihimmancin kirkira da tasirinta a cikin al’umma.
Ko a bangaren aikinsa ya yi matukar kokari inda ya kawo ci gaba a bangaren wanda yake yi na bankin ba da lamuni da gidaje na kasa wato (Federal Mortgage Bank of Nigeria) wanda aka yi ittifakin tun daga kafuwar bankin a 1973 yana cikin sahun farko da suka yi abin da ya dace bisa doka. Inda aka rika ginawa ma’aikata gidaje cikin farashi kankani da bayar da bashin gyaran gida ga ma’aikatan gwamati.Babban abin da ya fi kayatar da al’umma ga wannan dan talikin shi ne duk ire-iren wadannan ayyukan ana yin su ne a bude saboda komai an bar shi a fili kuma a bude a yanar gizo ba tare da rufa-rufa ba.
masa don ya samu kwarin gwiwar ci gaba da wannan hidima da yake yi ga al’umma sannan mutane wadanda suka samu dama irin tasa su yi koyi da shi. Al’ummar Katsina tana tare da shi kuma tana jinjina masa mu matasa muna yi masa fatan alheri don ceton rayuwarmu ne a gabansa”

Exit mobile version