An bayyana tarihin masarautu ba za su cika ba sai an ambaci Imam Bn Abdulkarim Almaghil saboda irin gudummuwarda ya bayar wajen.kafuwarsu da asssasu bisa doron addinin musulunci.Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ne ya bayyana hakan a wajen kaddamar da littafin rayuwar Imam Muhammadu Abdulkarim da aka yi a kofar Kudu.
Ya bayyana cewa kafin shigowarsa Kano ya bi ta wasu kasashe kuma yazo Kano ne a lolacin Sarki Muhammadu Rumfa, sannan ya rubuta masa littafai har da na kundin tsarin mulkin musulunci.
Ya ce, daga gudummuwar da Shehi Maghili ya bayar akwai kafa makarantu da gyara harkar kasuwanci da tsaftaceta ta ilmantarwa da tsara kasuwanci da tsara zaman fada da kusanto da shugabanni kusada al’umma ta samarda alkalai da Hakimai.
Aminu Ado ya ce, Shehu Danfodiyo ya yi mu’amaloli da littattafan koyarwar Maghili da dama. Suna rokon Allah ya jaddada rahama gareshi kuma su masu rubuta littafin Allah ya basu ladan.aikinda sukayi.
Ya ce, halayen Imam Maghili abin koyi ne ga al’umma wanda koyarwace ta Manson Allah tare da yaba wa wannan gagarumin kakari na hangen nesa da marubucin littafin yayi na wanzar da tarihinsa.
Shima a nasa jawabin shagaban Mu’assasa ta Imam Muhammad Almaghili Sharif Abdulkarim Sharif Ali Salihu Almaghili ya ce, aikin mu’assasar shi ne aiki ne wajen tattare zuri’arsa a Kano da kasa baki daya da bada kulawa akan Sharifai da suke kasarnan ta basu kulawa ta hanyar hada kai da sanin juna da janyo hankalin sharifai su san kansu, a kauda bara gurbi wadanda ba sharifai ba, suke fakewa da sharifta da kuma maganin wadanda suke tafiyar da abubuwa marasa daidai a cikin tafiyar Ahlul baiti.
Ya ce, wannan.littafi an rubuta shi ne sakamakon baye-baye da Allah ya yi wa iyalan Shehu Maghili masu yawa, danginsu na cikin kasar nan da Nijar da Aljeriya har Ingila da Amurka sun watsu wannan ma’assasa tana bin wurare dan tattaro wadannan al’umma dan basu kulawa.
Ya ce, masarautar Maghili ita ce ta Sharifan Najeriya gaba daya sanan ya yaba wa dukkan wadanda suka bada gudummuwa wajen kaddamar da littafin musamman wakilan shugaban kasa wanda ministocinsa na tsaro Janar Magashi dana Gona, Sabo Nanono suka sami halarta ya kuma godewa Gwamnan Kano Ganduje bisa turo Alhaji Muktar Ishak kwamishinan ayyuka na musamman.ya wakilce shi. Ya godewa mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado bisa kishinsa ga gidan Manzon Allah.
Shima a jawabinsa Manajan darakta na hukumar samarda ruwa ma Kano Injiniya Garba Ahmad Kofar Wambai yace wannan.kaddamarda littafi na kakansu Imam.Maghili suna yiwa Allah godiya akai kuma duk wanda a tarihinsa bai darsu dashi ba, a harkar shariftarsa akwai alamar tambaya.
Ya ce littafin ya jaddada zai sanin waye Imam Maghili domin shiya kawo musulunci ya yada zuriya kuma littafin zai sanar da wadanda basu san tarihinsa ba su sani.
Injiniya Garba Kofar Wambai ya yabawa Sarkin Sharifai da fadarsa godiya garesu bisa wannan kokari na jaddada wannan littafi.Ya godewa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayinsa na Uba daya bada gudummuwa wajen tabbatarda littafin.
Yace a rubutun. Littafin ya shafe shekaru Bakwai ana gwagwarmaya har zuwa wannan lokaci da aka tabbatar dashi aka kaddamar.
Yace irin hidmar da bayin Allah irinsu Imam Maghili suka yiwa Kano.itace take ta bibiyar Kano take samun tsari daga dukkan masifofi da bunkasar arzikinta.
Malam Habibu Sidi Sharifai ya nuna farin cikinsa da godiya ga Allah ga duk wadanda suka bada gudummuwa wajen samun nasarar taron kaddamarda littafin.
A yayin kaddamarda littafin babban mai kaddamarwa ya sayi kwafi 500 a kan N5,000,000.Ministan tsaro Bashir Magashi N5,000,000.Ministan Gona.N5,000,000.Gwamnatin.jahar Kano N500,000.Kwamishinan ayyuka na musamnan na Kano.Alhaji Muktar Ishak Yakasai 100,000 da sauran gudummuwa da dama daga mutane daban-daban.da suka halarci taron.