Idris Aliyu Daudawa" />

Yadda Aka Samu Karuwar Yunwa Saboda Annobar Korona

Duk da ya ke tuni ne a ka shiga cikin kungi ko kuma kangin cutar yunwa, sai kuma wani al’amarin da ya kara ruruta ita wutar ta yunwa ai sanadiyar cutar ko kuma annobar Korona ita ce wadda ta sa cutar ta yunwa ta kara ta’azzara. Saboda  kuwa a shekarar 2019 an kiyasata cewar mutane miliyan 821 wadanda daga cikin su miliyan 149 a ke ma kallon ko kuma maganar gaskiya su ne wadanda su ka fi fuskantar shiga cikin matsalar ta yunwar.

“Da ya ke yanzu tuni ne ita annobar cutar musamman ma idan aka yi la’akari da yadda shi halin na rayuwa ya ke, wanda shi mahaliccin mu Allah Subhanahu Wata’ala shi ne wanda da yardar sa ce al’amuran su ka kasance hakan. A na ma iya duba ko kuma la’akari da yadda a ke fuskantar canjin yanayi wanda wannan al’amarin ne ya kara jagula ko kuma bata al’amuran da suka shafi tsari ko shirin samar da abinci.

Hakan ne kuma zai iya sa ko mkuma barin milyoyin mutane da za su kasance cikin halin gaba Kura baya kuma sayaki, ko kuwa a ce mutum na ganin matsalare da yake fuskanta kamar ita ce wadda yake tsammani ko ganin kamar ruwa ne ya kai shi wuya a tsakiyar kogi, ashe bai sani baa baya akwai da wani babban Kada, Dorina da kuma Macijin ruwa wadanda su shi su ke bi bai sani ba.

“Shi dai tsarin abinci na duniya ko kuma World Food Programme (WFP a turanci ya kiyasta cewar, yawan al’umma wadanda suke fuskantar yunwa, ko ta wani bangare kuma wadanda suka su sun dade a cikin halin na yunwa suna iya karuwa zuwa miliyan 270, zuwa karshen wannan shekarar da mu ke ciki ta 2020 saboda kuwa ai tun shekarar data gabata ta 2019 a sanadiyar ita wannan annobar aka samu karuwar kashi 82.

“Akwai wasu kasashe ko kuma wuraren da su tuni a ke yi masu kallon can ne a ka fi samun ita wannan matsala ta yunwa, wadanda kuma  hada da Indiya, Afirka ta Kudu, da kuma Brazil, wasu wurare ne da ake ma kallon da akwai masu karamin karfi da yawa, wadanda kuma kuma kudaden da suka samu basu taka kara sun karya ba dalili kuwa shi ne na samun karuwa ta’azzar wadanda ke kara shiga cikin halin na yunwa. Wannan kuma ya ksance haka ne a sanadiyar su dama tun kafin kafin bullar ita annobar ta Korona sun dade da kwana cikin wata annobar ta yunwa.

Shi dai wannan rahoton ya nuna cewar” Koda kuwa su kasashen da ake yi ma kallon masu karfin arziki ne ba su karfin shiga cikin halin yunwa ba. Wasu bayanai wadanda aka samu daga gwamnatin kasar Ingila ko kuma hadaddiyar daular Turawa ya nuna tun ma kafin ita annobar ta bayyana, da akwai manyan mutane da suka zata miliyan bakwai (7.7 million) wadanda su sun dade da rage yawan  ko kuma kin cin abinci da gangan su ke kin cin abincin, bugu da kari kuma da akwai mutane miliyan fiye da 3.7, wadanda su kuma su nemi taimako ne na abinci ko kuma su yi amfani da Runbun ajiya na kayayyakin abinci wadanda aka ajiye ko tanada saboda tsarin kota kwana ko kuma abinda ka iya tasowa wanda yake bukatar daukar mataki na gaggawa.”

Exit mobile version